Allah mai hana kunya ranar gaskiya (1)
Tsawon shekaru fiye da talatin (30) nake ta faman gwagwarmaya, har da fito-na-fito da azzaluman shugabanni da barayin gwamnati da fajirai da matsafa, har na samu hadin kan muhimman mutane muka hadu muka kafa kungiyar Rundunar Adalci ta Najeriya – Mobement for Justice in Nigeria (MOJIN) a 1993. Mun yii ta fafatawa da barayin shugabanni […]
Tsawon shekaru fiye da talatin (30) nake ta faman gwagwarmaya, har da fito-na-fito da azzaluman shugabanni da barayin gwamnati da fajirai da matsafa, har na samu hadin kan muhimman mutane muka hadu muka kafa kungiyar Rundunar Adalci ta Najeriya – Mobement for Justice in Nigeria (MOJIN) a 1993. Mun yii ta fafatawa da barayin shugabanni har aka rika tsare ni har da fesa mini tiya-gas a ido da dukan bulala a hedkwatar jami’an asiri na SSS ta kasa. Sai da Sani Abacha ya mutu aka sake ni. Kwana biyu da saki na aka gayyace ni taro da manyan Jami’an Gwamnatin Tarayya don mu tsara mata yadda za a kori faruwar irin abin da aka yi mana nan gaba, mu kuma fitar da jadawalin irin siyasayar da ta dace a yi, wacce za ta hana sojoji yin juyin mulki a nan gaba. Har aka ba ni babban daki da rumfa a Hotel din Sheraton-Abuja tsawon lokaci. karshe aka kafa jam’iyyu uku (3): AD da APP da PDP. Tun a lokacin na fahimci PDP ta tsofaffin shugabannin soja ce, kamar yadda kowa zai iya gani Ibrahim Babangida da Abdussalami Abubakar suka kawo Olusegun Obasanjo daga kurkuku suka ba shi takarar shugabancin kasa. APP kuma Jami’an Gwamnatin Sani Abacha su ne suka mamayeta, Allah da ikonsa kamar yadda tun farko sai da aka turo min wani lauya Chief Olasupo Shonibare, dan wani fitaccen attajiri a Lagos bacin mun taba haduwa da shi da tsohon mataimakin Gwamnan Anambra a Legas, mun taba kaiwa har karfe hudu na Asuba (4:00am) muna tattaunawa akan hadin kan Arewa da Kudu da Yamma. Da Barr. Olasupo Sonibare ya zo wurina a Kano na sauke shi a Hotel, na kai shi wurin dan Masanin Kano (Maitama Sule) da Marigayi Malam Lawan Dambazau da wasu manyan mutane, muka yi taro a ofishina na da, No. 11 Beirut Road-Kano, daga nan muka dunguma zuwa Abuja, inda muka fahimci inda aka sa gaba. Sai muka hadu ni da Bola Ige da Dokta Ezeife, tsohon Gwamnan Anambra, wadanda su ma Sani Abacha ya tsare su, sai muka yi tunanin janyewa daga duk wani shiri da muka fahimci na tsofaffin sojojin da suka azaftar da mu ne, shi ne muka kafa A.D. Ni ne na dauki nauyin bude ofisoshinta na Jihohin Arewa masu yawa, tun daga Sakkwato har zuwa Barno. Kamar yadda hukumar zabe (INEC) ta kallafa wa kowacce jam’iyya sai ta bude ofisoshin 24 cikin jahohi 36, da kuma Hedkwata a Abuja kafin a yi mata rijistar farko, sannan sai ta samu kasha 5 cikin 100 (5%) na yawan kuri’un da aka kada a zaben kananan hukumomi da akalla jihohi 24 da Abuja. Haka na dauki nauyin wasu ‘yan takarar namu na kansiloli domin mu sami kasha biyar cikin 100 (5%) din sannan aka yi mana rajista babba, muka zama cikakkiyar Jam’iyya.
Ba zan manta ba lokacin da nike tsare a Hedkwatar SSS Abuja su Major Hamza Almustapha suka shigo inda nake da karfe 3:00am ina barci suka tashe ni, suka fesa min tiya-gas a ido suka kwada min bulala a kaina ta tsinke. Nayi ta yi musu addu’o’i masu karfi, har suka tsorata. Duk abin da na roki Allah sai da na ga biyan bukata.
Na farko, ina tsare Sani Abacha ya mutu, bacin na fito na samu labarin kwamishinan ‘yan sanda da aka taba ba shi ajiyata na kwana biyu a ofis dinsa na fito ba a kwana talatin (30) ba ya mutu, haka mataimakinsa da ya tsareni kwana daya a ofis dinsa na fito bai kwana talatin ba ya mutu. Kamar yadda ban kwana talatin (30) a Hedkwartar SSS ta Abuja ba Sani Abacha ya mutu. Shi kuma da ya sa aka fesa min tiya-gas aka kwada min bulala har ta ta tsinke, sai da ya shekara 13 a kurkuku. Watakila da na mutu shi ma sai an kashe shi, kamar yadda da aka sakoni na yi kashin abin da ban taba ganin irin sa ba. Sai kuma mai baiwa Sani Abacha shawara a kan tsaro da yake sawa ake yi mana a zaba, yanzu ya haukace. Lokacin da su Al-Mustapha suka zo inda nake da kwana daya ya sake dawowa neman hadin kaina, har ya ce da ni Gwamnati ta bai wa Buhari shugabancin PTF ne domin in daina yin rigima da su, bai san ni ba a sona ma Buhari ya karbi aikin na PTF ba, saboda ya taba gaya min Ibrahim Babangida da Sani Abacha ne suka yi masa juyin mulki, suka tsare shi watanni arba’in (40), sai daga baya nike tunanin ko su Almustapha din ne suka yi amfani da ma’aikatan PTF din, musamman na kusa da shi suka raba Buhari da mutanen kirki suna hada shi da mutanen banza, har aka nemi kashe shi. Bacin sun yi ta wahalar da shi tsawon shekaru saboda sun ga bai san kulle-kulle da yaudara na ‘yan siyasa ba, musamman wadanda suka yi masa juyin mulki suka rusa kasar da mutanen kasar sun hade kansu da duk makiyan kasar.
Da yake Allah shi ne gatan kowa, gatan mara kowa, Buwayi gagara misali, sai ga shi Babangida da Abdulsalami da suka fito da Obasanjo daga kurkuku, suka kakaba mana shi ya zama shugaban kasa na farar hula, mai cikakken iko, shi ne ya kafa hukumar EFCC mai cin gashin kanta, ta samu hurumin shiga kowane lungu da sako ta san sirrin kowa da kowa karkashin Malam Nuhu Ribadu, ya ce shugabannin kananan Hukumomi 774 barayi ne, Gwamnoni 36 barayi ne, inda ya fadi duk satar da tsofaffin shugabanni da iyalansu suka yi, har ya kama Sufeto Janar na ‘Yan sanda aka sa masa sarka a kafa da hannu da wuya aka rika kai shi kotu a bakar mota, aka tsare Muhammad Babangida (dan IBB) da ‘Yar Obasanjo (Iyabo) da Obasanjo ya firgita ya fara tunanin kada shi ma abin ya zo kansa.
Da Umaru Musa ‘Yar’aduwa ya zama shugaban kasa sai ya cire Ribadu ya kawo Farida Waziri, ita kuma tashin farko ta ce ta gano duk shekara ana satar Dala biliyan 10 daga gwamnati ana fitar da su wasu kasashe, cikin shekaru 10 an sace Dala biliyan 100, an kuma fitar da su zuwa wasu kasashe. Har ta kara da cewa, ya kamata duk wanda za a bai wa amanar dukiyar kasa a rika kai shi wajen likitocin kwakwalwa a duba shi, don a tabbatar yana da hankali ko ba shi da hankali, ta ba da shawarar a canja dokokin Najeriya yadda za a rika kashe duk wanda ya saci kudin gwamnati bacin kwato su baki daya. Kamar yadda ba Shugaban Rundunar Adalci ta Najeriya – Abdulkarim dayyabu ne ya kirkiro EFCC ba, haka ba Muhammadu Buhari ne ya kafa ta ba, ganinta ya yi an kafa, ya ce taci gaba da aikinta. Dama idan Allah ya tashi taimakon bayinSa, makiyansu ma sai su kawo gudun mawa – Alhamdulillahi.
Abdulkarim dayyabu, shi ne Shugaban Rundunar Adalci ta Najeriya (MOJIN) 08060116666, 08023106666