Alhajin Filato ya rasu a Makkah

Hukumar Alhazan Jihar Filato ta sanar da rasuwar Alhaji Isma’il Musa daga Karamar Hukumar Mangu, a Asibitin Kwararru na Annur da ke Makkah.

Alhajin Filato ya rasu a Makkah

Muslim pilgrims gather around the Kaaba, Islam’s holiest shrine, as they perform Eid Al-Adha morning prayers in Mecca, on June 28, 2023. (Photo by Abdulghani BASHEER / AFP)

Wani alhajin Najeriya daga Jihar Filato ya rasu a Makkah a daidai lokacin da alhazai ke kammala aikin Hajjin bana.

Hukumar Jin Dadin Alhazan Jihar Filato ce ta sanar cewa Alhaji Isma’il Musa daga Karamar Hukumar Mangu, ya rasu ne a Asibitin Kwararru na Annur da ke Makkah.

Babban Sakataren Hukumar, Alhaji Hayabu Dauda, ya sanar cewa ran Alhaji Isma’ila ya yi halinsa ne bayan da ya shafe makonni uku kwance a asibitin na Annur a birnin Makkah.

Sai dai sanarwar ba ta bayyana ko marigayin ya samu gudanar da aikin Hajjin na bana ba da ya kai shi Saudiyya ba.

Hukumar ta mika ta’aziyya ga iyalan Alhaji Isma’ila tare da rokon Allah yi masa rahama.

Dalilin da ba a fara biyan masu hidimar ƙasa N77,000 ba — NYSC

2027: Neman tazarce ba ya gabana yanzu — Tinubu

Shin Binani ta dawo?

’Yan sanda sun ƙwace sakamakon zaɓe a Ribas