Ali kwara ya yi artabu da ’yan fashi a Jigawa
Sananen mafaraucin barayin nan, Alhaji Ali kwara ya yi artabu da ’yan fashi da makami a Jihar Jigawa, inda ya samu nasarar harbe daya daga cikinsu saura kuma suka tsere a wata musayar wuta da yaran Ali kwaran suka yi da ’yan fashin a kan hanyar Kiyawa zuwa Azare a ranar Litinin da ta gabata.Da […]

Sananen mafaraucin barayin nan, Alhaji Ali kwara ya yi artabu da ’yan fashi da makami a Jihar Jigawa, inda ya samu nasarar harbe daya daga cikinsu saura kuma suka tsere a wata musayar wuta da yaran Ali kwaran suka yi da ’yan fashin a kan hanyar Kiyawa zuwa Azare a ranar Litinin da ta gabata.
Da yake hira da manema labarai a Dutse lokacin baje kolin gawar dan fashin a Sakatariyar Gwamnatin Jihar Jigawa ga manema labarai, Ali kwara ya ce ’yan fashin sun kwato motar da suke kokarin yin fashi da ita ce daga hannun wani mazaunin Abuja inda suka nufo don aikata fashi da ita.
Ya ce ’yan sanda sun amshe motar kirar Toyoa Camry mai lamba AH 243 ABJ, ya ce sun samu nasarar kwato albarusai na bindigar AK47 guda 136 da na karamar bindiga guda takwas da bindigogi biyu, daya ta wanda suka harbe, daya kuma wani daga cikin ’yan fashin ne ya yasar ya gudu.
Da yake amsa tambayoyin manema labarai Alhaji Ali kwara ya ce kamar yadda wasu kafafen watsa labarai suke azuzutawa cewa yana ba wasu jami’an tsaro taimakon asiri har ma wasu suna ikirarin cewa su yaransa ne shi yake ba su asirin da suke tinkarar ’yan Boko Haram, ya ce ba ya da wata alaka da jami’an tsaron hadin gwiwa na JTF balantana a ce yana ba su asiri.
Ya ce ba shi da wani abin dogaro sai Allah, kuma ba ya guru ko laya illa yaka yi addu’a wadda ita ce jarinsa. “Kuma ba ni da wata alaka da masu fafitikar Boko Haram kamar yadda wasu suke fada cewa ina da alaka da ’yan Boko Haram domin bata min suna,” inji shi.