Ali Nuhu na godiya bisa ta’aziyar rasuwar mahaifinsa
Tauraro a masana’artar fina-finai ta Kannywood, Ali Nuhu wanda mahaifinsa ya rasu ya yi godiya ga dimbin mutanen da suka taya shi jaje. Masoya da abokan sana’ar Ali Nuhu a Kannywood da sauransu sun yi ta mika ta’aziyya tare da aika masa sakonnin tausayawa da addu’o’i bisa rashin mahaifin nasa. Aminiya ta ruwaito cewa mahaifina […]
Tauraro a masana’artar fina-finai ta Kannywood, Ali Nuhu wanda mahaifinsa ya rasu ya yi godiya ga dimbin mutanen da suka taya shi jaje.
Masoya da abokan sana’ar Ali Nuhu a Kannywood da sauransu sun yi ta mika ta’aziyya tare da aika masa sakonnin tausayawa da addu’o’i bisa rashin mahaifin nasa.
Aminiya ta ruwaito cewa mahaifina Ali Nuhun, wato Marigayi Nuhu Poloma wanda tsohon dan siyasa ne ya rasu ne a jihar Gombe bayan jinya da ya yi.
Da yake mika sakon godiyarsa ga jama’a, Ali Nuhu ya wallafa a shafukansa na sa da zumunta cewa, “Ni da ’yan uwana muna mika sakon godiya ga dukkan wadanda suka yi mana ta’aziyyar mahaifinmu da ya rasu.
“Mun gode Allah Ya saka da alheri. Na gode da soyayya da kaunar da na samu daga gare ku gaba daya, Allah Ya bar zumunci.”
Yayin da mahaifin jarimin, wato Marigayi Nuhu Poloma dan asalin jihar Gombe ne, mahaifiyarsa Hajiya Fatima Karderam Digema — wadda daga sunanta ya samo sunan kamfaninsa na fina-finan Hausa wato FKD Productions Limited, ’yar asalin Bama ce a jihar Borno.
Shi kuma Ali Nuhu, wanda aka fi sani da Sarki a masana’antar Kannywood, ya taso a garin Jos inda ya yi karatu da kuma Kano inda daukaka ta same shi.