Alkali ya karbi tara kafin yanke hukunci
Reshe ya juya da mujiya a wata Kotun Yanki da ke garin Gauraka a karamar Hukumar Tafa a Jihar Neja, lokacin da jami’an Hukumar Yaki da Cin hanci da Rashawa (ICPC) suka yi awon gaba da alkalin kotun Mai shari’a Abba Mika’il Pandogari zuwa hedkwatarsu da ke Abuja.Wata majiya mai tushe ta da ke kusa […]

Reshe ya juya da mujiya a wata Kotun Yanki da ke garin Gauraka a karamar Hukumar Tafa a Jihar Neja, lokacin da jami’an Hukumar Yaki da Cin hanci da Rashawa (ICPC) suka yi awon gaba da alkalin kotun Mai shari’a Abba Mika’il Pandogari zuwa hedkwatarsu da ke Abuja.
Wata majiya mai tushe ta da ke kusa da Hukumar ICPC da ta nemi a sakaya sunanta ta shaida wa Aminiya cewa an cafke alkalin ne bisa zargin ya nemi Naira dubu 20 daga wani da aka gurfanar a gabansa a matsayin tara kan karar da ba a riga an yanke hukunci a kai ba, tare da bukatar ya ba shi Naira dubu 50 daga gare shi domin kashe karar gaba daya.
A harabar kotun da ke Gauraka wata majiya ta shaida wa wakilinmu cewa ana zargin wani da kotun ta yanke wa hukuncin daurin wata 3, ko tarar Naira dubu 20, kan laifin cin kudi wata mai neman dakin haya ne ya jagorancin jami’an zuwa kotun yayin da yake kokarin biyan kudin tarar da kotun ta yanke masa suka kama alkalin.
Majiyar ta ce, wanda aka yanke wa hukuncin mai suna Abubakar Sadik da karamin ofishin ’yan sanda na Dakwa da ke Jihar Neja ya gurfanar a gaban kotun bayan matar ta kai musu kuka, ya nemi alfarmar kwana uku don hada kudin tarar, bayan alkalin kotun Mai shari’a Abba Mika’il Pandogari ya yanke masa hukunci a ranar Juma’ar makon jiya.
Majiyar ta ce ya ba da Naira dubu shida tare da mika wayarsa ta hannu kafin kawo cikon kudin. Amma da ya tashi komawa kotun a ranar Talatar makon jiya, sai ya tafi da jami’an Hukumar ICPC wadanda suka tsaya a nesa, ya karasa kotun da daya daga cikinsu da ya gabatar da kansa a matsayin dan uwansa.
Ta ce a lokacin magatakardan kotun baya nan, sai ya ba da kudin ga dan sandan da ke shigar da kara, inda dan sandan da Sadik da jami’in ICPC suka shiga ofishin alkali suka danka masa kudin, sai ragowar jami’an ICPC suka shiga ofishin, suka kama alkalin da dan sandan, suka sanya musu ankwa suka tafi da su hedkwatarsu da ke Abuja.
Wata majiyaR ta ce a ranar Juma’a da ta gabata, Daraktar Shigar da kararraki na Jihar Neja (DPP) da Kwamishinan Shari’a na Jihar Barista Abdullahi Bawa Wuse, sun je ofishin Hukumar ICPC don neman belin alkalin.
Kakakin Hukumar ICPC Mista Folu Olamiti ya tabbatar wa Aminiya da kai samamen, inda ya ce hukumar ta ba da belin alkalin da dan sandan, kuma tana ci gaba da bincike a kan al’amarin. Ya ki yin karin bayani kan dalilin kamen inda ya ce sai an mika bayanin ga shugabansu ya sa hannun a kan rahoton, kafin su tura bayanansu ga kafofin watsa labarai.