Alhazan Kebbi rukunin farko sun dawo gida
tashi daga Kasar Saudiyya da misalin karfe 3:10 na dare agogon Najeriya, inda ya kwaso alhazai guda 426 zuwa babban birnin jihar.
Rukunin farko na Alhazan Jihar Kebbi na Hajjin shekarar 2026 sun sauka a Filin Jirgin Sama na Kasa da Kasa na Sir Ahmadu Bello da ke Birnin Kebbi a ranar Alhamis.
Wanda hakan ke nuna alamun fara jigilar dawo da alhazan jihar gida a hukumance.
Jirgin kamfanin jiragen sama na Flynas ya tashi daga Kasar Saudiyya da misalin karfe 3:10 na dare agogon Najeriya, inda ya kwaso alhazai guda 426 zuwa babban birnin jihar.
Jami’an gwamnatin jihar sun bayyana cewa, alhazan sun fito ne daga kananan hukumomin Koko-Besse da Aliero da Bunza, tare da rakiyar jami’an gwamnatin jihar Kebbi da kuma Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kebbi.
Alhazan da suka fito daga Koko-Besse da Aliero, wadanda suka zanta da manema labarai, sun nuna godiyarsu ga Allah da ya ba su ikon kammala aikin Hajji lami lafiya, sannan sun yaba wa gwamnatin jihar bisa goyon bayan da ta ba su a lokacin gudanar da aikin.
“Ina godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki da ya kiyaye rayukanmu kuma ya ba mu ikon kammala aikin Hajjin bana cikin nasara,” in ji daya daga cikin alhazan.
Ya kara da cewa, suna matukar godiya ga Gwamna Nasir Idris bisa kyakkyawar kulawar da suka samu a Kasar Saudiyya.
“Damuwarsa game da jin dadinmu ta sa tafiyar ta kasance cikin sauki a gare mu,” in ji shi.
Wata tawaga daga Gwamnatocin Jihar Kebbi da Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar ce ta karbi alhazan a filin jirgin tare da sauran jami’ai.
Tawagar ta jinjina wa kyakkyawan tsarin da aka samu tsakanin gwamnatin jihar, kamfanonin jiragen sama, da kuma hukumomin Saudiyya wanda ya tabbatar da dawowar alhazan cikin sauki.