Alkali ya yi watsi da bukatar Saraki
Kotun da’ar Ma’aikata a karkashin Mai shari’a danladi Umar ta yi watsi da bukatar da Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki ya gabatar ta alkalin kotun ya haramta wa kansa sauraron karar da ake yi masa kan shara karya game da kadarorin day a mallaka.A jiya Alhamis daya daga cikin lauyoyinsa mai suna Rapheal Oluyede […]
Kotun da’ar Ma’aikata a karkashin Mai shari’a danladi Umar ta yi watsi da bukatar da Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki ya gabatar ta alkalin kotun ya haramta wa kansa sauraron karar da ake yi masa kan shara karya game da kadarorin day a mallaka.
A jiya Alhamis daya daga cikin lauyoyinsa mai suna Rapheal Oluyede ya mike jim kadan bayan ya bayyana a gaban kotun inda ya yi kokarin gabatar da bukatar da ya ce an mika wa kotun a shekaranjiya Laraba.
Sai dai lauya mai gabatar da kara Rotimi Jacobs ya nuna adawa da bukatar inda ya taka wa Oluyede birki. Kuma nan take alkalin kotun ya yi watsi da bukatar.
Mai shari’a Umar ya ce bukatar ba ta da muhimmanci kuma ba ta cancanci a saurare tab a, don haka ya yi watsi da ita.
Sai dai kuma nan take sai cikin kotun ya hargitse a lokacin da lauya Oluyede da ke tsayawa a madadin babban lauyan Saraki Mista Kanu Agabi ya nace cewa dole a saurari bukatar. Kuma bayna ya fadi dalilansa sai Oluyede ya shiga musayaa zafafafan kalamai da Mai shari’a danladi Umar lamarin das aura kiris ’yan sanda su yi waje das hi bisa umarnin alkalin kafin lauyan EFCC Mista Jacobs ya roki alkalin ya yi hakuri.
Sanata Bukola Saraki dai ya bukaci Mai shari’a danladi Umar ya dakatar da kansa ne daga sauraren shari’ar da yake yi masa, saboda abin da ya kira akwai yiwuwar nuna son kai a cikin takardar da Oluyede ya shigar wa kotun a shekaranjiya Laraba.
Oluyede ce ya bukaci Mai shari’a danladi Umar ya dakatar da kansa daga zaman sauraren shari’ar da yanke hukunci a kan karar da aka kai Sanata Bukola, saboda ci gaba da kasancewarsa wajen gudanar da shari’ar ya saba wa sashi na 36 (1) na tsarin mulki.
A ranar Talata Saraki ya gaza samun damar dage shari’ar zuwa wani mako, bayan da ya bukaci kotun ta sauya ra’ayi kan shawarar da ta yanke na ci gaba da sauraren shari’ar a kullum, amma alkalin kotun Mai shari’a danladi Umar ya kafa hujja da sashi na 396 na dokokin gudanar da shari’a wajen yin watsi da bukatar.
Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta ci gaba da jero laifuffukan da ake zargin Sanata Saraki da aikatawa da suka hada da mallakar kadarori a ciki da wajen kasar nan ba tare da ya sanar da hukumar da’ar ma’aikata ba.
Babban mai ba da shaida na Hukumar EFCC, Michael Wetkas, ya yi zargin cewa Saraki ya sayi gida mai Lamba 15A Macdonald a Ikoyi, Jihar Legas ta amfani da wani kamfani mai suna Tiny Tee Ltd, kuma bai bayyana wannan gida a matsayin dukiyarsa ba. Mista Wetkas ya ce Tiny Tee ya biya kashi 75 cikin 100 na gidan wanda ya kai Naira miliyan 123 da dubu 750 daga asusun Skybiew Properties a bankin Intercontinental Bank (Access Bank a yanzu) da bankin GTB. Sai kuma gidan da ke Lamba 17, titin Macdonald Street a Ikoyi Legas kan Naira miliyan 256 da dubu 300 ta amfani da asusun kamfanin Carlisle Property and Inbestment Ltd a madadin Saraki.
Sai dai a zaman kotun na shekaranjiya Laraba Wetkast ya kasa gabatar da takardun da za su tabbatar da Saraki ya tura Dala 73,233.28 zuwa asusun banki na kasar waje a lokacin da yake Gwamnan Jihar Kwara kamar yadda yake kunshe a cikin zarge-zarge 11 da ke gaban kotun.
A wani labarin kuma Hukumar EFCC ta wanke Shugaban Kotun da’ar Ma’aikata Mai shari’a danladi Umar kan zargin karbar cin hanci daga wani da aka gurfanar a gaban kotun.
Aminiya ta gano Hukumar EFCC ba ta canja matsayinta kan binciken rahoton da aka mika wa ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya a shekarar 2015 da ya wanke Mai shari’a Umar ba.
Har wa yau Majalisar Dattawa ta dakatar yunkurinta na sauya dokar hukuma da kotun da’ar ma’aikatan da taso yi da kuma bukatar shugaban Kotun da’ar Ma’aikatan ya gurfana a gabanta a jiya. Har wa yau majalisar ta jingine yunkurinta na dakatar da Sanata Kabiru Marafa daga majalisarkan kalamansa ga shugaban majalisar.