Ali Sarkin Mota, Direban Sardauna ya rasu
Allah Ya yi wa Alhaji Ali Sarkin Mota, Direban Sardauna Ahmadu Bello rasuwa.
Allah Ya yi wa Alhaji Ali Sarkin Mota, Babban Direban Sardauna, Alhaji Ahmadu Bello rasuwa.
Iyalai da makwabtan Alhaji Ali Sarkin Mota sun tabbatar da rasuwarsa ne da safiyar Laraba, bayan fama da rashin lafiya.
- Abubuwa 14 da ya kamata ku sani kan tsohon shugaban Chadi, Idriss Deby
- A kan idona sojoji suka kashe Sardauna —Sarkin Mota
- Yadda na tuka Sarauniyar Ingila a Najeriya –Ali Sarkin Mota
Iyalansa sun sanar cewa za a yi jana’izarsa bayan Sallar Azahar a Babban Masallacin Sultan Bello da ke Unguwar Sarki, Kaduna.
Marigayi Ali Sarkin Motan Sardauna, na daga cikin daidaikun makusantan Sardaunan da a kan idonsu sojoji suka yi wa Sardauna juyin mulki tare kashe shi a shekarar 1966.
A wata hirar da Aminiya ta yi da shi a lokacin rayuwarsa, marigayin ya bayyana mata tun daga yadda sojoji suka kutsa a cikin gidan Sardaunan cikin taskar dare, suna barin wuta, har suka kashe shi tare da mai daikinsa.
Baya ga rika ubangidansa Sardauna wanda ya nada shi Sarkin Mota, Alhaji Ali ya kuma tuka Sarauniyar Ingila da shugabannin kasashen duniya da dama da suka ziyarci Najeriya a zamanin Sardauna.
Marigayi Ali Sarkin mota ya rasu ya bar ’ya’ya da jikoki da dama, kuma ya kasance abin girmamawa ga makwabta da dattawan Arewa. Ya shahara da lakabin Kawu a tsakanin ’ya’ya da makwabta, manya da kanana.