Aliyu Tilde ya yi murabus daga kwamishinan ilimi

Kwamishinan Ilimi na Jihar Bauchi, Dokta UsmanAliyu Tilde, ya ajiye mukaminsa   Aliyu Tilde ya tabbatar wa Aminiya ajiye mukaminsa na gwamnati, bayan wakilinmu ya tuntube shi ta waya. Zulum Ya Ziyarci ’Yan Gudun Hijirar Borno A Nijar Zan Tona Asirin Wike Idan… —Dogara Tilde ya shaida wa wakilinmu ta waya cewa, “Gsaskiya ne ya ajiye […]

Aliyu Tilde ya yi murabus daga kwamishinan ilimi

Kwamishinan Ilimi na Jihar Bauchi, Dokta UsmanAliyu Tilde, ya ajiye mukaminsa  

Aliyu Tilde ya tabbatar wa Aminiya ajiye mukaminsa na gwamnati, bayan wakilinmu ya tuntube shi ta waya.

Tilde ya shaida wa wakilinmu ta waya cewa, “Gsaskiya ne ya ajiye mukamina kuma na wallafa a shafina na  Facebook.

“Kafin nan na rubuta wa gwamna takardar neman izinin yin tafiya wurin wani abokina da ke matukar bukatar hidima daga gare ni, kuma Alhamdulillah gwamna ya amince.”

A sakon da Tilde ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce, “Yau (Litinin) 5 ga Dismba 2022, na samu wasika daga Sakataren Gwamnatin Jiha cewa Mai Girma Gwamna ya amince da ajiye mukamina.

“Da haka wa’adina a matsayin Kwamishinan Ilimi ya zo karshe, kuma ina farin cikin da hakan a kasance kyakkyawan karshe a aikin da na samu nasarorin da ba zan gushe ba ina gode wa Allah a kai ba.” 

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja

Tirela murƙushe ’yan sanda 3 har lahira

An ƙwace kwantainoni 54 mallakin Emefiele

Fulawa da dabbobin Fadar Shugaban Ƙasa za su ci N125m a 2025