Aliyu Aliyu, Bauchi
Mukkadashin Gwamnan Jihar Taraba Alhaji Garba Umar ya nuna bacin ransa kan yadda wasu matasa suka far wa wasu motocin da ke cikin ayarin wadanda suka je tarbo shi daga filin jirgin saman Jalingo. Alhaji Garba Umar wanda yake bayani ga manema labarai kan burinsa na tsayawa takarar Gwamnan Jihar ya ce ba za a […]
Mukkadashin Gwamnan Jihar Taraba Alhaji Garba Umar ya nuna bacin ransa kan yadda wasu matasa suka far wa wasu motocin da ke cikin ayarin wadanda suka je tarbo shi daga filin jirgin saman Jalingo.
Alhaji Garba Umar wanda yake bayani ga manema labarai kan burinsa na tsayawa takarar Gwamnan Jihar ya ce ba za a amince da irin wannan hali ba kuma jami’an tsaro za su gudanar da bincike don gano wadanda ke da hannu a lamarin.
Ya ce dole ’yan siyasa su gudanar da harkokinsu yadda doka ta tanada ta hanyar bai wa kowa damar tsayawa neman kowace kujera a jihar da kasa baki daya.
Ya ce ana neman dauwamammen zaman lafiya a jihar saboda haka akwai bukatar ’yan siyasa su ja kunnen magoya bayansu su guji tayar da fitina.
Alhaji Garba ya isa Jalingo ne daga Abuja inda ya sayi takardar neman tsayawa takarar Gwamna a Sakatariyar Jam’iyyar PDP ta kasa da ke Abuja inda dubban jama’a suka tarbe shi.
Mukaddashin Gwamnan ya ce ya kafa kwamitin takararsa mai Alhaji Ahmed Yusuf a matsayin Darakta Janar na kamfe, sai Rabaran Owolowo shugaban kamfen din.
Ya ce an yi raba daidai kan mukaman da wakilan kwamitin tsakanin Kiristoci da Musulmi. Ya ce wannan ya nuna yadda yake bayar goyon baya kan tafiyar da harkokin jihar ta nuna adalci a tsakanin al’umma.