Alhaji Muntari ya zama sabon Sa’in Katsina

Alhaji Muntari Sa’i shi ne babban da ga marigayin Amadu Na Funtuwa, wanda Allah Ya karbi rayuwarsa

Alhaji Muntari ya zama sabon Sa’in Katsina

Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmuminu Kabir, ya tabbatar wa Alhaji Muntari Amadu Na Funtuwa da sarautar Sa’in Katsina sarautar da mahaifinsa ya yi kafin rasuwarsa.

Alhaji Muntari Sa’i shi ne babban da ga marigayin Amadu Na Funtuwa, wanda Allah Ya karbi rayuwarsa a ranar Alhamis din da ta gabata.

Sa’in Kastina Marigayi Amadu Na Funtuwa ya rasu ne yana da shekaru sama da 90.

Marigayi Alhaji Ahmadu Na Funtuwa ya rasu ne a Asibitin Koyarwa ta Tarayya da ke Katsina bayan ya yi fama da rashin lafiya.

Marigayin shi ne Sa’in Katsina na farko wanda Marigayi Sarkin Katsina, Usman Nagogo ya nada, kuma shi ne dan majalisar Sarki da ya fi kowa dadewa.

Kafin rasuwarsa, Sa’in ya yi zamani da sarakunan Katsina uku, Sa Usman Nagogo, Sarki Kabir Usman Nagogo da kuma Sarki na yanzu Abdulmuminu Kabir.

Lakurawa sun kashe ma’aikatan kamfanin Airtel 3 a Kebbi

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya