Alherin tukin Keke Napep ya fi na acaba –Dahiru Hassan
Dahiru Hassan shi ne shugaban kungiyar Direbobin Keke Napep reshen karamar Hukumar Jos ta Arewa da ke jihar Filato. A tattaunawarsa da wakilinmu kwanakin baya, ya bayyana nasarorin da suka samu da kalubalen da suke fuskanta da kuma yadda sana’arsu take ci gaba da kawo zanzuwar zaman lafiya a jihar. Ga yadda tattaunawar ta kasance: […]
Dahiru Hassan shi ne shugaban kungiyar Direbobin Keke Napep reshen karamar Hukumar Jos ta Arewa da ke jihar Filato. A tattaunawarsa da wakilinmu kwanakin baya, ya bayyana nasarorin da suka samu da kalubalen da suke fuskanta da kuma yadda sana’arsu take ci gaba da kawo zanzuwar zaman lafiya a jihar. Ga yadda tattaunawar ta kasance:
Aminiya: Mene ne ya ja hankalinka zuwa sana’ar tukin Keke Napep?
Kafin wannan sana’ar, ina sana’ar acaba ne, wanda albarkacinta har na kai ga zama shugaban kungiyar ’yan acaba reshen karamar Hukumar Jos ta Arewa. Daga lokacin da gwamnatin jihar Filato ta kafa dokar hana acaba a garin Jos da kewaye ne, wato kimanin shekaru biyu da suka wuce ke nan, sai na shiga sana’ar tukin keke Napep. Muna cikin wannan ne zaben kungiyarmu ya taso. Kuma Allah Ya sa aka zabe ni a matsayin shugaban kungiyar reshen karamar Hukumar Jos ta Arewa. Duk da cewa an zabe ni shugaba amma hakan bai hana ni ci gaba da tuka Kekena ba kamar yadda na saba.
Aminiya: Wadanne irin nasarori kake ganin kungiyarku ta samu kawo yanzu?
A gaskiya mun gode wa Ubangiji bisa nasarorin da muka samu albarkacin wannan sana’ar. Nasarar farko da muka fara samu ita ce mun taimaka wajen hadin kan dukkan membobinmu da kuma al’ummar Jos da kewaye, musamman bangaren zirga-zirga da kuma dawo da yarda da juna a tsakaninsu. Misali a yanzu sakamakon yadda muke zirga-zirga da fasinjojin babu inda ba a shiga a cikin wannan garin. Wanda akasin haka ne a lokacin da muke sana’ar acaba, saboda akwai unguwanni da dama da ba kowane ba ne ke iya shiga ba saboda barazanar tsaro da kuma rashin yarda da juna a tsakanin al’ummar garin nan mabambanta. Nasara ta biyu kuma ita ce, sana’armu ta samar wa dimbin matasa ayyukan yi. A lokacin da aka hana sana’ar acaba a jihar nan, hankalinmu kowa ya tashi musamman ta la’akari da yawan kudin da mutum zai tanada kafin ya mallaki Keke Napep. Amma Alhamdulillah, domin daga bisani mun samu mutane masu kishi wadanda suka taimaka mana wajen mallakar wadannan Kekuna ta hanyar ba mu bashi, muna biya kadan-kadan. A yanzu muna da mutane fiye da 20 da suke taimaka mana ta wannan fuskar, akwai mutum daya da ya ba da bashin Kekuna akalla guda 200 da sauransu. A gaskiya babu abun da za mu ce wa wadannan mutane sai dai Allah Ya saka masu da alherinsa. Babu shakka al’umma da kuma gwamnatin jihar Filato suna bayyana goyon bayansu a gare mu saboda a lokacin da muke sana’ar acaba ana samu munanan hadarurruka a garin nan akai-akai, amma yanzu sakamakon kawo Keke Napep matsalar ta ragu matuka. Bayan wannan, a baya mata da kananan yara suna fuskantar matsaloli wajen hana babura, amma yanzu suna shiga Keke Napep ba tare da wata matsala ba. Hakazalika ‘yan kasuwa suna shiga tare da kayayyakinsu ba tare da wata fargaba ba kamar irin wanda ake fuskanta lokacin acaba ba. Har ila yau sana’ar tana kawowa masu gyaransa ayyukan yi da kuma masu sayar da kayayyakinsa wato (Spare parts) da sauransu. Kuma daga fara wannan sana’a zuwa yanzu, akwai wadanda na sani da dama sun gina gidan kansu, wasu sun yi aure, wasu kuma suna rike da iyayansu.
Aminiya: A karshe wane sako ko kira kake da shi zuwa ga gwamnati da kuma sauran masu wannan sana’ar?
Muna rokon gwamnati ta gyara mana hanyoyin cikin garin Jos. Musamman hanyar da ta tashi daga ‘Yan taya zuwa Nasarawa da hanyar Zololo zuwa Nasarawa zuwa Dutse Uku. Sauran su ne hanyar ‘Yan shanu da Tudun Wada da hanyar Jenta Adamu da hanyar unguwar Jarawa da sauransu. Kirana ga matasa shi ne su tashi tsaye, su rike wannan sana’ar da gaskiya da kuma amana, idan suka yi haka za mu ci gaba da samun nasarori da albarkatun da ke cikinta.