Alhazan Kaduna sun sha wuya a hannun kamfanonin jiragen sama – Sarkin Birnin Gwari

Mai martaba Sarkin Birnin Gwari kuma Amirul Hajji na Jihar Kaduna, Malam Zubairu Jibril Maigwari ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda kamfanonin jiragen sama suka yi jigilar alhazan jihar zuwa kasa Mai tsarki a bara, inda ya ce alhazan sun sha bakar wahala a hannunsu.Sarkin ya bayyana haka ne bayan ya mika wa Gwamnan […]

Alhazan Kaduna sun sha wuya a hannun kamfanonin jiragen sama – Sarkin Birnin Gwari
Alhazan Kaduna sun sha wuya a hannun kamfanonin jiragen sama – Sarkin Birnin Gwari

Mai martaba Sarkin Birnin Gwari kuma Amirul Hajji na Jihar Kaduna, Malam Zubairu Jibril Maigwari ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda kamfanonin jiragen sama suka yi jigilar alhazan jihar zuwa kasa Mai tsarki a bara, inda ya ce alhazan sun sha bakar wahala a hannunsu.
Sarkin ya bayyana haka ne bayan ya mika wa Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir Ahmed El-Rufa’i rahoton Aikin Hajjin bara a gidan Gwamnati Jihar a ranar Litinin da ta wuce.
Ya ce mafi yawan alhazan babu wanda bai yi zaman fiye da sa’oi’ ashirin da hudu ba a filin jirgin sama wanda hakan bai dace ba. Saboda haka ya bukaci a rika amfani da tsarin da ake yi a shekarun baya inda jihohi ke zama da Hukumar Hajji ta kasa domin zaben kamfanonin jirage da suka dace.
Alhaji Zubair Maigwari ya ce kwamitinsa ya maida wa gwamnatin jihar ragowar kudi har Dala Dubu 50 da ba a kashe a lokacin aikin Hajjin da ya gabata ba.
“An yi aikin ne saboda Allah har ta kai ga kudin da aka tafi da su an dawo da Dalar Amurka dubu 50 ko fiye da haka saboda haka ba karamin abu ne aka yi ba domin ba a taba samun irin haka ba. Na biyu mun nuna cewa alhazan Kaduna mun sha wuya a hannun masu jiragen da aka ba su damar jigilar alhazanmu domin da can jihohi kan zauna da Hukumar Hajji ta kasa a zabo kamfanonin da ake so amma a wannan karo sun zabar mana ne kawai suka ba mu. Shi ya sa da za a dawo alhazanmu suka sha wuya kwarai da gaske. Babu wanda bai yi sa’o’i sama da 24 a filin jirgin sama ba. Saboda haka muka fada wa gwamnati cewa muna san a koma yadda ake yi a da, a zauna mu zabi wanda muke so ya kwashe mu. Idan ba a yi mana daidai ba mun san da hannunmu a ciki,” inji Sarkin.
Ya koka kan abincin da aka ba alhazai a bana, inda ya ce abincin ba ya da dadi lamarin da ya sa alhazai suka koma suna cin abinci wajen Takari. Sai masu yi wa alhazai hidima a Saudiyya, ya ce  a bar jihohi su zabi wadanda za su yi musu hidima.
Game da sansanin alhazai na Mando a Kaduna ya ce shekara uku ko hudu ke nan ana karbar Naira dubu biyar daga hannun kowane maniyyaci da sunan za a gyara shi, amma har yanzu ba a gyara ba. Don haka ya bukaci gwamnatin jihar ta hana hakan tare da maido wa alhazai da kudinsu tunda jihar ke gyara wurin ba Gwamnatin Tarayya ba.
“Sannan akwai bukatar a gyara wa wasu daga cikin ma’aikatan hukumar alhazai ta jihar zama ko ma a cire su daga wurin domin binciken da muka yi akwai abubuwa marasa dadi da suka faru da bai kamata a maimata fadarsu ba,” inji shi.
Da yake mayar da jawabi Gwamna Nasir El-Rufai wanda Mataimakinsa Barnabas Bala Banted ya wakilta ya bayyana kwamitin Amirul Hajjin a matsayin amittattu saboda maido da ragowar kudi da suka yi ga gwamnati, ya ce hakika abin da ake bukata ke nan daga shugabanni.
Sai ya ce tafiya da kuma dawowa lafiya da alhazan suka yi abin a godiya ne ga Allah. Sai ya jajanta wa iyalan alhazai tara da suka rasu a kasa Mai tsarki a lokacin aikin hajjin inda ya yi addu’ar Allah Ya jikansu da rahama. Ya ce gwamnati za ta duba shawarwarin da ke cikin rahoton da idon basira domin aiwatar da su.