Allah Ya jikan Lawal baidu

Tsohon ma’aikacin gidan rediyon tarayya na Kaduna, Alhaji Lawal Yahaya baidu wanda aka haifa a unguwar Katika, kwarbai, a cikin birnin Zariya a shekarar 1946 ya kwanta dama a makonnin da  suka gabata. Allah Ya sa kyakkyawan halinsa ya kwanta da shi, Ya yafe kurakuransa.Aminiya, don ta’aziyyar marigayin, sai ta tattuna da wasu daga cikin […]

Allah Ya jikan Lawal baidu

Marigayi Alhaji Lawal Yahaya VaiduMalam Yahaya Shehu Madaki, yayan marigayinTsohon ma’aikacin gidan rediyon tarayya na Kaduna, Alhaji Lawal Yahaya baidu wanda aka haifa a unguwar Katika, kwarbai, a cikin birnin Zariya a shekarar 1946 ya kwanta dama a makonnin da  suka gabata. Allah Ya sa kyakkyawan halinsa ya kwanta da shi, Ya yafe kurakuransa.
Aminiya, don ta’aziyyar marigayin, sai ta tattuna da wasu daga cikin makusantansa kamar haka:  “Sunana Yahaya Shehu Madaki, ni yayan marigayi ne, na girmi marigayi da kamar shekara bakwai kuma kusan kamar mun taso tare ke nan, sai dai shi ya yi makarantar zamani. A sanina mutum ne wanda yake da kwazo, mai biyyaya”.
 “Sunana Malam Muhammadu Adamu gidan Magatakarda Sambo, ni abokin marigayi ne, kuma kusan kamar rana daya aka haife mu, sai Allah Ya sa muna kamanni iri daya, wasu ma har ce mana suke yi ’yan tagwaye. Kai, ba na manatawa, wata rana ina cewa na girme shi, shi kuma yana cewa ya girme ni, sai gardama ta kai mu wajen wani kakanmu, sai ya ce rana daya aka haife mu. daya an haife shi da safe, daya kuma da yamma, amma bai fada mana wanda aka haifa da safe ko da yamma ba. Saboda tsananin kamar da muka yi, yana da farar mota, ina da farar mota, har ma akwai ranar da na dauko mahaifiyarsa da na ganta a hanya, na kai ta gida, amma ba ta gane cewar ni ne ba, sai da ta ji ban ambace ta da sunan da marigayin kan kira ta shi ba ne, sannan ta gane ba danta ba ne, sai wadanda ke wajen suka bushe da dariyar wai ba ta gane danta ba.
Malam Muhammadu Adamu, abokin marigayin“Marigayi ya fara aiki ne a ma’aikatar jiragen kasa a garin Jos, kafin ya fara aiki da gidan Rediyon Tarayya Kaduna, inda daga nan sai ya koma gidan rediyo Muryar Amurka, wanda ya baro yayin da mahaifiyarsa ta matsa ya dawo gida don ba ta jin dadi in ba ya kusa da ita, saboda irin biyayyar da yake da ita. Bayan dawowarsa, ya kara komawa gidan Rediyon Tarayya na Kaduna suka tura shi Sakkwato, sannan Maiduguri.  Bayan ya aje aiki, ya dawo gida muka zauna, sannan ya yi doguwar jinya, har Allah Ya karbi rayuwarsa.  Allah Ya gafarta masa, amin summa amin”.
“Sunana Yahaya, ni ne danshi namiji na farko. Yana da yara goma sha uku (13), kuma kusan kodayaushe yana yi mana nashihar cewa mu zama masu gaskiya, mu kula da addini, sannan mu so juna. Ina son yin godiya ga Mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris, saboda ya kula da mu, kuma ya kula da mahaifinmu. Haka nan ina yi wa duk wadanda suka zo ta’aziyyar mahaifinmu godiya tare da abokin babana da iyayena da kuma duk ’yan uwasa fatan Allah Ya saka wa kowa da alheri.
Malama Izzatu, uwargidan marigayin Malam Yahaya, dan marigayi na farkoMalama Izzatu ta ce, “Ni ce mace ta farko a wajen marigayi, amma mu hudu ne,  akwai Hajiya Binta da Hajiya Gambo  da Hajiya Hasana, ina fata Allah Ya gafarta masa. Mutum ne mai son zumunci. Mu ba za ka ji muna hayaniya irin ta wasu kishiyoyi ba. Kodayaushe yana yi mana nasihar mu zama masu hankuri, kuma masu son junanmu, kuma a gidan nan ba za ka iya gane dan wancan daki da dan wannan daki ba, kusan dukkan yaran daya ne. ya yi kokari wajen hada kan yaranshi. Allah Ya yafe kurakuransa, amin.