‘Alherin da ke cikin sana’ar yankan taya sai wanda yake yi ke gani’
Shugaban Layin ’Yan Taya na Babbar Kasuwar Gombe Alhaji Alhassan Ahmed ya bayyana sana’ar yankan taya da cewa sana’a ce mai cike da alherai, da sai wanda yake cikinta zai gane hakan. Alhaji Alhassan Ahmed ya bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa da Aminiya, inda ya ce idan suka samu tallafi daga wajen gwamnati […]
Shugaban Layin ’Yan Taya na Babbar Kasuwar Gombe Alhaji Alhassan Ahmed ya bayyana sana’ar yankan taya da cewa sana’a ce mai cike da alherai, da sai wanda yake cikinta zai gane hakan.
Alhaji Alhassan Ahmed ya bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa da Aminiya, inda ya ce idan suka samu tallafi daga wajen gwamnati babu tayar da ba za su sarrafa ba, i aka cire wacce take da waya a cikinta.
Shugaban ya ce ya shafe shekara sama da 30 yana wannan sana’a ta yankar taya kuma ta rufa masa asiri fiye da yadda mutane ke tunani; domin kamar yadda ya ce ‘alherinta sai wanda yake cikinta.’
Ya ce tayoyin manyan motoci suka fi sarrafawa domin sun fi tsoka, maimakon tayoyin kananan motoci. “Kuma wannan sana’a ko jarin mutum bai da yawa sosai zai iya farawa har ya bunkasa,” inji shi.
Alhaji Alhassan Ahmed, ya ce ya koya wa yara masu yawa yadda ake sarrafa taya wadanda yanzu haka suke cin gashin kansu a wannan sana’a kuma sun dauki yaran da suke koyawa.
Sai dai ya ce duk da haka akwai bukatar kayan aiki na zamani da idan suka samu tallafi daga wajen gwamnati za a yi mamakin yadda za su rika sarrafa tayoyin da ake amfani da su a jikin motoci da kuma wasu na’o’in tayoyi da robobi.
Ya ce, yanzu da karfinsu suke aiki ta hanyar amfani da wuka; “Amma da a ce za mu samu kayayyakin aiki na zamani, to da kowa sai ya sha mamaki,” inji shi.
Da ya juya kan matasan da suke raina sana’a ya yi kira a gare su cewa su rungumi sana’a musamman yanka taya don yana ganin babu sana’ar da take da rufin asiri irinta.
Daga nan sai ya shawarci masu gudanar da sana’o’i su rike gaskiya a sana’o’insu; kada su sa ha’inci domin idan suka rike gaskiya za su yi mamakin yadda sana’ar za ta kai su a rayuwa.
Sai ya nemi gwamnati ta kai wa masu wannan sana’a ta yankan taya irin tallafin da take bai wa masu kananan sana’o’i saboda a cikinsu akwai wadanda suka gamu da jarrabawa ta rayuwa dan abin da suke da shi ya kare kuma rayuwa dole sai da tallafi.