Aljan ya kama wadanda suka addabi Taraba
Fitaccen mai kama barayin nan Alhaji Shehu Usman Aljan ya samu nasarar kama wadanda suka addabi Jihar Taraba da fashi da makami da sace-sacen shanu da garkuwa da mutane ciki hard a wanda ake zargi da jagorancin gungun masu satar mutane da suka sace mahaifiyar Mataimakin Gwamnan Jihar Taraba, Hajiya Belli Manu wata uku da […]
Fitaccen mai kama barayin nan Alhaji Shehu Usman Aljan ya samu nasarar kama wadanda suka addabi Jihar Taraba da fashi da makami da sace-sacen shanu da garkuwa da mutane ciki hard a wanda ake zargi da jagorancin gungun masu satar mutane da suka sace mahaifiyar Mataimakin Gwamnan Jihar Taraba, Hajiya Belli Manu wata uku da suka wuce.
Alhaji Shehu Usman Aljan wanda yake yawon kama barayin shanu da masu garkuwa da mutane a sassan jihohin kasar nan ne ya kama wanda ake zargin tare da wadansu fitattun barayi 40 a sassan jihar.
Wadanda aka kama ana zargin su ne shugabanin ’yan fashi da makami da satar mutane da shanu da suka addabi sassan jihar, kuma an kama su ne a kananan hukumomin Donga da Bali da Gassol da Gashaka da Takum inda matsalar satar mutane da fashi da satar shanu suka zama ruwan dare.
Alhaji Shehu Aljan ya kuma kama wadanda ake zargin da manyan bindigogi da alburusai masu yawa da suke amfani da su wajen aikata miyagun laifuffukansu da halaka jama’a.
Daga cikin wadanda ake zargi da satar mutane da Shehu Aljan ya kama akwai Shede da Charles wadanda ake zargin su ne kan gaba wajen sace mutane a jihar.
Ana zargin Shede ne ya jagoranci barayin mutune zuwa gidan mahaifiyar Mataimakin Gwamnan Taraba da ke garin Mutum-Biyu inda suka sace ta kuma suka rike ta na tsawon kwana shida kafin su sake ta bayan an ba su miliyoyin Naira a matayin kudin fansa.
Shehu Aljan ya shida wa manema labarai cewa wadanda ake zargin sun sace sama da mutum 20 a garuruwan Tella da dan’anacha da Mutum-Biyu da Chull da Maihula da Garba Chede da Marabar Baissa da sauran garuruwan jihar, inda suka karbi miliyoyin Naira daga ’yan uwan wadanda suka sace.
Shehu Aljan ya ce ’yan uwan daya daga cikin masu satar mutanen da ya kama mai suna Charles sun biyo dare suka kawo masa cin hancin Naira dubu 800 domin ya sake shi, amma sai ya karbi kudin ya sa aka dauki hoton kudin da wanda ake zargi da satar mutanen sa’annan ya tasa keyar Charles zuwa hedkwatar ’yan sadan Jihar Taraba ya mika shi gare su.
Ya ce amma abin mamaki daga bisani, sai ’yan sandan suka sake shi, lamarin da ya ce ya ba shi mamaki matuka.
Shehu Aljan ya ce akwai bukatar ganinduk wanda aka kama da zargin aikata laifi a rika hukunta shi domin ta haka ne kawai za a samu nasarar yaki da masu aikata miyagun laifuffuka a kasar nan.
Shehu Aljan ya ce ya kuma kama wadansu da ake zargin manyan ’yan fashi da makami ne a garin Bali da Takum, kuma sun amsa cewa su ne ke da alhakin mafi yawan fashi da makamin da ake aikatawa a manyan hanyoyin da suka ratsa kananan hukumomin Gassol da Bali da Donga da Takum.
Shehu Aljan wanda ya taba gudanar da aikin kama barayi a jihohin Kaduna da Filato da Neja da Nasarawa da kuma Bababn Birnin Tarayya, Abuja, ya nuna takaici ka yadda miyagu suka mai da Jihar Taraba wani dandali na gudanar da mummunan ayyukansu.
Ya ce duk da yawan shingayen duba ababen hawa da sojoji da ’yan sanda ke gudanar da bincike, amma sai ga shi miyagun na cin karensu babu babbaka a jihar. Ya ce irin manyan makaman da ya kama a hannunsu abin tsoratarwa ne, inda ya ce wasu makaman na iya tayar da gari. Ya ce, ya zama tilas hukumomi su tashi tsaye domin karfafa bincike a daukacin hanyoyin jihar.
Shehu Aljan ya ce ya kama barayin shanu masu yawa a kananan hukumomin Gassol da Bali da Donga kuma shi da masu taimaka masa sun samu nasarar gano shanun da aka sace sama da 400, kuma tuni aka mai da wa masu shanu kayansu. Ya bayyana cewa ya yi nasarar kama alburusai masu yawa a garin Baruwa da ke karamar Gashaka a hannun wani dan kabilar Ibo.
Ya ce gwamnatin Jihar Taraba ce ta gayyace shi domin taimaka wa jami’an tsaro wajen yaki da masu aikata miyagun laifuffuka da suka addabi al’ummar jihar. Ya ce da isarsa jihar ya fihimci cewa masu aikata laifuffukan sun maida jihar wata daba inda suke cin karensu babu babbaka.
Shehu Aljan ya ce a halin yanzu da yawa daga cikin masu aikata laifuffuka a sassan jihar sun arce zuwa wasu sassa na kasar nan.
Wasu mazauna yankunan da Shehu Aljan ke gudanar da aikin kama barayi sun nuna gamsuwa da nasarorin da ya samu. daya cikinsu mai suna Alhaji Yakubu Sabon Gida ya ce kafin zuwan Shehu Aljan satar shanu da fashi da makami da satar mutane sun addabe su, amma yanzu wadannan matsaloli sun ragu sosai.
Ya ce a watanin baya duk mai dukiya ba ya iya kwana a gidansa, saboda tsoron kada a sace shi, haka su ma masu shanu ba sa iya barci gudun kada barayin shanu su far musu. Ya kara da cewa akwai wasu hanyoyi da ’yan fashi suka hana jama’a bi saboda yawan fashi da hallaka jama’a da ke faruwa a kowace rana.
Alhaji Yakubu, ya ce hanyoyin da jama’a suka kaurace musu sun hada da hanyar Nanguru da Sansani da Gwiwar Kogi da sauransu.
Shi ma Malam Ibrahim Lawal ya nuna gamsuwa kan ci gaban da aka samu ta fuskar tsaro a sanadiyyar aikin Shehu Aljan na yaki da barayi a yankunansu. Malam Ibrahim Lawal ya ce a watannin baya jama’a da dama masamman masu hannu da shuni sun kaurace wa garuruwansu saboda matsalar sace-sacen mutane da fashi da makami. Ya ce akwai bukatar gwamnati ta tura Shehu Aljan yankunan kananan hukumomin Wukari da Ibbi don yaki da masu fashi da makami da satar mutane da shanu.
Da yake magana dangane da aikin Shehu Aljan, Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Taraba DSP Joseph Kwaji ya ce rundunar ta san da kasancewar Aljan a jihar.
Ya ce mai kama barayin yana aiki ne kafada-da-kafada da ’yan sanda kuma a wasu lokuta ma ana hada shi da ’yan sanda ne domin su taimaka masa wajen gudanar da ayyukansa.
DSP Kwaji ya tabbatar da cewa Shehu Aljan ya kama masu aikata laifuffuka masu yawa tare da makamai da alburusai kuma ya mika su ga rundunar.
Ya ce rundunar ta gamsu da irin ayyukan da Shehu Aljan yake gudanarwa ta fuskar yaki da masu aikata laifuffuka a jihar.
Sai dai DSP Joseph Kwaji ya ce ba ya da masaniya kan Shehu Aljan ya mika wa rundunar wani wanda ya kama da zargin satar mutane har da Naira dubu 800 da ya nemi ya ba mai kama barayin a matsayin cin hanci.