Aljihun gwamnatin Taraba ya bushe – Mukaddashin Gwamna
Aljihun Gwamnatin Jihar Taraba ya bushe, ba ko kudin da za a biya albashi balle kudaden da za a gudanar da muhimman ayyuka.Wannan kalaman suna kunshe ne a cikin wata takarda da mukaddashin Gwamnan Jihar, Alhaji Sani Abubakar danladi ya tura wa Majalisar Jihar a wannan makon, don neman a amince masa ya karbo bashi […]
Aljihun Gwamnatin Jihar Taraba ya bushe, ba ko kudin da za a biya albashi balle kudaden da za a gudanar da muhimman ayyuka.
Wannan kalaman suna kunshe ne a cikin wata takarda da mukaddashin Gwamnan Jihar, Alhaji Sani Abubakar danladi ya tura wa Majalisar Jihar a wannan makon, don neman a amince masa ya karbo bashi a banki.
Takardar, wacce ke dauke da sa hannun Mukaddashin Gwamnan ta nuna irin halin rashin kudi da jihar ta sami kanta a ciki, inda ya ce ya zama tilas jihar ta ciyo bashi in ana son ta ta iya biyan bashin wannan wata na Disamba.
Ya kara da cewa dama akwai wani bashi da Gwamnati ta ciyo na Naira biliyan bakwai da miliyan dari biyar daga Bankin Zenith.
Bashin ne ya sa jihar ta tsiyace, har ya sa ba ta da kudin da za ta iya biyan albashi balle ma gudanar da sauran ayyuka na yau da kullum.
Ya ce saboda haka yanzu an daidaita lokacin biyan wannan bashi zuwa watanni ashirin da hudu, don gwamnati ta samu saukin biyan bashin cikin natsuwa. Amma duk da haka akwai bukatar karbar wani bashin domin, kada ayyukan gwamnati su tsaya cik.