Alison Madueke na neman kotu ta hana Diezani amfani da sunansa

Alison Madueke ya shigar da karar ne shekara uku bayan mutuwar aurensu da tsohuwar ministar man fetur, Diezani.

Alison Madueke na neman kotu ta hana Diezani amfani da sunansa

Rear Admiral Alison Amaechina Madueke, ya garzaya kotu neman ta hana tsohuwar matarsa kuma tsohuwar ministar kudin Najeriya Diezani, amfani da sunansa.

Alison Madueke ya shigar da karar ne shekara uku bayan rabuwar aurensu da tsohuwar ministar.

Yana rokon kotu ta hana Diezani amfani sunansa, Alison da na mahaifinsa Madueke ta koma amfani da sunanta ta da na mahaifinta, Agama, kamar yadda sunanta yake kafin su yi aure..

Ya kuma bukaci babbar kotun Jihar Legas ta umarci Diezani ta wallafa sanarwar daina amfani da sunansa da na mahaifinta ta koma dunya na asali, a manyan jaridun Najeriya da kuma na kasar Birtaniya inda take a halin yanzu.

Tun a watan Mayun 2015 Allison da Diezani suka daina zama tare bayan ta sauka daga kujerar minista kafin daga bisani su rabu a watan Nuwamba, 2021.

Rear Admiral Madueke ya shaida wa kotu cewa ci gaba da amfani da sunansa da Diezani take yi na jefa dukiyarsa cikin hadari.

Hakazalika yana fuskantar barazanar shari’a a musamman yayin shari’ar manyan laifukan rashawa da almundahana da take a Najeriya da Birtaniya.

Ya bayyana cewa amfani da sunansa da take ci gaba da yi na sa wasu su dauka cewa har yanzu suna tare wanda hakan yake zubar masa da kima a cikin al’umma.

Duk da rabuwar aurensu da kuma takardar da lauyoyin Alison Madueke suka aika wa Diezani a 2023, na neman hana ta amfani da sunansa, har yanzu ba ta daina ba.

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya

Kano: Kwamishinan da Abba ya tsige ya koma Jam’iyyarAPC

Amurka za ta dawo wa Najeriya N80bn da ta ƙwato daga Diezani