Ali Wakili ya raba wa mutane 350 jari a Bauchi
Shugaban Kwamitin Rage radadin Talauci a Majalisar Dattijai ta kasa, Sanata Ali Wakili ya raba kayyakin koyon sanao’i, inda ya raba wa mutane 350 jari masu kananan sana’o’i maza da mata a karamar Hukumar Bauchi domin su kara su bunkasa sana’arsu. Wadanda suka samu tallafin jarin daga sanatan sun hada da masu sana’ar yin masa […]
Shugaban Kwamitin Rage radadin Talauci a Majalisar Dattijai ta kasa, Sanata Ali Wakili ya raba kayyakin koyon sanao’i, inda ya raba wa mutane 350 jari masu kananan sana’o’i maza da mata a karamar Hukumar Bauchi domin su kara su bunkasa sana’arsu.
Wadanda suka samu tallafin jarin daga sanatan sun hada da masu sana’ar yin masa da tuyar kosai da abinci da kayan tireda da sauran kananan sana’o’i.
Rabon shi ne rabo na bakwai a mazabar sanatan bayan tun da fari ya yi irin wannan rabo a kananan hukumomin Dass da Tafawa Balewa da bogoro da Toro da Alkaleri da Kirfi da kuma yanzu karamar Hukumar Bauchi.
Da yake mika tallafin Naira Dubu goma ga kowannensu a garin Bauchi, Mallam Ali Wakili ya ce wannan yunkuri na daga cikin ayyukan da yake yi a mazabarsa, inda ya ce yunkurin kawar da talauci, ta hanyar inganta sanao’in tunda ita ce babbar hanyar kawar da talauci, kuma hakan zai karfafa wa masu kananan sana’o’i gwiwa, wadanda ba su da lalaci, domin su samu habakar tattalin arziki.
Wakili ya bukaci matasan da su yi kyakykyawar amfani da kayayyakin domin kyautata rayuwarsu dana iyalansu , sannnan ya bai wa mutanen mazabarsa tabbacin cewa zai ci gaba da yin ayyukan da za su inganta rayuwar al’umma.
Ya jaddada kudirin majalisun tarayya domin ganin an dawo da ’yancin cin gashin kai wa kananan hukumomimnmu, sannan ya bukaci al’umma da majalisun jihohi da su amince da wannan yunkuri domin samun nasara da ci gaban yankunan karkara.
Bikin ya samu halartan Shugabannin Jamiyyar APC daga mazabar sanatan, a bayan an ba da horo da irin wannan tallafi a mazabun Kirfi da Alkaleri da Bauchi da Dass da Tafawa Balewa da Bogoro da Toro.
A jawabansu dabam-dabam dukkan shugabannin sun yaba wa kan saboda yadda yake kulawa da al’ummar mazabar sa sannan suka yi kira ga wadanda suka ci moriyar tallafin da su yi amfani da shi yadda ya kamata da nufin bunkasa tattalin arzikinsu.