Alhazan Najeriya su guji sayar wa takari ‘uniform’ — NAHCON

Hukumar ta gargaɗi maniyyata kan yin alaƙa da takari.

Alhazan Najeriya su guji sayar wa takari ‘uniform’ — NAHCON

Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), ta gargaɗi maniyyatan da ke shirin sauke farali, kan sayar wa takari kayansu da hukumar ta ɗinka musu domin neman kuɗi.

Daraktan Da’awah na NAHCON Jihar Kebbi, Sheikh Aminu Hassan ne, ya bayyana haka lokacin da yake yi wa maniyyatan jihar jawabi bayan sun sauka a Saudiyya.

Akwai zarge-zargen cewa takarin na sayen tufafin wasu maniyyatan musamman mata da kuɗi masu yawan gaske, domin ɓatar da kama wajen shiga cikinsu da fakewa da aikin hajjin wajen aikata abubuwan da ba su dace ba.

Hassan, ya ce sayar da tufafin babban laifi ne da zai iya janyo wa mutum hukunci mai tsanani.

“Haƙiƙa za ka iya samun kuɗi masu yawa a wajen takari, musamman ku mata, to amma ku tuna cewa za su yi amfani da tufafin ne wajen aikata ɓarna.

“Sannan ku sani cewa za a danganta laifin da Najeriya da ma Jihar Kebbi”, in ji shi.

“Ku tuna cewa tufafinku alama ce ta ƙasa da jihar da kuka fito, don haka ku kiyaye duk wani abu da zai bata muku suna.”

Kazalika, ya kuma yi kira ga maniyyatan su kauce wa yawan kashe kuɗaɗe babu lissafi, sannan su lura sosai wajen yin canji domin kauce wa faɗa wa hannun ’yan damfara.

Gobarar tankar mai ta yi ajalin mutum 18 a Enugu

An yi taron Maulidin ƙasa duk da gargaɗin harin ’yan ta’adda a Kano

An saki Falasɗinawa 200 da ke ɗaure a Isra’ila

Tinubu zai tafi taron makamashi a Tanzania