Ali Ndume, Rufa’i Hanga sun zama jagororin Majalisar Dattawa

Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ya bayyana Sanata Ali Ndume da Sanata Rufa’i Hanga cikin ƙunshin jagororin masu rinjaye da marasa rinjaye na Majalisar. A safiyar Talatar nan ne Sanata Akpabio ya sanar da Sanata Ali Ndume daga jihar Borno a matsayin mai tsawatarwa na ɓangaren masu rinjaye. Kuma ya sanar  da Sanata Rufa’i Hanga […]

Ali Ndume, Rufa’i Hanga sun zama jagororin Majalisar Dattawa

Sanata Ali Ndume mai wakiltar Borno ta Kudu

Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ya bayyana Sanata Ali Ndume da Sanata Rufa’i Hanga cikin ƙunshin jagororin masu rinjaye da marasa rinjaye na Majalisar.

A safiyar Talatar nan ne Sanata Akpabio ya sanar da Sanata Ali Ndume daga jihar Borno a matsayin mai tsawatarwa na ɓangaren masu rinjaye.

Kuma ya sanar  da Sanata Rufa’i Hanga daga jihar Kano a matsayin  mataimakin mai tsawatarwa ɓangaren marasa rinjaye.

Dalilin da na fadi zaben Shugaban Majalisar Dattawa — Abdulaziz Yari

Sanata Akpabio ya zama sabon shugaban Majalisar Dattawa

Sauran jagororin da Sanata Akpabio ya sanar sun haɗa da shugaban masu rinjaye, Opeyemi Bamidele, mataimakin shugaba, David Umahi, da mataimakin mai tsawatarwa ɓangaren masu rinjaye Lola Ashiru.

Daga ɓangaren maarasa rinjaye kuwa, Sanata Akpabio ya sanar da Simon Davon Mwadkwon a matsayin shugaba, Oyewumi Olalere a matsayin mataimakin shugaba, da Darlington Nwokwocha a matsayin mai tsawatarwa.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan