Alhaji Sule Katagum: Tonga Uban ’Yan boko ya kwanta dama
Masarautar Katagum da ke Jihar Bauchi cikin kasa da makonni uku ta yi rashin fitattun manyan mutane da ke rike da sarautu masu muhimmanci a masarautar. Wanda ya fara rasuwa cikinsu shi ne Alhaji Muhammad Disina Marafan Katagum, bayan kwana goma da rasuwarsa sai Mai martaba Sarkin Katagum Alhaji Muhammadu Kabiru Umar ya rasu, sannan […]

Masarautar Katagum da ke Jihar Bauchi cikin kasa da makonni uku ta yi rashin fitattun manyan mutane da ke rike da sarautu masu muhimmanci a masarautar.
Wanda ya fara rasuwa cikinsu shi ne Alhaji Muhammad Disina Marafan Katagum, bayan kwana goma da rasuwarsa sai Mai martaba Sarkin Katagum Alhaji Muhammadu Kabiru Umar ya rasu, sannan bayan kwana takwas da rasuwan Sarki kuma sai Wazirin Katagum Alhaji Sule Katagum CBE, KBE, CFR, Allah Ya yi masa cikawa.
Wani basarake a fadar Katagum ya shaida wa Aminiya cewa Wazirin wanda ake yi masa kirari da “Tonga Uban ’Yan boko, Uban Habu Baban Audu, Uban Ladi da Mairo,Tonga Uban Mai Talle,” Allah Ka kai haske kabarinsa, ya rasu ne yana da shekara 93 bayan ya yi fama da rashin lafiya na tsawon lokaci.
Wata majiya daga fadar ta shaida wa Aminiya cewa Wazirin ya rasu ne bayan jikinsa ya yi tsanani inda aka garzaya da shi Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Azare, inda ya rasu a can.
Ya rasu ya bar matan aure biyu da ’ya’ya 26 da jikoki da dama. Babban Limamin Masarautar Katagum Malam Ayuba ne ya jagoranci Sallar Jana’izar Wazirin wadda aka yi shi a kofar Fadar Sarkin Katagum.
Rasuwar Wazirin kuma dan Majalisar Sarkin Katagum ta kara jefa al’ummar masarautar cikin alhini, saboda shi ne Shugaban wakilan Majalisar Sarki inda duk abin da ya taso shi zai kai gaban Sarki, kuma shi ne zai fada wa Sarki in ya yi hukunci aka samu kuskure ko hukuncin bai dace da addini ko al’ada ba.
Waziri a tsarin Masarautar Katagum shi ne babban mai bai wa Sarki shawara, kuma duk wanda za a nada wa wata sarauta shi yake jagorantar nada shi, shi ne kuma zai fadi yawan tamburan da za a buga wa mai sarautar, sannan kuma shi ne shugaban masu zaben Sarki. Wata majiya ta ce ko sabon Sarkin Katagum da aka nada kafin ya rasu, duk da ba ya da lafiya, cikin ikon Allaha ya samu baki ya fadi wanda yake so.
Wata majiya daga Fadar Katagum ta ce Sarautar Waziri ba gadonta ake yi ba, sai dai ana bai wa duk wanda Sarki yake so ne ta lura da kwazo da iliminsa saboda yakan kasance abokin aikin Sarki ne. Majiyar ta ce akwai gidan da sarautar Wazirci ta taba yin shekara 80 amma ta bar gidan daga baya.
An haifi marigayi Wazirin Katagum ne a 1924 a garin Katagum Maikaba hedkwatar karamar Hukumar Zaki da ke Jihar Bauchi. Ya yi makarantar firamare a garin Azare da Makarantar Midil ta Bauchi, kafin ya zarce zuwa makarantar ba da horo kan sadarwa da ke Kaduna. Har wa yau ya yi karatu a Makarantar Harkokin Mulki ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya. Kuma ya yi kwas kan gudanar da kananan hukumomi a kasar Ingila, kafin ya sake yin wani kwas kan kananan hukumomi a Ibadan, sannan ya yi kwas kan aikin gwamnati a kasar Ghana,
Alhaji Sule Katagum ya yi aiki a wurare da dama daga ciki akwai Akawun Majalisa lokacin tsohuwar Gwamnatin Arewa, sai ya dawo Katagum ya yi Sakataren Mulki daga nan kuma ya koma aiki a Gwamnatin Tarayya ya zama Shugaban Hukumar daukar Ma’aikata ta Tarayya. Kuma ya taba zama Shugaban Hukumar Kula da Ayyukan ’Yan sanda, kuma ya yi aiki a kwamitin ba da shawara kan zama dan kasa.
Alhaji Sule Katagum ya kuma zama Shugaban Bankin Ciniki da Masana’antu, sai ya dawo gida aka nada shi Madakin Katagum, daga baya aka ciyar da shi gaba aka nada shi Wazirin Katagum a 1989, ya shafe kimanin shekara 28 yana sarautar Wazirci.
Gwamnan Jihar Bauchi Muhammadu Abdullahi Abubakar da Sabon Sarkin Katagum Alhaji Umar Kabir Umar na Biyu da Mai martaba Sarkin Misau Alhaji Ahmed Suleiman da Mai martaba Sarkin Ningi Alhaji Yunusa Muhammad danyaya suna daga cikin mutanen da suka halarci jana’izar Wazirin,
Liman Malam Ayuba ya roki Allah Ya jikan Waziri Ya gafarta masa Ya yafe masa kura- kuransa Ya kyauta bayansa Ya sa Aljannah ce makomarsa.
Gwamna Abubakar ya bayyana rasuwar Wazirin da babban rashi ga masarautar Katagum da Jihar Bauchi da Najeriya baki daya. “Na yi rashin uba wanda yake fada mini gaskiya komai dacinta a kowane lokaci, domin tun muna yara muke zuwa gidansa, har kwana muke yi a gidan tare da ’ya’yansa. Allah Ya jikansaYa gafarta masa,” inji Gwamnan.
Shi kuwa Talban Katagum Dokta Musa Babayo a sakon ta’aziyyarsa ya ce, “Muna mika ta’aziyya ga Fadar Katagum da al’ummar Masarautar Katagum bisa babban rashin da muka yi na uba, dattijon arziki, Wazirin Katagum Alhaji Sule Katagum.”
Ya ce “Wannan babban rashi ya biyo bayan manyan rashe-rashe da Masarautar Katagum ta yi na Mai martaba Sarkin Katagum Alhaji Kabir Umar da kuma Marafan Katagum sai kuma ga shi yau mun tashi da rashin uba, dattijon arziki mutumin kirki wato Wazirin Katagum, wanda duka suka auku a cikin mako uku. Ubangiji Allah Ya jikan Mai girma Wazirin Katagum da Mai martaba Sarkin katagum da Mai girma Marafan Katagum, Allah Ya kai haske kabarinsu, Allah Ya sa Aljanna ce makomarsu Allah Ya ba mu hakurin jure rashinsu.
Wani marubuci kuma mai sharhi a kan al’amuran yau da kullum Malam danlami Baban Takko Falakin Dass ya bayyana Wazirin a matsayin uba na aikin gwamnati a Najeriya, ya ce ba za a yi maganar aikin gwamnati a Nijeriya ba tilas sai an ambaci marigayi Wazirin Katagum, domin yana daga cikin wadanda suka fara aikin gwamnati daga Arewa tun kafin samun ’yancin kan Najeriya da bayan samun ’yancin kan lokacin da aka yi masa sauyin aiki zuwa Gwamnatin Tarayya daga rusashshiyar Gwamnatin Jihar Arewa ya zama Shugaban Hukumar daukar Ma’aikata ta Najeriya. Ya ce marigayin ya ba da gagarumar gudunmawa wajen hada kan Najeriya kuma lokacin da yake makarantar midil a 1940, Alhaji Sule Katagum mutum ne mai hazaka kuma ba ya barin ko-ta-kwana don a wancan makaranta ya jagoranci neman kyauta abincin dalibai.
Baban Takko ya ce za a ci gaba da tunawa da Wazirin saboda irin gudunmawar da ya bayar wajen gina kasar nan, kuma za a ci gaba da tuna martabarsa da sanin darajar jama’a da kula da mutuncin jama’a. Allah Ya jikansa Ya gafarta masa.