Ali Nuhu ya zama jakadan ‘New Omo’

Shahararren jarumin fina-finan Hausa Ali Nuhu ya zama jakadan kamfanin New Omo. An kaddamar da jarumin a matsayin jakadan kamfanin ne a Legas a kwanakin baya.An kaddamar da jarumin ne tare jaruma Funke Akindele da kuma Chion Akpotha.Daraktan Kamfanin Unileber na Najeriya wadanda suke samar da Omo, Dabid Okeme ya ce sun yi hakan ne […]

Ali Nuhu ya zama jakadan ‘New Omo’
Ali Nuhu ya zama jakadan ‘New Omo’

Shahararren jarumin fina-finan Hausa Ali Nuhu ya zama jakadan kamfanin New Omo.
An kaddamar da jarumin a matsayin jakadan kamfanin ne a Legas a kwanakin baya.
An kaddamar da jarumin ne tare jaruma Funke Akindele da kuma Chion Akpotha.
Daraktan Kamfanin Unileber na Najeriya wadanda suke samar da Omo, Dabid Okeme ya ce sun yi hakan ne don nuna wa jama’a muhimmancin sabon ‘New Omo’.
Ali Nuhu ya yaba wa ’yan fim da masoyansa kan goyon bayan da suke ba shi.