Alhaji Musa Alkali ne sabon Sarkin Sudan na Tiggi

Masarautar Argungu da ke Jihar Kebbi ta nada Alhaji Musa Alkali Yusuf a matsayin Sarkin Sudan na Tiggi.Nada Alhaji Musa Alkali, Sarkin Sudan ya biyo bayan rasuwar Sarkin Sudan marigayi Alhaji Lawal Namera a ran 10 ga Maris din bana. Da yake zantawa da wakilinmu a Argungu bayan karbar takardar tabbatar masa da sarautar, ya […]

Alhaji Musa Alkali ne sabon Sarkin Sudan na Tiggi
Alhaji Musa Alkali ne sabon Sarkin Sudan na Tiggi

Masarautar Argungu da ke Jihar Kebbi ta nada Alhaji Musa Alkali Yusuf a matsayin Sarkin Sudan na Tiggi.Nada Alhaji Musa Alkali, Sarkin Sudan ya biyo bayan rasuwar Sarkin Sudan marigayi Alhaji Lawal Namera a ran 10 ga Maris din bana. Da yake zantawa da wakilinmu a Argungu bayan karbar takardar tabbatar masa da sarautar, ya gode wa Majalisar Masarautar Argungu da kuma gwamnatin Jihar Kebbi da duk wanda ya taimaka wajen ganin ya samu sarautar. Ya yi kira ga wadanda suka yi takara wajen neman sarautar cewa, su sani dukkansu daya ne saboda haka su ba shi hadin kai don ciyar da kasar Tiggi da masarautar Kabbi da Jihar Kebbi gaba.  Alhaji Musa Alkali wanda tsohon Babban Sufurtandan ’Yan sanda ne ya yi aiki a jihohi daban-daban na kasar nan.