Alkali ya yanke wa barawo hukuncin sharar kotu
Kotun majistire da ke zama a Wuse Zone 6, Abuja, ta zartar wa wani direba mai shekara 35, Ahmed Danladi, hukuncin sharar farfajiyarta ta kwanaki biyu bisa laifin sata. Mai shari’a, Omolola Akindele, ya umurci mai laifin ya rika zuwa yana share farfajiyar kotun na tsawon kwanaki biyu ba tare da zabin tara ba. Gabanin […]
Kotun majistire da ke zama a Wuse Zone 6, Abuja, ta zartar wa wani direba mai shekara 35, Ahmed Danladi, hukuncin sharar farfajiyarta ta kwanaki biyu bisa laifin sata.
Mai shari’a, Omolola Akindele, ya umurci mai laifin ya rika zuwa yana share farfajiyar kotun na tsawon kwanaki biyu ba tare da zabin tara ba.
Gabanin hukuncin, ‘yan sanda sun kai Danladi kotu bisa zargin aikata laifin satar.
Mai gabatar da kara, ASP Peter Ejike, ya fada wa kotun cewa, a ranar 1 ga watan Satumba, Samuel Joseph, ya kai kara ofishin ‘yan sanda da ke Wuse zone 3 cewar Danladi, wanda ya dauka a matsayin direba, ya satar masa injin shara da ba a san adadin kudinsa ba.
Ejike ya ce Danladi ya yi kokarin mika injin sharar ga mai sayen kayan nauyi ta katanga don a gudu da shi.
Ya kuma ce, a yayin gudanar da bincike Danladi ya amsa laifinsa wanda ya saba wa sashe na 289 na Kundin Tsarin Mulki Kasa, kamar dai yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito