Alkali Ibrahim Maikaita Bako ya rasu
Allah Ya yi wa mai shari’ar tarayya Alkali Ibrahim Maikaita Baƙo rasuwa a safiyar yau Lahadi a wani asibiti a Abuja bayan hadarin mota da ya yi a kan hanyar Funtua zuwa Kankara cikin jihar Katsina. Marigayin ya yi hadarin ne a ranar 4 ga Janairu makon da ya wuce. Inda ya samu mummunan rauni. […]
Ibrahim Maikaita Bako
Allah Ya yi wa mai shari’ar tarayya Alkali Ibrahim Maikaita Baƙo rasuwa a safiyar yau Lahadi a wani asibiti a Abuja bayan hadarin mota da ya yi a kan hanyar Funtua zuwa Kankara cikin jihar Katsina.
Marigayin ya yi hadarin ne a ranar 4 ga Janairu makon da ya wuce. Inda ya samu mummunan rauni.
Babban Alkalin jihar Katsina Musa Danladi, ne ya sanar da rasuwar Alkali Ibrahim Maikaita Baƙo a yau Lahadi.