Alhazan Jigawa sun angwance bayan kammala aikin Hajjin bana

Mutane da dama sun taya su murnar auren da suka yi.

Alhazan Jigawa sun angwance bayan kammala aikin Hajjin bana

Wani abun farin ciki ya faru a birnin Makkah, inda wasu alhazai biyu daga Jihar Jigawa, suka zama mata da miji bayan sun kammala aikin Hajjin bana.

Angon, Malam Abdulmumin Abdulkareem, shugaban alhazan K5aramar Hukumar Birniwa, da amaryarsa Malama Salamatu A. Duku, sun haɗu ne a lokacin aikin Hajji.

Bayan sun fahimci juna, sai suka yanke shawarar yin aure.

Malam Abdulmumin, ya bayyana farin cikinsa da yadda aka gudanar da auren, yana mai cewa bai yi tsammanin abubuwa za su tafi cikin sauƙi ba.

Ya kuma gode wa Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhaza na Jihar Jigawa, Alhaji Ahmad Umar Labbo, wanda ya ɗauki nauyin shirye-shiryen auren.

Ya ce su biyun masu aikin wa’azi ne da koyar da addinin Musulunci, kuma yana fatan aurensu zai ƙara ƙarfafa ayyukan da suke yi wajen yaɗa addini.

Shi ma Alhaji Ahmad Umar Labbo ya ce kafin a ɗaura auren, an tabbatar da cewa ma’auratan sun yi gwajin lafiya kamar yadda dokokin jihar suka tanada.

Bayan likitoci sun tabbatar da lafiyarsu, aka amince a ɗaura auren.

An ɗaura auren ne a gaban jami’an Hukumar Alhazai, wakilan gwamnatin jihar, malamai da sauran alhazan Jigawa da suka halarci bikin.

Lamarin ya ja hankalin alhazan Jigawa da dama, inda mutane suka bayyana shi a matsayin wata ni’ima da kuma kyakkyawar alaƙa da Hajji ya haɗa tsakanin Musulmi.