Alhakin ’yan Najeriya ne ya fara kama PDP –Nazifi Ahmad

Alhaji Muhammad Nazifi Ahmad, shi ne tsohon shugaban marasa rinjaye a Majalisar Jihar Filato, jigo a sabuwar Jam’iyyar APC, a tattaunawarsa da wakilinmu, ya bayyana matsalolin da Jam’iyyar APC take fuskanta a yanzu da dambarwar da ke faruwa a Jam’iyyar PDP da kuma zaman lafiyar da aka fara samu a Jihar Filato: Aminiya: Zuwa yanzu […]

Alhakin ’yan Najeriya ne ya fara kama PDP –Nazifi Ahmad
Alhakin ’yan Najeriya ne ya fara kama PDP –Nazifi Ahmad

Alhaji Muhammad Nazifi Ahmad, shi ne tsohon shugaban marasa rinjaye a Majalisar Jihar Filato, jigo a sabuwar Jam’iyyar APC, a tattaunawarsa da wakilinmu, ya bayyana matsalolin da Jam’iyyar APC take fuskanta a yanzu da dambarwar da ke faruwa a Jam’iyyar PDP da kuma zaman lafiyar da aka fara samu a Jihar Filato:

Aminiya: Zuwa yanzu yaya kake ganin tafiyar jam’iyyarku ta APC?
Nazifi Ahmad: To gaskiyar magana ita ce, kamar yadda kowa ya sani jam’iyyarmu ta APC.  Jam’iyyu uku  da suka hada da ANPP da CPC da ACN  da bangarorin  jam’iyyun DPP da APGA ne suka hade suka kafa ta.
A duk lokacin da aka ce za a zo a yi hadaka irin wannan, dole ne a samu mutane sun zo da bambance- bambancen ra’ayoyi. Kuma kowa na kokarin kare irin ra’ayin da jam’iyyarsa take da shi. Wannan shi
ne matsalar da Jam’iyyar APC take fuskanta a yanzu.
Bayan haka, APC an riga an nada shugabanninta na riko na kasa. Sai dai abin bakin ciki tun da aka nada shugabannin rikon har zuwa wannan lokaci an kasa nada shugabanni a jihohi.
Wannan tsawon lokaci da aka ja ya dada rikirkita abubuwa ya fito da gutsiri-tsoma ya kawo rashin sanin inda aka dosa a cikin jam’iyyar. Son zuciya yana neman ya shiga cikin tafiyar.
Aminiya: Wato akwai matsaloli a tafiyar Jam’iyyar APC ke nan?
Nazifi Ahmed: Eh, akwai matsaloli amma matsaloli ne da za a iya magancewa. Wannan tafiya garke ne na mutane, dole idan babu shugaba kowa ya yi yadda ya so, kuma jam’iyya dole sai tana da shugabanci. To matsalar dai ke nan shugabannin riko na kasa har yau sun kasa kafa shugabannin riko na jihohi. Saboda haka duk dan Jam’iyyar APC kusan yana zaune ne kara-zube. In da a ce shugabannin za su yi ta maza, su kawar da duk wani son zuciya su kafa shugabannin riko a jihohi, duk wadannan abubuwa za su kau. Don an yarda a yi hadakar kuma ana son a yi tafiyar.
Aminiya: Idan muka dawo ga Jam’iyyar PDP yaya kake ganin dambarwar da ke faruwa a cikinta a yanzu?
Nazifi Ahmad: Ai, dambarwar da ke faruwa a Jam’iyyar PDP a yanzu addu’ar talakawan Najeriya ne ya kama ta. Shekara 14 ke nan PDP tana mulki kasar nan, kuma duk wani dan Najeriya ya ji a jikinsa, saboda mulkin PDP. Harkokin ilimi sun lalace, tsaron kasa ya lalace, ma’aikatun gwamnati ba sa aiki, zabe babu adalci a ciki, babu wutar lantarki babu ruwan sha, an kara kudin man fetur sau shida a zamanin mulkin PDP. Saboda haka, kullum ’yan Najeriya suna addu’o’in Allah Ya ba mu mafita a kasar nan, kuma Allah Ya fara karbar addu’o’insu. Don haka warware wannan dambarwa ta PDP zai yi wahala.
Aminiya: To,  ganin irin matsalolin da jam’iyyarku ta APC  da Jam’iyyar PDP suke fuskanta mece ce mafita  a kasar nan?
Nazifi Ahmad: Wato ciwon da ya samu ’yan siyasar kasar nan, idan ana son a fahimci wannan lamari sai an koma baya. A lokacin mulkin Janar Babangida da mulkin marigayi Janar Sani Abacha an yi ta wahalar da ’yan siyasa cewa za a bayar da mulki. Don haka a lokacin da Janar Abdulsalam ya ce zai mika mulkin, sai ainihin ’yan siyasar suka ki shiga saboda sun gaji. Domin haka, sai ’yan dagajin ’yan siyasa suka karbi mulkin kasar nan, saboda haka muka shiga wannan hali. Don haka mafita kan wannan hali da muke ciki ita ce, na farko mutanen kasar nan masu tsoron Allah, Musulmi da Kirista su fito su shiga siyasa. Domin a samu a ceto kasar nan daga halin da ta shiga. Matukar mutanen kirki suka ki shiga siyasa, to ba za a warware matsalolin da suke damun al’ummar kasar nan ba. Bayan haka wadanda suke kan mulkin kasar nan, su sani cewa za su mutu kuma Allah zai tambaye su kan abin da suka aikata, saboda haka su ji tsoron Allah. Abu na gaba shi ne, ya zama wajibi duk wani dan Najeriya ya ci gaba da yin addu’a Allah Ya kawo mana daidaituwar al’amura a kasar nan. Domin kasar nan tana cikin wani hadari Allah ne kawai Ya san me zai faru kafin nan da shekara ta 2015.
Aminiya: Idan muka dawo Jihar Filato, yaya kake ganin yanayin zaman lafiyar da aka fara samu a jihar?
Nazifi Ahmad: Babu shakka an fara samun zaman lafiya a Jihar Filato, amma ka sani cewa ba gwamnati ce ta kawo zaman lafiya ba. Zaman lafiyar nan ya samu ne, ba don gwamnati ta kawo wani gudunmawa ko ta taimaka ko ta yi wani kokari na ganin an samu zaman lafiyar ba.
Mutanen jihar ne Allah Ya soma sanya musu fahimtar cewa Musulmi da Kirista duk wanda ya cutu shi ya cutu, gwamnati ba ta san abin da ake yi ba. Saboda haka kowa ya yi wa kansa fada ya koma ya zauna.
Saboda haka fatarmu ita ce zaben kananan hukumomin jihar da za a gudanar a ranar 7 ga Disamba mai zuwa, wadanda aka dora musu hakkin gudanar da zaben su gudanar da shi tsakani da Allah.
Kuma muna fata gwamnatin Filato kada ta yi la’akari da cewa an yi zaben kananan hukumomi a jihohin kasar nan, amma jam’iyyun da suke kan mulki sun lashe zaben baki daya. Domin idan aka dubi fadace-
fadacen da aka yi a jihar nan, mafiya yawansu sun taso ne a kan zabe. Saboda haka gwamnatin Filato ta sake wa hukumar zabe ta jihar mara, domin ta yi abin da ya dace.
A karshe ina kira ga al’ummar Jihar Filato, su yarda cewa Allah ne Ya hada su, don haka babu wanda ya isa ya raba su. Ko Bahaushe yana so ko baya so, dole sai ya zauna da kabilar da ba Hausa ba. Kowane dan wata kabila yana so, ko ba ya so dole ne sai ya zauna da Bahaushe domin haka Allah Ya tsara. Bayan haka, gwamnati ta tsaya kan gaskiya ta yi adalci. Malamai da fastoci su yi wa’azin gaskiya, al’umma kuma su yarda da junansu, idan aka samu haka, zaman lafiyar da aka fara samu a Filato zai dore.

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50