An bayyana zakarun Gasar Labarun Aminiya
A lokacin da aka yi ta dakon sakamakon Gasar Rubutun Gajeren Labari da kamfanin Aminiya-Trust Abuja ta shirya da hadin gwiwar kamfanonin Gandun Kalmomi da Open Arts Kaduna, daga karshe dai alkalumman da alkalan gasar suka mika wa masu gudanar da gasar ta farko sun daidaita da zabar labarai uku daga cikin 20 da aka […]
A lokacin da aka yi ta dakon sakamakon Gasar Rubutun Gajeren Labari da kamfanin Aminiya-Trust Abuja ta shirya da hadin gwiwar kamfanonin Gandun Kalmomi da Open Arts Kaduna, daga karshe dai alkalumman da alkalan gasar suka mika wa masu gudanar da gasar ta farko sun daidaita da zabar labarai uku daga cikin 20 da aka tantance daga cikin labarai sama da 350 da suka shiga gasar a bana.
Gasar, wacce aka bukaci marubuta su baje kolinsu a kan matsalolin dimokuradiyya da dambarwa siyasa, ta samu gagarumar nasara ya zuwa yanzu.
Alkalan gasar, wadanda suka kasance malaman jami’a, Dokta Aliyah Adamu Ahmad da Dokta Umar Aliyu Bunza da kuma fitaccen marubuci, Nazir Adam Salih, sun yi aiki tukuru, inda suka bayyana cewa labaran da suka zaba zuwa matakin karshe, kowanne daga cikinsu yana iya lashe gasar saboda ingancinsu.
Labarai uku da suka zama zakaru sun hada da: Tufka da Warwara, Dimokuradiyar Talaka da kuma labarin Ranar Kin Dillanci.
Haka kuma sun fitar da labaran da suka cancanci yabo guda 12 kwarara.
Wadannan kuwa sun hada da Komai Nisan Dare Hassada Ga Mai Rabo, Baki Guba Ne, Tsaka Mai Wuya da Kawalwalniya.
Sauran sun hada da Kazar Kwanci, Ci Ga Rashi, Igiyar Linkaya, Kotun Allah Ya Isa, Zabin Allah, Tsalle Daya da kuma Yanayi.
Kamar yadda Shugaban Kwamitin Gasar, Farfesa Ibrahim Malumfashi ya bayyana, ya ce: “Wadannan labarai guda 15 da suka yi zarra, za a sake tace su domin sake tsarawa da buga su a matsayin littafi, wanda za a kaddamar a wajen wani kwarya-kwaryan biki da Hukumar Gudanarwar Jaridun AMINIYA da TRUST za su gudanar a garin Kaduna, a ranar 2 ga watan Janairu na shekarar 2021 mai zuwa.”
Ya kara da cewa, a wajen wannan biki ne za a bayyana wadanda suka lashe gasar ta bana, wato na 1 zuwa na 3, a kuma ba su awalajar kudi da kambum yabo da satifiket.
“Su kuma wadanda suka samu yabo na musamman, kowanne za a ba shi satifiket na shiga wannan gasa, in Allah Ya kai mu”, inji shi.
Ita dai wannan gasa ta rubutun gajeren labari ta AMINIYA-TRUST, hadin gwiwa ne tsakanin kamfanonin GANDUN KALMOMI da OPEN ARTS da ke Kaduna da Hukumar Gudanarwar jaridun AMINIYA da TRUST da ke Abuja, domin sa wa matasa, maza da mata shaukin rubuta gajerun labarai da suke tattauna matsalolin al’umma daban-daban da nema musu mafita, domin ba da gudunmuwa wajen rayawa da bunkasa adabin Hausa, wadda za a dinga gabatarwa kowace shekara da yardar Allah.