Alhazan Jigawa sun sake dawowa Kano bayan jirgin da aka canza musu ya samu matsala
Jirgin da aka sauya musu ya samu matsala ne a kan hanyar kasar Kamaru, lamarin da ya tilasta masa dawowa Kano.
Jirgin da aka canza wa alhazan Jihar Jigawa su 554 ya sake dawowa Filin Sauka da Tashin Jirage na Malam Aminu Kano a ranar Alhamis bayan ya tashi zuwa Kasar Saudiyya.
Idan za a iya tunawa jirgin da aka fara zuba alhazan Jihar Jigawa ya yi saukar gaggawa a Kano sakamakon kankarar ruwan sama da ta bugi gilashinsa, lamarin da ya janyo tsagewarsa.
Sai dai jirgin da aka musanya musu wanda ya tashi misalin karfe 2:00 na dare ya dawo Kano misalin karfe 5:40 na asuba ranar Alhamis sakamakon wata matsala da ya samu.
Majiyar Aminiya ta ruwaito cewa jirgin ya samu matsala ne a kan hanyarsa ta kasar Kamaru, lamarin da ya tilasta masa dawowa Kano.
Wani da ya nemi a boye sunansa da ke aiki a filin jirgin na Kano ya bayyana cewa alhazan suna nan suna jiran jirgin da zai kwashe su.
“A yanzu ga su nan a kasa, jirgin da ya fara diban su daga Dutse tuni aka gyara, shi wanda za a yi amfani da shi wajen kwashe alhazan,” in ji majiyar.
Wata maniyyaciyya da Aminiya ta tattauna da ita ta bayyana cewa a yanzu haka ana shirye-shiryen sanya su a wani jirgin don, “har mun kai Kamaru sai aka sake juyowa da mu, aka ce shi ma wannan jirgin ya samu matsala. Sai dai ba su sanar da mu matsalar ba. A yanzu haka dai ana shirye-shiryen sake zuba mu a wani jirgin.”
Manajan Daraktan Kamfanin Max Air a Kano, Malam Bello Ramalan, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce alhazan za su tafi kasar Saudiyya an jima kadan.
“Jirgin farko ba wai saukar gaggawa ya yi ba, domin babu wata matsala da ta sami injinsa, lamarin ya shafi gilashin jirgin ne.
“Amma wannan jirgin har yanzu ba mu san matsalarsa ba. Yanzu haka dai muna kokari wajen sama wa alhazan wani jirgin. An jima kadan za su tashi insha Allah.”
A cewarsa “Alhazan suna cikin koshin lafiya; Mun ba su abinci da duk abubuwan da suke bukata.”