Allah ya jikan AbM Mukhtar Muhammed 1944 – 2017
Innalillahi Wa Innah Ilaihir Raji’un a ranar lahadi 1-11-2017, Allah Ya karbi ran Iya Bayis Mashal Mukhtar Muhammed, inda ya rasu a wani asibiti da ke birnin Landan a kasar Birtaniya, bayan ya yi fama da jinya. Marigayi AbM, kamar yadda aka fi nakalta masa, ya rasu yana da shekaru 73 a duniya, ya bar […]
Innalillahi Wa Innah Ilaihir Raji’un a ranar lahadi 1-11-2017, Allah Ya karbi ran Iya Bayis Mashal Mukhtar Muhammed, inda ya rasu a wani asibiti da ke birnin Landan a kasar Birtaniya, bayan ya yi fama da jinya. Marigayi AbM, kamar yadda aka fi nakalta masa, ya rasu yana da shekaru 73 a duniya, ya bar matarsa Hajiya Rabi da ‘ya’ya shidda, hudu maza biyu mata da ’yan uwa 21, kafin rasuwarsa AbM shi ne Shugaban Hukumar Daraktocin gidan Rediyon Freedom, gidan Radiyo na farko mai zaman kansa a Kano.
A dai ranar Asabar 30-09-2017, Allah Ya yi wa Tijjani Ado Ahmad daya daga cikin ma’aikatan Rediyon Freedom rasuwa, a wani asibiti da ke kasar Amurka, kasar da ya je wani taron kara wa juna sani da ofishin Jakadancin kasar Amurka da ke nan kasar ya shirya. Kafin rasuwarsa Tijjani shi ne mataimaki a cikin shahararren shirin nan na BARKA DA HANTSI na gidan Rediyon. Zan ajiye maganar rasuwar Tijjani har sai mako mai zuwa in Allah Ya kaimu, bisa ga wasu mahimman dalilai, Allah Ya jikan Tijjani.
Yanzu bari in dawo kan AbM Mukhtar Muhammed, wanda a lokacin aikin soja, bayan ya yi Kantoman mulkin soja na tsohuwar Jihar Kaduna tsakanin 1978 zuwa 1979, ya kuma yi mamba a Majalisar koli ta mulkin soja, ya kuma rike shugaban farfado da noman amfanin gona da za a fitar a samu kudin shiga na kasa, ya kuma rike mukamin ministan gidaje da inganta birane da muhalli. Allah Ya sa ni ba ni da wata cikakkiyar alaka ta kut-da-kut da AbM, duk kuwa da ya yi Kantoman mulkin soja na tsohuwar jihata ta Kaduna. Na fara kusantarsa a baya-bayannan da ina wakilin sashen Hausa na BBC a Kano. Alaka ta kusa-da-kusa ta fara faruwa wadda kuma ta kullu, a karshe-karshen shekarar 2011, bayan da na fara yi wa Radiyon Freedom shirin BARKA DA HANTSI. Amma ko da kafin in kama wannan aiki na taba fada wa AbM cewa, ina taya su murna da suka kafa tashar Radiyo Freedom, suka kuma kawar da jinsu da ganinsu da ma dauke kawunansu, wajen kokarin barin gidan Rediyon ya kasance mai gudanar da aikace-aikacensa, bisa ga kwatanta aikin jarida yadda yake. Wanda da ba su yi haka ba, to kuwa da gidan Rediyon zuwa yanzu da ba zai zama lamba 1 ba a cikin kafofin yada labarai da ke Kano da ma Arewa baki daya ba, da kuma bai amsa takensa ba na “MURYAR JAMA’A.”
Abin da ya sa na fada masa haka, kuma na ta ya shi murnar, bai wuce sanin da na yi ba a kan irin yadda mu ma’aikatan kafofin yada labarai kullum muke cikin tsangwama ga mahukunta da sauran masu madafun iko da magoya bayansu ‘yan gaza gami da ma sauran jama’ar gari da labaran da aka yada bai musu dadi ba, muke shiga cikin tsangwama da kyara, a wani lokaci ma har da barazanar neman a kai mana hari da ka iya jikkata mu, kuma mu rasa rayukan mu gaba daya, a wani lokaci ma wasu sukan yi kokarin kaimu kara ga shugabanninmu, abin da ka iya haddasa canjin wurin aiki ko dakatarwa ko ma kora dungurungum.Don kawai mun fadi gaskiyar abin da ya faru.
Amma sai ga shi hukumar Daraktoci da ta gudunarwar gidan Rediyo Freedom ba ta da tarihin hukunta ma’aikacinta da sunan irin wancan tsarin na yin fushi da fushin wani, duk kuwa da kasancewar AbM da sauran ‘yan uwansa ‘yan asalin Jihar Kano ta farko ne, da suke da iyaye da yayye da ‘yan uwa da surukai da abokai da aminai bila’adadin tsakanin jihohin Kano da Jigawa na yau, wannan matsayi da suka dauka ya sanya nakan ce da shi Freedom Rediyo kanwar gidan Rediyon BBC ce.
Daga lokacin da na kusance shi sosai da sosai da idan lokacin Sallah babba ko karama ya zo nakan je in yi masa Barka da Sallah ko in wani abu na jaje ko na murna ya faru, ko haka kawai in je wajensa mukan yi labarin wa da kani da shi, inda yakan nuna matukar damuwarsa a kan yadda harkokin zamantakewa da inda aka dosa a kan makomar kasar nan na rashin hadin kai da neman tashin-tashina. Idan na nemi jin su da muke musu kallon shugabanni da a kan zo a taba alli garesu kafin ma a aikata wani abu, ga shi kuma yana cikin kungiyar nan ta mutanen Arewa, wato ACF da kungiyar Dattawan Arewa wato NEF, yakan ce da ni ai a cikin nasu ba dukkansu ba ne sukan zama kaifi daya a kan abin da ake so a cimmawa don ci gaban Arewa da mutanenta da ma kasa baki daya.
Ta bangaran yadda AbM, ya kama ‘yan uwansa ya kuma tabbatar da cewa da dadi ba dadi kwarya na bin kwarya, wato kowa ya san na gaba da shi kuma tilas ya ba shi girmansa, ta sanya zan iya cewa na dade ban ga iyalin da suke da hadin kai da girmama na gaba gwargwadon zarafi kamar su ba. Idan ka dawo hulda da jama’a gama gari AbM na kowa ne talaka da mai kudi, mace da namiji yaro da babba, ta yadda a kodayaushe kofar gidansa a bude take a dukkan wanda ya bukaci ganinsa. Yadda aka yi jana’izarsa ta nuna karara abin da nake magana, don kuwa sojoji manya da kanana karkashin jagorancin babban Hafsan mayakan sama na Iya Mashal Sadik Abubakar da ayarin shugaban kasa karkashin jagorancin babban jami’i mai kula da ma’aikatan fadar shugaban kasa Alhaji Abba Kyari da wasu ministoci da gwamnonin jihohin Kano da Jigawa da daruruwan talakawa, haka suka raka shi kushewarsa a cikin wannan dare na Laraba wayewar garin Alhamis.
Ta fannin kulawa da ci gaban gidan Rediyon Freedom kuwa a kullum AbM a shirye yake da ba da ta shi gudummuwar. Ni kaina ganau ne ba jiyau ba, alal misali AbM ya taba kawo mani bakuncin manyan mutane irin su Dakta Lemo tsohon Alkalin Alkalan Jihar Neja da Sardaunan Katsina kuma Shugaban kungiyar ACF, sannan tsohon Sufeto Janar na ‘yan sandan kasar nan, Alhaji Ibrahim Kumasi da sauran manyan mutane. Haka labarin yake ga AbM a duk lokacin da aka shaida masa wani babban bako da ba ta hannunsa ya biyo ba, to kuwa muddin aka sanar da shi shigowar bakon dare ko rana, safiya ko yamma, to kuwa ba makawa AbM zai zo ya tarbe shi ya kuma jira ya kammala abin da ya kawo shi.
Ba ko shakka AbM ya samu kyakyawar shaida a cikin rayuwarsa ta aikin soja da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a cikin sakonsa na ta’aziyya ya bayyana shi da cewa mutum ne mai akidar kansa da ya bar aikin soja a lokacin da ritayarsa ba ta yi ba. Haka daya daga cikin aminansa Alhaji Lawal Idris ya bayyana shi da cewa shi AbM mutum ne da kullum ko tsegumi ka kawo masa karshen maganar da zai fada maka ita ce wane a yi hakuri. Da dan wannan bayani nake mika ta’aziyyata ga iyalai da ‘yan uwa da masoya da sauran alumma da addu’ar Allah Ya gafarta wa AbM. Mu kuma Ya ba mu hakurin rashinsa. Gidan Rediyon Freedon da ya shugabanta na tsowon shekaru 14, Allah Ya kara daukakarsa Ya kade fitina. Ameeen Summa Ameen.