Alhaji Widi dantijjani ya kwanta dama
Allah Ya yi wa fitaccen dan kasuwar nan, Alhaji Muhammadu Usman wanda aka fi sani da Widi dantijjani rasuwa a gidansa da ke Sabo Yaba, Jihar Legas. Alhaji Widi dantijjani wanda a ranar Juma’ar da muka kawo tattaunawa da shi kan alkarsa da Alhaji Mamman Shata ya rasu yana da shekara 86 dabayan ya yi […]
Allah Ya yi wa fitaccen dan kasuwar nan, Alhaji Muhammadu Usman wanda aka fi sani da Widi dantijjani rasuwa a gidansa da ke Sabo Yaba, Jihar Legas.
Alhaji Widi dantijjani wanda a ranar Juma’ar da muka kawo tattaunawa da shi kan alkarsa da Alhaji Mamman Shata ya rasu yana da shekara 86 dabayan ya yi fama da rashin lafiya.
An kai gawarsa zuwa garinsu na ’Yanleman da ke Jihar Jigawa inda aka yi masa jana’iza aka bisne shi a makabartar garin kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Marigayi Widi ya rasu ya bar ’ya’ya 22 da matan Aure biyu da jikoki fiye da 40.
Daga cikin ’ya’yansa akwai Fatima Widi Jalo wacce ta taba zama Kwamishinar Harkokin Mata ta Jihar Jigawa da Abubakar Widi Jalo da ke aiki a ofishin Majalisar Tarayya da ke Legas da Kabiru Widi Jalo da ke aiki da Babban Bankin Najeriya da ke Abuja.
dan kanwar marigayin kuma shugaban kungiyar Hausawan birnin Ikko, Alhaji Ghali Sulaiman ya ce wadanda suka halarci jana’izarsa sun hada da Limamin garin ’Yanleman, Sheikh Salihu Baro da Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido da mataimakinsa da sarakunan Hadeja da Auyo da Ringim da limamin Hadeja da Jakadan Turkiyya, Abdulhamid Ahmed da manyan shugabanni da ’yan kasuwa.