Allah ne kadai zai magance matsalolin ’yan Najeriya – Shugaban CAN

Shugaban kungiyar Kiristoci ta kasa (CAN) reshen Jihar Bauchi, Rabaran Joshua Ray Maina ya bayyana cewa Allah ne kadai zai iya magance dimbin matsalolin da suka addabi ’yan Najeriya ba wani shugaba ba, ind ya bukaci kowa ya gyara tsakaninsa da Allah.Rabaran Joshua Maina ya bayyana haka ne lokacin da yake amsa tambayoyin wakilin Aminiya […]

Allah ne kadai zai magance matsalolin ’yan Najeriya – Shugaban CAN
Allah ne kadai zai magance matsalolin ’yan Najeriya – Shugaban CAN

Shugaban kungiyar Kiristoci ta kasa (CAN) reshen Jihar Bauchi, Rabaran Joshua Ray Maina ya bayyana cewa Allah ne kadai zai iya magance dimbin matsalolin da suka addabi ’yan Najeriya ba wani shugaba ba, ind ya bukaci kowa ya gyara tsakaninsa da Allah.
Rabaran Joshua Maina ya bayyana haka ne lokacin da yake amsa tambayoyin wakilin Aminiya a ofishinsa da ke Bauchi a karshen makon jiya, inda ya ce: “Mun yi addu’a Allah Ya zaba mana shugabanni masu adalci a shekara ta 2015, an yi zabe lafiya sai dai kuma daga bisani talauci da tsadar rayuwa sun addabi al’umma baki daya, akwai wadanda suke kashe makudan kudi domin ganin gwamnati ba ta yi nasara ba.
Sannan kuma ya kamata gwamnati ta fahimci cewa duk dadewa akwai ranar da za su sauka daga mulki tun daga kan shugaban karamar hukuma zuwa kansiloli zuwa gwamnoni da Shugaban kasa ya kamata su yi wa al’umma abin da ya dace,” inji shi.
Ya ce shugabanci amana ne kuma kowa zai amsa tambayoyi gobe kiyama. Ya ce tabbas talakawa suna fama da kuncin rayuwa a wannan lokaci, kayan abinci ya yi tsada mutane da dama ba sa iya cin abinci sau uku a rana sakamakon matsin tattalin arziki. “Muna ba da shawara ga Gwamnatin Tarayya ta yi wa Allah ta bude kan iyakokin kasa a shigo da kayan abinci domin rage wa talakawa ukubar da suke fuskanta a halin yanzu. A matsayinmu na shugabannin addini ya zamo wajibi a kanmu mu rika fada wa gwamnati gaskiya, shugabanni kuma su fahimci cewa masu fada musu gaskiya su ne masoyansu na gaskiya Allah Ya kara mana zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya,” inji shugaban.