Yadda alhazai suke tsayuwar Arafa
Alhazai za su shafe yinin yau suna ibada da addu’o’i a Filin Arafa.
Alhazai 60,000 da ke halartar aikin Hajjin bana sun isa filin Arafa inda za su shafe yinin Litinin suna gudanar da ibada da addu’o’i da kuma neman gafara.
Alhazai sanye da takunkumi da ke aikin Hajjin sun baro sansaninsu da ke Mina suka kwana ne a Filin Arfa, inda za su halarci babbar ibadar da a baya miliyon mahajjata ke halarta daga ko’ina a fadin duniya.
Sai sabanin shekarun baya da ake ganin mahajjata babu masaka tsinke a kan Dutsen Rahama, wanda aka fi sani da Dutsen Arafa, bana ma abin ya bambanta.
Halartar tsayuwar Arfa 9 ga Dhul-Hijja, 1441 Hijiriyya shi ne kololuwar aikin Hajji, kuma daya daga ciki shika-shikan Musulunci.
Alhazan, wadanda daukacinsu mazauna kasar Saudiyya ne, za su yi sallolin Azahar da La’asar a Arfa, inda a bana Limamin Masallacin Harami, Sheikh Bandar Baleelah, zai gabatar da huduba.
A filin Arfa ne aka ruwaito cewa Manzon Allah (SAW) ya gabatar da hudubarsa ta karshe sama da shekara 1,400 da suka gabata.
Gabanin faduwar rana alhazan za su tafi Muzdalifah — tsakanin Arafat da Mina — su kwana, kafin washegari su koma Mina su yi “jifar shaidan”.
– ’Yan gata –
Selma Mohamed Hegazi, ’yar kasar Masar ta ce kasancewa daga cikin masu rabo “zai sa ka ji cewa lallai Allah mai gafara ne kuma Ya zabe mu mu halarci a wannan wurin. In Allah Ya yarda addu’o’inmu za su karbu” .
Ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, “Duk jikina ya sai rawa yake ta yi,” a lokacin da take tsaye a tsakanin sauran mahajjata sanye da harami.
A yayin da masu ibadar suka halarci Filin Arafa a cikin yanayi na natsuwa, Baref Siraj, dan kasar Saudiyya mai shekara 58 ya ce, “Hakika kasancewata cikin mutum 60,000 da ke aikin Hajji …. babbar ni’ima ce.”
Aikin Hajji daya ne daga cikin manyan tarukan addini a duniya, wanda sama da mutum miliyan 2.5 ke halarta a lokaci guda kuma a wuri guda.
Gudanar da aikin Hajji lamari ne mai matukar daraja ga mahukuntan Saudiyya, wadanda su ne Hadiman Masallatai biyu Masu Alfarma.
Hana mahajjata daga wajen kasar ya haifar da matukar damuwa tsakanin Musulmin duniya, wadanda yawanci suke yin ajiya ta shekaru domin su samu halartar ibadar.
An zabi mahalarta daga cikin mutum 558,000 da suka nemi damar ta hanyar tsarin tantancewa ta intanet.
An kuma takaita halartar idabar ga mutane masu shekara 18 zuwa 65 da suka kammala daukar allurar rigakafin cutar COVID-19 kuma ba sa fama da wata cuta mai tsanani.