Alkawuran manyan ’yan takarar shugaban kasa ga ’yan Najeriya
Aminiya ta tattaro manyan alkawura 12 da ke cikin takardun manufofin manyan ’yan takarar shugaban kasan suka yi wa ’yan Najeriya.
Yakin neman zaben shugaban kasa na 2023 ya kara kankama, kuma manyan ’yan takarar zaben sun gabatar da manufofinsu ga ’yan Najeriya.
Kawo yanzu dai suna ci gaba da yin tarukan gabatar da manufofin ’yan takara, da kuma wasu tarukan yakin neman zabe da alkawura iri-iri da suke ga al’ummar kasa.
Aminiya ta tattaro manyan alkawura 12 da ke cikin takardun manufofin manyan ’yan takarar shugaban kasan suka yi wa ’yan Najeriya.
Manyan ’yan takarar hudu su ne, Atiku Abubakar na Jam’iyyar PDP, Bola Tinubu na APC, Peter Obi na Jam’iyyar LP, da kuma Rabiu Kwankwaso na NNPP.
Kwankwaso
Sanata Rabi’u Kwankwanso wanda tsohon Gwamnan Jihar Kano ne kuma tsohon Ministan Tsaro, ya yi alkawarin:
1- Tsaro
A taron kaddamar da kundin manufofinsa, Kwankwaso ya yi alkawarin kara yawan dakarun sojin Najeriya zuwa miliyan daya ta hanyar daukar sabbin sojoji 750,000.
A cewarsa, ta haka ne za a samu wadatattun sojoji da za a iya girkewa a ko’ina domin dakile matsalolin tsaro da Najeriya ke fama da su a halin yanzu.
2- Ilimi
Tsohon gwamnan Kanon ya yi alkawarin soke kudin jarabawar kammala makarantun sakandare na WAEC da NECO da sauransu.
Hakazalika zai soke kudin rajistar shiga manyan makarantu da ma na jarabawar shigar su irin su JAMB da sauransu ga ’yan Najeriya.
3- ’Yancin kananan hukumomi
A taron mahawara da kafofin yada labarai suka gudanar, Kwankwaso ya ce duba da yawan talauci a Najeriya, akwai bukatar sauya tsarin mulki ta yadda kananan hukumomi za su rika samun kudadensu kai tsaye daga Gwamnatin Tarayya.
4- Bangaren jiragen ruwa
Ya yi wa masu ruwa da tsaki a harkar jiragen ruwa alkawarin gyara a bangaren, wanda ya ce an yi watsi da shi.
A zamansa da su a Legas, ya ce, bangaren ne cibiyar Jam’iyyar NNPP, shi ya sa shi da jam’iyyar suka je tattauna jin “abubuwan da kuke bukata daga bakinku, idan mun ci zaben 2023.”
Bola Tinubu
Tinubu wanda shi kuma tsohon gwamnan Jihar Legas ne kuma tsohon Sanata, ya yi alkawura kamar haka:
5- Samar da ayyuka
A gangamin yakin neman zabensa a Yenagoa, Jihar Bayelsa, dan takarar ya yi alkawarin samar wa matasan dubban ayyuka domin su samu cika burinsu, idan ya ci zabe.
A cewarsa: “Daga kafa jihar nan zuwa yanzu PDP ke karbar kudaden amma ta kasa gina hanyoyi, ballantana samar da ayyuka. Zan samar da dubban ayyuka a bangaren kwarewa domin sada ku (matasa) da saura sassan duniya.
6- Bunkasa masana’antu
Tinubu wanda mahaifiyarsa ’yar kasuwa ce ya yi alkawarin gina cibiyoyin masana’antu tare da zamanantar da wadanda ake da su a fadin Najeriya, idan ya zama shugaban kasa.
Dan kasuwar, wanda mahaifiyarsa shugaban ’yan kasuwa ce, ya ce, “Na samu nasarori a bangaren shugabanci, kuma ina so ne in samar da abubuwan da rayuwarmu za ta yi kyau a nan gaba.
7- Ba wa ’yan kasuwa kariya
A lokacin taron jin ra’ayi da ya gudanar a Abakakaliki, Jihar Ebonyi, Tinubu ya yi alkawarin kariya harkokin kasuwancin ’yan kabilar Ibo idan aka zabe shi.
A cewarsa, “Na gamsu cewa kasuwancin a jinin ’yan kabilar Ibo ya kuma kuma na karfafe su a bangaren da ma zuba jari a Jihar Legas, kuma zan kara yin hakan tare da kare manufarsu da mutunta su, idan na ci zabe.”
Petert Obi
Alkawuran Peter Obi, wanda tsohon Gwamnan Jihar Anambra sun hada da:
8-Gina kasa
A gangamin yakin neman zabensa a Benin, Jihar Edo, Peter Obi, alkwarin sake gina kasa ya yi, “Kuma zan hana mutane sace dukiyar kasa,” idan ya ci zabe.
9- Yajin aikin ASUU
Ya kuma yi alkawarin kawo karshen yajin aikin malaman jami’a, “Wanda daga 1999 zuwa yanzu suka yi guda 50 wanda kuma babban bala’i ne ga samar da ilimi mai inganci.”
10- Kawar da talauci
Ya ce zai yi amfani da albarkatun da Allah Ya yi wa Najeriya wajen yakar talauci domin, “Rashin aikan yi ne silar matsalolin tsaron kasar nan. Zan mayar da kasar yadda mutane za su zauna cikin farin ciki da kwanciyar hankali.”
Atiku Abubakar
Daga cikin alkawuran Atiku da suka hada da hanzarta samar da tsaro, akwai kuma:
11- Bunkasa tattalin arziki
Ya bayyana a Benin cewa manufofinsa “Biyar su ne hada kan Najeriya, samar da tsaro, ilimi kyauta a matakin firamare da ganin malaman jami’a sun daina yajin aiki, sai kuma farfado da tattalin aarziki.”
12- ’Yancin ’yan jarida
A zamansa da Kungiyar Editoci ya yi alkawarin kare ’yancin ’yan jarida, “saboda sadukarwarsu da rawar da suka taka wajen tabbatar da dorewar dimokuradiyya a Najeriya.”
13- Cire tallafin mai
A cewarsa, zai waiwayi rahoton Kwamitin Steve Orosanye kan hade wasu hukumomin gwamnati da cire tallafin mai da ke durkusar da tattalin arzikin Najeriya.
“Ni ne shugaban kwamitin cire talllafin mai kuma mun cire shi a matakin farko da na biyu; tun ta cuta ce kawai, idan na ci zabe zan cire shi gaba daya, a rika amfani da kudaden wajen farfado da tattalin arziki.”
Daga Sagir Kano Saleh, Abudlyassar Abdulhamid da Mu’awiya Shu’aibu