Alhaji Shehu Shagari (1924 zuwa 2018)

Najeriya ta rasa manyan fitattun ’ya’yanta a shekarar 2018, amma babu shakka mafi fice daga cikinsu shi ne Alhaji Shehu Shagari, Shugaban Najeriya a Jamhuriyya ta Biyu daga 1979 zuwa 1983. Ya rasu ne a Babban Asibitin Kasa da ke Abuja a ranar Juma’a 28 ga Disamba yana da shekara 94. Ya shugabanci kasar nan […]

Alhaji Shehu Shagari (1924 zuwa 2018)

Najeriya ta rasa manyan fitattun ’ya’yanta a shekarar 2018, amma babu shakka mafi fice daga cikinsu shi ne Alhaji Shehu Shagari, Shugaban Najeriya a Jamhuriyya ta Biyu daga 1979 zuwa 1983. Ya rasu ne a Babban Asibitin Kasa da ke Abuja a ranar Juma’a 28 ga Disamba yana da shekara 94. Ya shugabanci kasar nan ne a lokaci mafi annashuwa kuma mafi kalubale a tarihinmu. Yadda Shagari ya killace kansa bayan ya bar shugabanci wani babban abin koyi ne na kasancewa dattijo wanda abin da ya fi so shi ne zaman lafiyar kasa da ci gabanta da bauta wa Ubangiji da hidima ga jama’a.

An haifi Alhaji Shehu Shagari ne a garin Shagrai da ke Jihar Sakkwato a 1924. Mahaifinsa Aliyu shi ne Magajin Shagari, wato Dagacin Shagari wanda ya rasu a lokacin da wanda zai zama Shugaban Kasa na gaba yake da shekara biyar kacal a duniya. Daga nan ne sai babban yayansa Muhammadu Bello ya dauki nauyin rainonsa. Alhaji Shehu Shagari ya hakarci Makarantar Elemantare ta Yabo daga 1931-1935, sai Makarntar Midil ta Sakkwato daga 1936 zuwa 1940 sai Kwalejin Gwamnati ta Kaduna wadda daga baya ta koma Kwalejin Barewa, Zariya daga 1941 zuwa 1944.

Ya fara aiki ga kasar nan inda ya shafe shekara 40 tare da farawa daga Hukumar En’e zuwa karamar hukumar zuwa gwamnatin lardi zuwa ta yanki zuwa ta kasa da ta duniya. Shagari ya yi aiki a matsayin malamin makaranta (Malamin Kimiyya da Labaran Kasa, Jogurafi) a Makarantar Midil a shekarun 1940 da farkon 1950, inda a lokacin ya tsara fitacciyar wakarsa ta Wakar Najeriya, wadda ta kawo bayanin daukacin Najeriya.

A 1951 ne Shagari ya shiga harkokin siyasa inda ya zama Sakataren Jam’iyyar APC na Lardin Sakkwato. Kuma an zabe shi Dan Majalisar Wakilai zuwa Legas a 1954 daga Mazabar Sakkwato ta Yamma. Kuma ya zama wakili a Hukumar Bayar da Tallafin Karo Ilimi ta Tarayya daga 1954 zuwa 1958. Kuma ya zama Sakataren Harkokin Majalisa ga Firayi Ministan Najeriya Sa Abubakar Tafawa Balewa a 1956. Daga nan ne ya shiga rike mukaman minister a ma’aikatu bakwai a Jamhuriyya ta Farko zuwa gwamnatocin mulkin soja da suka biyo baya. Ya kasance Ministan Kasuwanci da Masana’antu a 1958 zuwa 1959; sai Ministan Bunkasa Tattalin Arziki daga 1959 zuwa 1960; sai Ministan Harkokin Fansho daga 1960 zuwa 1962; sai Ministan Harkokin Cikin Gida daga 1962 zuwa 1965, sannan ya zama Ministan Ayyuka a 1956 har zuwa lokacin da aka yi juyin mulki ga gwamnatin Jamhuriyya ta Farko a Janairun 1966.

A 1967 ne ya zama Sakataren Gidauniyar Bunkasa Ilimi ta Lardin Sakkwato, wadda ta giggina makarantu a Lardin Sakkwato. Kuma ya zama Kwamishinan Daukar Ma’aikata na tsohuwar Jihar Arewa maso Yamma a 1968 zuwa 1969. A 1970, Shugaban Kasa Janar Yakubu Gowon ya nada shi Kwamishinan (Ministan) Bunkasa Tattarlin Arzki na Tarayya, Sake Tsugunarwa da Sake Gina Kasa, sannan shekarar da ta biyo baya yam aye gurbin Cif Obafemi Awolowo a matsayin Kwamishinan (Minstan) Kudi na Tarayya. Kuma ya zama Gwamna Bankin Duniya da na Asusun Lamuni na Duniya (IMF).

A 1976 ne aka zabi Alhaji Shehu Shagari a matsayin Kansila a Karamar Hukumar Yabo. Kuma ya taba zama Shugaban Hukumar Bunkasa Birnin Sakkwato (SUDA), wadda ta gina kaswar zamani ta Sakkwato. Ya zama wakili a Kwamitin Tsarin Mulki daga 1977 zuwa 1978, kwamitin da ya shirya Tsarin Mulkin 1979. A watan Nuwamban 1978 ne Jam’iyyar National Party of Nigeria (NPN) ta zabe shi a matsayin dan takararta na Shugaban Kasa. Kuma ya lashe zaben Shugaban Kasa da aka gudanar a watan Agustan 1979, inda ya kama ragamar shugabancin kasar nan a ranar 1 ga Oktoban 1979.

Lokacin da ya zama Shugaban Kasa, Shagari ya yi aiki wurjanjan wajen cimma manufofin jam’iyyarsa ta NPN na “samar da abinci da muhalli.” Kuma a kokarin cimma wannan manufa ce ya kaddamar da shirin samar da abinci na Green Rebolution a 1980, sannan ya gina rukunin gidajen da ake kira da Rukunin Gidajen Shagari a dukan hedkwatocin jihohin kasar nan a wancan lokaci. A 1982 kuma ya kaddamar da “Shirin Gyaran Hali” domin mayar da jama’a kan kyawawan halayen da suka yi watsi da su. Faduwear farashin man fetur a 1981 ya tilasta shi ayyana matakan “tsuke bakin aljihu.” Jim kadan da lashe zaben 1983 wanda ’yan adawa suka yi zargin an tafka magudi, sai sojoji suka kwace mulki tare da kawar da Jamhuriyya ta Biyu. An tsare Shagari na wasu shekaru, kuma bayan sako shi, sai ya koma rayuwarsa a Sakkwato da garin Shagari ba tare da yana yawan surutu ba. 

An nada shi Turakin Sakkwato tun 1962, kuma ya kasance cikakken wakili a Majalisar Sarkin Musulmi tun daga 1996.

Za a dauki lokaci mai tsawo ana tunawa da Alhaji Shehu Shagari kan saukin halinsa da tawali’u da son zaman lafiya da kuma rashin gajiyawa da kokari wajen bunkasa ci gaban kasa da samar mata kyakkyawar makoma. Allah Ya jikansa da rahama Ya sa Aljanna ce makomarsa. Amin.