Alhazai sun fara barin Saudiyya bayan kammala Aikin Hajji

Akalla mahajjatan Indonesiya 230 ne suka rasu a yayin Aikin Hajjin.

Alhazai sun fara barin Saudiyya bayan kammala Aikin Hajji

Dubun-dubatar Musulmai sun fara barin birni mai tsarki na Saudiyya bayan da suka kammala Aikin Hajji wanda ya gudana a cikin tsananin zafi.

A ranar Juma’a, kwana uku bayan gagarumin aikin, dubun-dubatar mutane sun yi ta shiga motocin bas-bas daga birnin Makkah don kama hanyar kasashensu, a cewar kamfanin dillancin labarai na AFP.

Alhazan sun fara tafiya ne bayan kammala Dawafin Bankwana, ta hanyar zagaye Dakin Ka’aba sau bakwai wanda yake cikin Masallacin Harami.

“Na yi matukar farin cikin kammala Aikin Hajjina lafiya,” in ji wani mahajjaci Mohammad al Bashir mai shekara 47, dan kasar Tunusiya, ya fada bayan da ya kammala Sallar Juma’a.

Tun ranar Litinin alhazai suka tafi Mina daga Makka don fara zaman Aikin Hajjin, inda washe gari ranar Talata kuma suka wuce Filin Arafa.

A ranar Laraba suka yi Dawafin Ranar Sallah tare da fara jifan Shaidan, aka ci gaba da zaman Mina don karasa jifan Shaidan a ranakun Alhamis da Juma’a.

Sai dai yawanci ’yan kasashen da suka fi makwabta da Saudiyya da ma ’yan wasu kasashen Turai da yankin Asiya ne suka fara komawa kasashensu a ranar Juma’ar.

Amma sauran kasashe irin su Nijeriya sukan fara jigilar mayar da alhazai ne bayan kwanaki da kammala Aikin Hajjin.

A bana, mutum fiye da miliyan daya da dubu 800 ne suka gudanar da Aikin Hajji, wanda yana daya daga cikin shika-shikan Musulunci biyar, kuma shi ne taron ibada mafi girma da ake yi a duniya.

Yawan wadanda suka yi Hajjin a bana ya karu da mutum 926,000 a kan na bara, inda mutum miliyan daya ne kawai suka halarta saboda ba a gama dage dokokin annobar cutar korona ba.

A shekarar 2020 kuma, mutum 10,000 kawai aka bai wa damar yin Aikin Hajjin, inda yawan mutanen ya karu da 59,000 a shekarar 2021.

Mace-mace sakamakon tsananin zafi

An sha samun afkuwar munanan al’amura a lokutan Aikin Hajji da suka hada da turereniya da ma harin masu ta da kayar baya, amma babbar matsalar da aka samu ita ce tsananin zafin da aka zabga.

Fiye da mutum 2,000 ne tsananin zafin ya kwantar da su, a cewar hukumomin Saudiyya, bayan da ma’aunin zafin ya kai digiri 48 na salshiyas.

Akalla mahajjatan Indonesiya 230 ne suka rasu a yayin Aikin Hajjin, a cewar alkaluman da kasashe da dama suka fitar, ba tare da bayyana sakamakon mutuwar ba.

Ana zaton mai yiwuwa yawan wadanda zafin ya yi wa illa sun fi wancan adadin yawa, don wadansu ba a kai su asibitoci ba.

A shekarun baya-bayan nan, Aikin Hajji na fadowa a cikin lokacin zafi, a daidai lokacin da sauyin yanayi ke sa zafin yankin hamada ke kara tsananta.

Kwararru sun yi gargadin cewa nan gaba za a ci gaba da samun tsananin zafi a Saudiyya nan da karshen karnin da muke ciki, inda ma’aunin zai kai digiri 50.

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta