Aljeriya ta kaddamar da Masallaci mafi girma a Afrika
Masallacin shi ne na uku mafi girma a duniya.
Shugaban Kasar Aljeriya, Abdelmadjid Tebboune, ya kaddamar da Babban Masallacin kasar, wanda shi ne na uku mafi girma a duniya kuma na daya a Nahiyar Afirka.
Katafaren Masallacin zai iya daukar masallata 120,000 a lokaci guda.
- Gaza: Sojan Amurka ya kona kansa a ofishin jakadancin Isra’ila
- An kashe mai juna biyu a turereniyar sayen shinkafar kwastam
An fara gudanar da sallah a Masallacin ne a watan Oktoban 2020, a lokacin da COVID-19 ta hana shugaban kasar halartar kaddamar da masallacin.
Masallacin mai suna ‘Great Mosque of Algiers’, na da hasumiya mafi tsayi a duniya, inda ta kai tsawon mita 265 daidai da kafa 869.
An kwashe sama da shekara bakwai ana aikin gina Masallacin, kuma an yi amfani da kadada 27.75 wajen tsara ginin masallacin.
A cikin Masallacin, akwai filin saukar jirgi mai saukar ungulu da kuma katafaren dakin karatu da zai iya daukar litattafai sama da miliyan daya.
A yanzu Aljeriya ce kasa ta farko da ke dauke da katafaren Masallaci a wajen biranen Makka da Madina.
Kazalika, an sanar da al’ummar Musulmi cewa za su iya amfani da masallacin wajen gudanar da ibada a lokacin azumin watan Ramadan.