Allah taimaki Sanusi Magajin Sanusi
Batun nadin sabon sarki tamkar bari ne wanda ba a kwashewa duka. Kafin a kai ga nadin sarki sai an yi rashin wanda ke bisa karaga, kuma daga cikin masu neman maye gurbinsa guda ne kawai zai yi nasara. Wannan mawuyacin al’amari ne, domin wasu za su yi murna nasu ya samu, wasu kuma za […]
Batun nadin sabon sarki tamkar bari ne wanda ba a kwashewa duka. Kafin a kai ga nadin sarki sai an yi rashin wanda ke bisa karaga, kuma daga cikin masu neman maye gurbinsa guda ne kawai zai yi nasara. Wannan mawuyacin al’amari ne, domin wasu za su yi murna nasu ya samu, wasu kuma za su yi ta bakin ciki, walau don rashin gwarzonsu, ko kuma rashin nasarar gwanin da suke tsammani zai gaje shi. Haka nan dai al’amarin maye gurbin kowane sarki ya gada, a manya da kananan masarautu.
A Kanon Dabo nadin Sanusi Lamido Sanusi a makwafin kanin kakansa, Alhaji Ado Bayero, ya sa an tayar da hakarkari, an kuma kai ruwa rana. A kasar Hausa an dauka cewa idan hayaniya da hayagaga sun biyo bayan nadin sarauta, to tabbaci hakika za ta yi karko, ta kuma yi albarka mai yawa. Wannan dai ba sabon abu ne ba a masarautar Kano, domin kuwa an taba yi. Ana iya cewa tarihi ne ya maimaita kansa, domin lokacin nadin tsohon sarki, Ado Bayero, sai da aka tayar da targa da gangar saboda sunayen da suka yi kamannu da juna, na Ado Midil da kuma na Ado dan Iya, babban dan Sarki Muhammadu Sanusi mai murabus. Hakan ya tayar da wani yamutsi, wasu na cewa sarautar ta komo gidan Sanusi, wasu kuma na cewa ba haka ba ne, har sai da aka samu sanarwa daga Kaduna, hedkwatar Jihar Arewa, wacce ta raba gardama, ta ce Ado Bayero, ma’aikacin ofishin huldar jakadancin Najeriya a kasar Sanagal ne aka ba sarautar. Hakan ya tayar da wata ‘yar kura, amma da yake sabon Sarki Ado Bayero da sauran jama’arsa sun kai zuciya nesa sai aka samu sukunin yayyafa mata ruwa cikin hikima da basira, kuma komai ya lafa lif.
To shi ya sa wasu masu son tayar da rudani irin wacce ta biyo bayan nadin Ado Bayero a 1963 suka riga liman tayar da kabbara, suka yi amfani da sunan , don tayar da gaggarumar fitina. Sun bayar da sanarwar da wasu kafafen yada labarai suka yada cewa Sanusi Ado Bayero, Chiroman Kano ne aka nada sabon sarki, jama’a kuma suka yi ta zaryan murna, suna cewa sarauta ta koma gidan Ado. Sai daga baya gwamnati ta bayar da sanarwar cewa Sanusin ne dai aka ba sarauta, amma ba Ciroma ba, danmajen Kano, Sanusi Lamido Sanusi ne, a matsayin Sarkin Kano Sanusi na biyu. Duk da cewa wasu sun ji zafin wannan al’amarin, amma daga bisani sun huce, hankulansu sun kwanta, sun fahimci cewa wannan abu dai duk na Bani Ibrahim Dabo ne, harka ce ta ‘ya’yan Abashe, kuma al’amari ne tsakanin zuriyar Abdullahi Bayero, kuma ba za su bari bangonsu ya tsage ba, balle kadangarun bariki su kurkurda.
Mahukuntan da aka dora wa hakkin zaben sabon Sarki, watau mahankaltan hakimai guda shida sun yi aikinsu yadda ya kamata, sun kuma tura sunayen mutane uku ga Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso, wanda ya yi aiki da kaifin basirarsa, ya kuma tuntubi wadanda ya kamata a tuntutuba a ciki da wajen Jihar Kano kafin ya natsu, don amincewa da daya daga cikin hakimai ukun da suka gabatar da sunayensu gabansa don zaben mafi cancanta kamar yadda doka ta tanada. To bayan haka ne Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso ya danka masa takardar shaidar amincewa da nadinsa, sa’annan kuma Madakin Kano, Alhaji Yusuf Nabahani ya mika masa takobi da tagwayen masu da takalman sanbatsai na fatar jimina don tabbatar masa da sarautar a gargajiyance.
Wannan al’amari ne da ya zo yayin mulkin siyasa, kuma tilas gwamnatin siyasa ce za ta yi nadin, kaman yadda gwamnatin Sa Ahmadu Bello ta nada Alhaji Ado Bayero a zamanin jamhuriya ta farko. Abin la’akari game da haka shi ne, wanda duk wadancan gwamnatocin suka nada ba zai kasance dan siyasa ba, sa’annan kuma ba za a yi haka don a zurma shi cikin harkokin siyasa ba. Ita gwamnati kan yi la’akari ne da zabin mahankaltan hakimai masu zaben sabon sarki wadanda suka san al’adu da dabi’un masarautarsu da kuma irin halayen wadanda suka fi cancanta wajen kare su da kuma kwanzarta su.
Ita kuma gwamnati za ta duba ne, ta darje wanda take ganin ya fi dacewa da zamani, wanda kuma zai yi mata cikakkiyar biyayya, ya kuma hada kan dukkan jama’arsa, kuma wanda duk ta fitar shi ne Allah Ya ba, kuma tilas a yi masa biyayya. Ta haka ne aka zabo kwararren ma’aikaci, wanda ya dace da zamani, kamar yadda aka zakulo marigayi Ado Bayero, yana aiki a wata duniyar, aka yi masa sarautar Kano don dacewarsa.
A yanzu dai ‘yan siyasa na kokarin haddasa fitina game da batun nadin Sanusi Lamido Sanusi, don rarraba kawunan jama’a, suna ta zuga sojan bante, don tayar da husuma, sa’anan kuma shugabannin hukumomin gwamnati na yin take-taken da ba su dace ba, wadanda kuma za su iya zubar musu da mutunci, warwas. Amma sai dai zuriyar Abashe sun hade kawunansu wuri guda, sun kuma yi wa Sarki Sanusi na biyu mubaya’a, ba sauran jayayya. Hakan kuma shi ya fi dacewa don a tabbatar da zaman lafiya. Masu ja da ikon Allah sai su hakura, bakin alkalami ya bushe.