Alkawura 5 da Abba ya yi wa Daurawa da ’yan Hisbah
‘Operation Kau Da Badala’ zai ci gaba gadan-gadan, babu kama hannun yaro
Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta sanar cewa za ta yi wa jami’anta karin albashi domin su ji dadin gudanar da ayyukansu.
Shugubanta, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya kara da aikin hukumar na ‘Operation Kau Da Badala’ zai ci gaba gadan-gadan, babu kama hannun yaro.
Sheikh Daurawa wanda ya dawo aiki ranar Talata, ya sanar cewa hakan na daga cikin alkaruwa biyar da gwamnan jihar Abba Kabir, ya yi wa hukumar kamar haka:
1- Samar da motocin aiki ga rundunar Operation Kau Da Badala da kuma bunkasa shirin hukumar na ‘taya ni mu gyara’, wanda ya mayar da hankali kan kananan ’yan mata.
2- “Za a kara wa ’yan Hisbah Albashi. Shekara 20 da suka wuce albashin N10,ooo ne, wadanda ke hedikwata kuma N15,000.”
3- Samar wa Hisbah kayan aiki.
4- Daina korar jami’an Hisbah saboda siyasa.
5- Kafa makarantar koyar da a ikin Hisbah a aikace.
Malamin ya ba wa masu aikata badala a Jihar Kano wa’adin mako bi su tuba, ko su gamu da fushin rundunar ‘Operation Kau Da Badala’.
Shugaban hisban ya ce, hukumar ta tanadi fom mai suna ‘na tuba na daina’, wanda duk wanda ke son daina badala zai je ya cike domin gwamnati ta sama masa abin da zai inganta rayuwarsa a bangaren sana’a ko neman ilimi.
A cewarsa, duk wanda ya kawo kansa Hisha ya cika fom, za “a kai wa mai girma gwamna ya taimaka masa da sana’a da jari, wanda zai koma makaranta a taimaka masa komawa makaranta, mun bude wannan kofa daga nan har zuwa mako biyu.”
Sai dai ya yi karin haske da cewa kofar tuba da hukumar ta bude ba ya nufin za a bar kowa ya yi abin da ya ga dama.
An bude damar ce domin wanda ke aikata laifi ya gabatar da kansa hukumar ta san ya daina ta kuma dauki bayanansa domin ganin gwamnati ta yi abin da ya dace.