Ali Nuhu da Zango sun sasanta
Masu magana sukan ce komai ya yi farko zai yi karshe, kuma duk abin da ya yi tsanani to zai yi sauki, wadannan maganganu tabbas haka suke, domin a yanzu Ali Nuhu da Adam A Zango sun sasanta bayan rikicin da ya barke tsakaninsu. Idan ba a manta ba al’amarin ya taso a lokacin da […]
Masu magana sukan ce komai ya yi farko zai yi karshe, kuma duk abin da ya yi tsanani to zai yi sauki, wadannan maganganu tabbas haka suke, domin a yanzu Ali Nuhu da Adam A Zango sun sasanta bayan rikicin da ya barke tsakaninsu.
Idan ba a manta ba al’amarin ya taso a lokacin da Rahama Sadau ta shiga shafinta na Istagram ta gasa wa Adam Zango munanan kalamai bisa zargin ya cire ta a fim dinsa mai suna ‘Duniya Makaranta’, inda dan gani kashenin Zango mai suna Ali Artwork ya rama a kan Ali Nuhu bisa tsammanin shi ne ya sanya ta aikata hakan, duk da jarumar ta ba Zango hakuri bisa tilastawar Ali Nuhu, amma hakan bai hana Zango ya gana da ’yan jarida sannan ya tabbatar da yanke duk wata dangantaka tsakaninsa da Ali Nuhu ba.
Hakan ya sanya kwamitin ladaftarwa na kungiyar MOPPAN ya dakatar da Rahama tsawon wata shida.
Kwatsam ranar Litinin sai Zango ya shiga shafin Instagram ya ba Ali Nuhu hakuri, al’amarin da ya ba mutane da yawa mamaki, ya kuma dadada musu.
Ya ce: “Salamu alaikum jama’a. Ina so in yi amfani da wannan dama domin in bai wa Ali Nuhu tare da magoya bayansa hakuri a kan abin da ni da Ali Artwork muka yi masa. Sannan ina bai wa jama’ar Kannywood hakuri a kan tashin hankali da rikicin ya janyo musu, ina fatan hakan zai kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a masana’antar baki daya.”
Wannan ta sanya Ali Nuhu shi ma ya yafe wa Zango, inda ya rubuta a shafin Instagram dinsa kamar haka: “Na ga sako @de_prince_zango. Allah Ya kara kiyayewa Ya kuma ba mu zaman lafiya. Duk wanda ransu ya baci sakamakon abubuwan da suka faru kuma Allah Ya ba su hakuri. Magoya bayana da na Adam don Allah a mance komai a zauna lafiya. Na ki cewa komai tun farko saboda kimar Adam a wurina ta wuce mu fito a ji mu a duniya. Allah Ya ba mu zaman lafiya da ci gaba a masana’antarmu, amin.”
Daga nan aka shirya jaruman za su gana da juna a ranar Litinin, sai tafiya zuwa Nijar ta taso wa Ali Nuhu, inda aka sanya shekaranjiya Laraba a matsayin ranar zaman.
Abu Sarki mai magana da yawun jarumi Adam A. Zango ya ce sun fahimci tun bayan dangantaka ta sukurkuce tsakanin jaruman biyu wadansu matsaloli suka rika tasowa, hakan ya sanya suka sasanta tsakaninsu.
“A halin yanzu yaran jaruman (Ali da Zango) ba sa samun aiki a wurin magoyan juna, wanda hakan ya kawo nakasu, domin ba sa samun wani kudin shiga. Mun yi tunanin hakan ba zai haifar mana da da mai ido ba, sai muka ga sasantawa ce mafi a’ala gare mu da gare su da kuma Kannywood gaba daya.” Inji shi.