Alkali ya banke mutane da mota ya ki tsayawa

Litinin din makon jiya aka zargi wani alkali da  yin sanadiyar mutuwar dan shekara 60, tare da raunata mutum biyu, bayan da ya kade su da mota. Aminiya ta gano Alkali Haruna Aliyu mazaunin kwarbai ne a Unguwan Doya da ke Zariya.A rohoton da Aminiya ta samu ya nuna cewa Alkali Haruna ya ture Malam […]

Alkali ya banke mutane da mota ya ki tsayawa

Litinin din makon jiya aka zargi wani alkali da  yin sanadiyar mutuwar dan shekara 60, tare da raunata mutum biyu, bayan da ya kade su da mota. Aminiya ta gano Alkali Haruna Aliyu mazaunin kwarbai ne a Unguwan Doya da ke Zariya.
A rohoton da Aminiya ta samu ya nuna cewa Alkali Haruna ya ture Malam Ibrahim Yahaya ne a daidai Kwalejin Alhuda-Huda a inda aka kai shi asibiti daga baya rai ya yi halinsa.
Marigayin  Malam Ibrahim mai sana’ar sayar da buhu, mazaunin Unguwar Nufawa, ya rasu ya bar mata daya da ’ya’ya 19, kamar yadda rohoton ke cewa Alkali Haruna Aliyu, Alkalin Kotun Shari’a ne da ke Gubuci a karamar Hukumar Makarfi ta  Jihar Kaduna, ko da ya buge Ibrahim mai sayar da buhu bai tsaya ba, ya ci gaba da tafiya, har ya sake buge samari biyu a Unguwar Rimin Tsiwa, a dalilin haka daya mai suna Yusuf Bello ya samu karaya a kafa shi kuma Sani Bashir ya samu miyagun raunuka.
Duk da faruwan wannan al’amari wannan alkali bai tsaya ba, har sai da matasan Unguwar Rimin Tsiwa suka yi masa tarar aradu gami da duka, sai da dattawan anguwa tare da hadin gwiwar ‘yan sanda suka shiga cikin al’amarin.
Alkali Haruna an tsare shi a ofishin ’yan sanda da ke cikin birnin Zariya tare da motarsa mai kirar Rober, inda daga bisani aka sake shi ya tafi gidansa.
’Yan uwan marigayin sun ce kaddara dai ta faru, kuma Alkali ya zo ya yi masu ta’aziyar, tare da wasu hakimai na Kurmin kogi da na Samunaka, a inda ya ce musu da su yi hakuri, a cewar Malam Aliyu Yahaya  dan uwan mamacin
Ya ce Alkali Haruna shi ya yi sandiyyar mutuwar dan uwansa, saboda haka tunda Alkali ne ai ba abin da za su iya yi tunda ba su da karfi, amma lallai suna neman taimako na hakkin marayu.
Su ma samari biyun da ke jinya, wato Yusuf Bello da Sani Bashir, sun bayyana cewa, tunda abin ya faru ba su ga wannan Alkali ba, domin bai zo gaishe su ba, kuma bai aiko ba, sai dai kawai dan sanda da ke zuwa duba su a gida, kuma tunda wannan abu ya faru ba abin da ya aiko masu da shi na sayan magani.
Aminiya ta tuntubi wasu daga cikin ‘yan uwan wadannan mutane, inda dattijo Alhaji Musa Na’iya mai shekaru 93 da Malam Yusuf Bello suka nuna juyayi tare da mamaki cewa Alkalin Kotun Shari’a ya aikata wannan mumunar barna lallai abin tahuma ne.
Duk kokarin da wakilinmu ya yi na ganawa da alkalin, abin ya ci tura, domin ya je sau da yawa bai same shi ba, amma makwabtansa  sun ce mai shari’a baya zaman lafiya da su, amma sun sami labarin yana cewa shi ko kaza bai ture ba, bakin ciki ne ake masa saboda ya fara samun kudi.
Ganin haka wakilin namu ya  tafi ofishin ‘yan sanda na garin Zariya, domin inji ta bakin su, ba su amince da su ce masa komai ba, amma a wata majiya daga ofishin wanda ba su amince da ambatan sunan su ba, na sami tabbacin suna da wannan labari, rohoto ya zo musu cewa ga samarin Unguwar Rimin Tsiwa can suna dukan wani Alkali, tare da fasa masa mota, bisa dalilin buge musu mutane ya kuma gudu.
Don haka ya sami taimakon ‘yan sanda da na mai anguwar wannan yanki, sai dai mai shari’a Haruna Aliyu bai amsa ya sha giya ba, cewa ya yi turare ne yake wannan kamshi ko tashi a cikin motarsa.
Aminiya ta tumtubi kakakin hukumar ’yan sanda DSP Aminu Lawal ta wayarsa, wadda ya tabbatar mana da faruwar lamarin, cewa Alkalin ya buge mutane uku daya ya rasu, biyu sun yi rauni, amma batun ya sha giya wannan likita ne kawai zai iya tabbatarwa. Ana kuma ci gaba da bincike.
Aminiya ta ziyarci Babban ofishin mai Shari’a Kadi a Kaduna
Aminiya ta ziyarci ofishin Babban Kadi na Kaduna domin ta bincika ko suna da labarin abin da daya daga cikin alkalansu ya aikata, amma sai akawunsa, wato mai rajistar kararraki, ya ki cewa komai, domin a cewarsa wai ba shi da hurumin yin magana da ’yan jaridu.
Da wakilinmu ya tambaye shi ko suna da jami’an hulda da jama’a a kotun sai ya ce eh, amma ba ta nan, saboda tana da ayyuka da yawa kuma wai ba ta zama waje daya.
Malam Bello mahaifin wanda ya karyeMalam Musa Na’iya mahaifin marigayisai dai wata majiya a  ofishin Babban Kadin ta tabbatar wa Aminiya cewa babu yadda za a ce wani abu dangane da hadarin saboda ba su samu wata takardar koke daga iyalan wadanda aka kade musu ’yan uwa ba, sannan kuma ’yan sanda ba su aika da takarda ofishin babban Mai Shari’ar ba.
“Gaskiya ko da muna da labarin abinda ya faru muddin iyalan wadanda abin ya shafa ko kuma yan sanda ba su aiko da takarda akan zancen ba. Babu yadda za a yi yallabai  ya ce wani abu,” inji shi.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan