Allah Ya jikan Dokta Ameen Al-Deen Abubakar: 1951 zuwa 2015
Inna lilLahi wa inna ilaiHi raji`un “Daga Allah muke gare Shi kuma za mu koma” Allah Ya yi gaskiya, a ranar Juma`ar 10-07-15, Allah Ya karbi ran shararren Malamin addinin Islaman nan na kasa da ma duniyar Musulunci baki daya, Dokta Ameen Al-Deen Abubakar a kasar Saudiyya, inda ya je aikin Umrar bana a cikin […]
Inna lilLahi wa inna ilaiHi raji`un “Daga Allah muke gare Shi kuma za mu koma” Allah Ya yi gaskiya, a ranar Juma`ar 10-07-15, Allah Ya karbi ran shararren Malamin addinin Islaman nan na kasa da ma duniyar Musulunci baki daya, Dokta Ameen Al-Deen Abubakar a kasar Saudiyya, inda ya je aikin Umrar bana a cikin watan azumin nan da ya gabata. Malamin, wanda dama ya dade yana fama da rashin lafiyar da ya ke ta fama da ita a tsaitsaye, ya rasu yana da shekaru 64, a duniya, ya bar matan aure biyu da `ya`ya 18.
An haifi Dokra Ameen Al-Deen, a ranar 16-12-1951, a cikin unguwar Sheshe ta cikin karamar Hukumar birnin Kano. Kamar yadda aka san dan kowane Musulmi a kasar musulmi, wajen fara shiga makarantar Allo don neman Alkur`ani kafin shiga makarantar Boko, shi ma Dokta Ameen Al-Deen, ya yi makarantar allo har kusan zuwa yana dan shekaru 8 zuwa 9. Sai da ya kai shekaru 9, ne, wato a shekarar 1960, ya shiga makarantar Firamare ta Shahuci, inda ya kammala a shekarar 1966. Bayan ya kammala ilmin Firamare, ya samu shiga makarantar Koyon Harshen Larabci ta S.A.S. da ke dai cikin birnin Kano, makarantar da ya kammala a shekarar 1970
Kwadayin neman ilmi ya sanya Dokta Ameen Al-Deen, ya shiga jami`ar Ahmadu Bello da ke Zariya, inda ya samu shaidar takardar Difloma a 1974, ya samu digirinsa na farko da na biyu da digirin-digirgir a kan fannin addinin islama duka daga jami`ar Bayero da ke Kano a shekarun 1978 da 1983 da 1991, bi-da-bi.Ya yi karatun shaidar gudanar da makarantu a Cibiyar Horas da ma`aikata ta ASCON a shekarar 2003.
Idan ka juya akan aikin koyaswa a makarantun gwamnati, wanda ba mutane duka suka san marigayin ya yi har na tsawon kusan shekaru 15, wato tsakanin shekarar 1970 har kusan zuwa 1986. Da farko Dokta Ameen Al-Deen ya fara koyarwa a makarantar Firamare ta Ma`ahaddeen a shekarar 1970, sai Kwalejin Horon Malamai ta Bichi, da ke cikin Jihar Kano a shekarar 1974, bayan ya kammala digirinsa na farko. Aikin koyarwar ya kai marigayi Dokta Ameen Al-Deen har zuwa tsohuwar makarantarsa ta S.A.S. da S.A.S. ta Shahuci da A.T.C.Gwale. A shekarar 1986, Dokta Ameen Al-Deen ya kafa makarantunsa ta Da`awah, makarantun da suka fara suka kuma bunkasa daga na rainon yara zuwa Firamare zuwa makarantun Sakandare da zuwa yanzu suke da dalibai a fagen ilmi daban-daban a cikin kasar nan, kai har ma da kasashen waje.
Idan mai karatu ya duba rayuwar neman ilmin Marigayi Dokta Ameen Al-Deen, zai iya fahimtar cewa tun farko ya dandage ya nemi ilmin anan cikin gida, ba tare da ya tsaya yana tunanin sai ya je kasashen waje ba, irin su kasar Saudiyya ko Masar ko Sudan da makamantansu da sunan sai can zai yi karatu. Tunani da tsammanin da ya rika hana da yawa daga masu neman ilmin addinin Islama a wancan lokacin neman ilimi a nan cikin gida, lamarin da ya rika haddasa wa wasu saki na dafe, wajen bata samu ba gidan kuma an rena, amma shi marigayi Dokta Ameen Al-Deen ya yi amfani da damar da ya samu, ta yadda ya iya kammala digirinsa na digirgir yana dan shaekaru 40, mai karatuka iya cewa ai bai samu da wuri ba.
Eh! Haka ne, amma abin tambaya shi ne Malamin addinin Islama nawa ne da ya fara da karatun H.I.S. karatun da ya ke zaman kamar takardar shaidar ilmin koyarwa mai daraja ta biyu, wanda akasari tun a wancan lokacin da ma zuwa yanzu magidanta masu `ya`ya suke yinsa. Don haka in ka duba tarihin karatunsa, tun daga kan Difloma da digiri na daya da na biyu da na ukun, duk a cikin dawainiyar iyali da ke tattare da karancin albashi ga dawainiyar karantarwa da sauran matsalolin rayuwa amma a haka ya yi karatuttukan, wanda ba karamin jarumi zai yi haka ba, sai kuma wanda ya taso da kwadayin neman ilmin. Alhamdulillah! Ya kuma samu, ya kuma yi amfani da shi gwargwadon zarafi, sai addu`ar Allah Ya kai ladar dawainiyar da ya yi ga kabarinsa.
Fili irin wannan ba zai wadatar ba wajen kawo lissafin jerin ayyukan alheri kama daga na karantarwa zuwa ga kira na addinin Islama da na wallafe-wallafe da sauran wadanda suka jidanci tallafa wa rayuwar al`umma da marigayi Dokta Ameen Al-Deen ya yi a cikin rayuwarsa, sai dai a kawo wadanda suka saukaka. Tun kafin bayyanar kungiyar Izalatul Bid-di`a Wa`ikamatus Sunnah, marigayi Dokta Ameen Al-Deen ya ke shiga lungu da sako-sako na cikin birnin Kano mahaifarsa, yana kira akan a yi riko da sunnah a kauce wa bidi`a, wani wuri a saurare su, a wasu ma a rako su da jifa, haka ya yi ta yi, har zuwa lokacin da ya fadada akan fita kauyuwa da sauran garuwan Jihar Kano ita da sauran jihohi na kusa da na nesa. Ya fara wannan jihadi ne a karkashin kungiaysa ta Da`awah, wadda daga bisani ta zama a karkashinta ya kafa makarantu da Masallatan Juma`a da na hamsun salawatu, baya ga wallafe-wallafe da fassara wasu littattafan ilmin addinin Islama da na tarihi cikin harsunan Hausa da Turanci na wasu mashahuran Malam addinin Islama na duniya irin su Sheikh Abdul-azeez Ibn Baz da na Sheikh Usman Ibn Fodiyo da na Sarki Abdul-azeez Ibn Abdurrahaman Al Saud da na sauran wallafe-wallafe da aka kiyasta sun kai 14.
Yana daga cikin sahun farko na Maluman addini Islama da suka fara kafa makaratun Boko hade da na Islamiyya a Kano, tun daga kan na rainon yara zuwa na Firamare zuwa na Sakandare, a karkashin wannan karantaswa ya rika gudanar da makarantun manya da na matan aure (kamar yadda na fadi a sama). Kasancewarsa shugaban farko na Hukumar Daraktocin Hisbah (ta gwamnati), a Jihar Kano, tun daga shekarar 1999 zuwa 2004 da kuma 2011, zuwa lokacin da Allah Ya karbi ransa a watan jiya. Dokta Ameen Al-Deen ya yi yaki da badala, musamman a wa`adinsa na farko, lokacin da akan fita sintiri da shi zuwa wuraren da aka san ana aikata masha`a, ta yadda har ta kai da kansa ya ke wa mata masu yawan tazubas da aka kama bulala.
Ta karkashin Daurah, kasancewarsa mamba a Kwamitinta na nahiyar Afirka da ke karkashin jagorancin Yarima Dokta Bandar Ibn Salman Al Saud, babban abin da jama`ar Musulmin Arewacin kasar nan ba za su manta da shi ba, shi ne ta dalilinsa aka rika yin Daurah din a Kano da wasu garuruwan jihohin Arewa, al`amarin da ya rika bada dama ana daukar dalibai zuwa yin karatu a Jami`o`in addin Islama da suke kasa mai tsarki, musamman jami`ar Madina. Wannan damar karo ilmi da aka rika bai wa daliban wannan yanki ba karamar taimakawa ta ke yi ba wajen kara samar da zakakuran matasa, cikin yada sunnah a kasar nan da ma makwabtan kasashe. Baya ga tarurruka da Daurah din kan gabatar akan yadda harkokin Musulunci za su bunkasa a nahiyar Afirka da ma duniya baki daya, wadanda duk da marigayi Dokta Ameen Al-deen aka rika yinsu.
Mai karatu kamar yadda na fadi wannan fili, ba zai bada damar gabatar da dukkan irin ayyukan daukaka kalmar Allah da marigayi Dokta Ameen Al-Deen ya yi ba a rayuwarsa, domin idan ka duba ban kawo wasu daga cikin aikace-aikacen da ya yi ba a cikin kungiyoyi irin na kungiyar dalibai Musulmi MSS da ya taba shugabanta a shekarar 1975. Sai dai in ce Allah Ya jikan Dokta Ameen Al-Deen Abubakar, Ya duba bayansa. Iyalansa da dalibai da sauran al`ummar Musulmi Allah Ya ba mu hakurinn rashin.