Ali Musa: Makahon da ya kware wajen saka

Ali Musa wani makaho ne da ya kware a sana’ar saka, dan asalin karamar Hukumar Kaltungo ta Jihar Gombe, ya gana da Aminiya game da tarihinsa da kuma kalubalen da yake fuskanta: Ga yadda hirar ta kasance: Aminiya: Za mu so mu ji takaitaccen tarihinka? Sunana Ali Musa, an haife ni a karamar Hukumar Kaltungo […]

Ali Musa: Makahon da ya kware wajen saka

Ali Musa wani makaho ne da ya kware a sana’ar saka, dan asalin karamar Hukumar Kaltungo ta Jihar Gombe, ya gana da Aminiya game da tarihinsa da kuma kalubalen da yake fuskanta: Ga yadda hirar ta kasance:

Aminiya: Za mu so mu ji takaitaccen tarihinka?

Sunana Ali Musa, an haife ni a karamar Hukumar Kaltungo ne a Jihar Gombe. To dama dai ni na dade ina son na koyi sana’ar saka abin sa Fure wato (Flower Base) ban san yadda zan yi ba, don na kai shekara hudu amma sai a shekarar 2015 Adamu Isiaku Gombe Shugaban kungiyar mu ta Makafi ta kasa shi ne ya yi mini hanya ya tura ni Legas wata Makarantar mu ta Makafi na je nayi shekara daya a can na koyi wannan sana’ar da wasu daban ciki har da Noma da kiwo.
Aminiya: Wannan makaranta ta koyar sana’a ce ta masu makanta ko ya ya makarantar take?
Eh, makaranta ce ta musammam da ake ce mata Nigeria Falm Craft Centre for the Blind da ke Osheri a Legas inda na shekara daya na koyi sana’ar.
Aminiya: A lokacin da ka samu tafiya wannan makaranta akwai wanda ya baka tallafi dan ganin za ka je koyon sana’a ne?
Akwai tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Gombe Alhaji Bala Muhammad Magaji Magajin Garin Gombe ya ba ni tallafi a lokacin da na nuna masa Fom din makarantar. Har ila yau, akwai wani Alhaji Mamuda da ke Unguwar Arewa shi ma ya ba ni taimako, sai tsohon shugaban karamar hukumar Gombe Malam Babawuro duk sun taimaka mini kafin na gama koyon wannan sana’ar.
Aminiya: Kafin koyon sana’ar saka, akwai wata sana’a da ka iya?
A’a na koyi sana’o’i daban-daban da suka hada da yin sabulu irin na sandan nan mai hoton Agwagwa irin na da Morning Fresh da Turaren daki da na Mota da kuma yadda ake hada Fiya-fiya har da yadda ake kiwon kajin gidan Gona da Dabbobi da yadda ake yi Izal duk an koya mana kuma na iya su duka da zan samu jari da babu batun yin bara kai har wasu ma’aikata ma zan dauka.
Aminiya: Masu koya muku wadannan sana’oi din masu ido ne ko makafi ne?
Akwai makafi akwai masu ido domin shugabar makarantar tana da ido, mataimakin ta ne makaho haka malaman su ma akwai masu gani, akwai makafi.
Aminiya: Idan ka saka wannan abin sa furen ya kake yi wajen sayar da shi?
Ina sayarwa ne kama daga dubu biyu da dari biyar zuwa dubu biyu bisa ga girmansa ne domin kala-kala ne akwai mai dungu biyu,akwai mai hudu mai ukun ina sayar da shi dubu daya da dari biyar kafin na hada kowanne guda yakan ta shi kamar Naira dubu daya da dari biyu wani da dari biyar.
Aminiya: Ta yaya kake kai wa kasuwa don sayarwa?
Eh, na hada kai da wani dan kasuwa ne a nan Gombe mai suna, Alhaji Gambo Bonanza a tsohuwar Kasuwar Gombe shi yake sayar mini da abubuwa suka cakude sai wani Alhaji Sani a babbar Kasuwar ta Gombe ya ce ina kai masa shi ne yanzu wanda nake kai wa yake sayar mini.
Aminiya: Wane kira kake da shi ga matasa wadanda zuciyarsu ta mutu?
Kirana shi ne dogara da abin hannun wani bai dace ba ko masu nakasa irina da kake gani suna yawon bara wasun dole ne ba yadda suka iya, amma masu gani da zuciyarsu ta mutu su tashi tsaye wajen neman na kansu suna dogara da abin da za su samu ba wanda wani zai basu ba.
Aminiya: Da a nan Gombe akwai masakar makafi da ta butu, mene ne kiranka ga gwamnati na ganin an farfado da ita don amfanar wanda ba su da hanyar zuwa wani gari don koyon irin wannan sana’ar?
Babban kira na shi ne ina son gwamnati da tayi mana kokari
ba sai lailai a masana’antar mu ba, ko a makarantun cikin gari idan aka samu cibiyar koyar da sana’ar, ba makaho kadai ba hatta masu ido su ma za su amfana. Ka ga hakan zai kawo karshen zaman banza musammam a tsakanin matasanmu.
Aminiya: bangaren karatu, ko ka taba yin karatun boko?
Na yi karatun boko matakin firamare tun ina gani kafin larurar makanta ta same ni, amma ban gama ba makanta ta same ni da yake a kauye nake sai rashin gata ya hana ni kammala karatun, sai kuma yanzu da na je Legas makarantar wannan sana’ar.
Aminiya: A ina kake samun kudi don sayen kayan aikin sakar nan?
Wani lokacin Barar nan dai da ba na so ita nake dan yi kadan-kadan, idan na samu kudin sayen kayan aiki na gama na sayar to wani lokacin ba na fita barar shi ke nan na samu yadda zan yi.
Aminiya: Mene ne burinka?
Fata na shi ne masu hannun da shuni suna taimaka mana suna jan mu a jiki idan suka bude kamfani suna daukar mu aiki hakan zai sa mu samu hanyar dogara da kai da kuma kaucewa yin barace-baracen da ba’a so a gefen titi in sha Allah.