Allah Ya jikan Magaji danbatta (1931 zuwa 2014)

Inna lillahi wa inna ilaihi raji`un (Daga Allah muke gare shi kuma zamu koma,) A ranar Larabar da ta gabata ce 27-08-14, Allah Ya tabbatar da wannan aya akan babban dan gwagwarmaya kuma tsohon dan siyasa, dan jarida kuma gogaggen ma`aikacin gwamnati kuma dattijon arziki Malam Magaji danbatta, lokacin da Allah Ya karbi ransa a […]

Allah Ya jikan Magaji danbatta (1931 zuwa 2014)
Allah Ya jikan Magaji danbatta (1931 zuwa 2014)

Inna lillahi wa inna ilaihi raji`un (Daga Allah muke gare shi kuma zamu koma,)

A ranar Larabar da ta gabata ce 27-08-14, Allah Ya tabbatar da wannan aya akan babban dan gwagwarmaya kuma tsohon dan siyasa, dan jarida kuma gogaggen ma`aikacin gwamnati kuma dattijon arziki Malam Magaji danbatta, lokacin da Allah Ya karbi ransa a assibitin Garki a birnin tarayya da ke Abuja, kwanaki hudu bayn ya dawo daga jinyar sama da wata guda a wani assibiti da ke birnin Landan. Ya rasu ne yana dan shekaru 83.  Ya mutu ya bar matar aure daya, wato Hajiya Sa`adatu da `ya`ya hudu, biyu maza, biyu mata, aka kuma yi jana`izarsa kashe garin ranar Alhamis, a Kano.
Tarihin rayuwar Malam Magaji danbatta ya tabbatar da cewa an haife shi ne a shekarar 1931, ya kuma yi karatunsa a shararriyar makarantar Midil ta Kano wadda a yau ake kira Kwalejin Rumfa ta Kano.  Daga cikin `yan ajinsa a Midil din akwai marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero. Kazalika tarihin rayuwar Malam Magaji,ya tabbatar da cewa kusan tun yana dan  kasa da  shekara 20, ya fara gwagwarmayar ganin an ceto talaka daga hannun mulkin Sarakunan gargajiya da suke da daurin gindin Turawan mulkin mallaka.
   Malam Magaji, na daga cikin mutanen 8, da suka taru a ranar 08-08-1950, a wani gida da ke kan titin Ibadan a cikin unguwar Sabon Garin Kano, inda suka kafa Jam`iyyar NEPU SAWABA, yau kimanin shekaru 64, kenan.  Shi ne kuma Mataimakin Sakatare Janar dinta na farko, wanda a wancan lokaci yana dan shekara 20. Ya fara aikin jarida a jaridar rana-rana kuma ta farko a Kano wato Daily Comet, wadda tsohon shugaban kasar nan a jamhuriya ta daya Dokta Nnamdi Azikwe ya kafa a Legas, amma saboda samar da wata madafa a cikin gwagwarmayar da mazajen farko ta samarwa kasar nan `yancin kai su kayi, ya sanya ya dawo da ita Kano.  Marigayi Malam Magaji danbatta shi ne Editan farko na bangarenHausa na Jaridar daga shekarar 1950 zuwa 1953, wannan ita ta bashi damar kasancewa cikin aikin jarida kuma daya daga cikin `yan jaridar farko na kasar nan, ba ma a Arewa kadai ba.
 Mai karatu, daga `yar wannan shinfida ta farkon tarihin Malam Magaji, za ka iya fahimtar cewa “Tun ranan gini, tun ran zane,”mutum ne da ke cikin sahun farko na mutanen da ba su kai goma ba da suka zauna suka haifi jam`iyyar NEPU SAWABA, jam`iyyar da har yau ake jinjina mata da shugabanninta  akan gwagwarmayar da suka sha tsakaninsu da Turawan mulkin mallaka da `yan kazaginsu Sarakunan gargajiya, da sunan samawa Talakawa maza da mata `yanci da ita kanta kasar, kome zaka fadi akan rayuwarsa sai dai kamantawa, amma ba wai don ka sansu duka ba.
 Duk da yake Malam Magaji ya bar harkokin tafiyar da jam`iyyar NEPU a hannun su  marigayi Malam Aminu Kano, wanda duk da bada shi aka kafata ba tun farko), ya kama aikin gwamnati gadan-gadan, ta bangaren aikin jarida, har ta kai ya zama Wakilin kasar nan ta fannin yada labarai a ofishin Jakadancinmu dake k Birtaniya, kasar da ta yi mana mulkin mallaka, idan ka duba rayuwarsa kaf, tunda ya fara waccan gwagwarmaya ta siyasa da jarida (wadda ita ma aikin gwagwarmayar ceton al`umma ce tun wancan lokaci zuwa yau), za ka ga cewa marigayin cikin hidimar ceton al`umma ya taso kuma cikinta ya mutu. Allah Ya gafarta masa.
Alal misali ya yi shugaban Hukumar Daraktocin jaridar New Nigerian dake Kaduna mallakar gwamnatin arewa ta farko kuma ta karshe tun farkon kafuwarta, ya kuma shugabanci Hukumar Daraktocin Kamfanin jaridun Daily Times da ke Legas ya kuma yi shugaban Hukumar Daraktocin Hukumar gidaje ta kasa  da dai sauran aikace-aikacen wucin gadi bayan ritaya.
Tarihinsa ya tabbatar da cewa tun daga shekarar 1979, yake zama shugaba ko wakili daga jihar Kano walau a cikin Kwamitocin rubuta tsarin mulkin kasar nan ko duk wani batu da za a yi na makomar kasa.   Aikinsa na kasa na baya-bayannan, shi ne na Kwamitin taron kasa, wanda aka kammala a cikin watan Agustan nan da ya gabata inda shi ne jagoran ayarin `yan asalin jihar Kano da gwamnatin jihar ta tura taron, kuma inda ya bada gagarumar gudummuwa wajen saita alkiblar wakilan arewa a wajen taron. Kazalika ya taba zama tsohon shugaban kungiyar tuntuba ta mutanen Arewa wato ACF.
Saboda irin hakurinsa da jajircewa na iya daukar nauyin harkokin al`umma, koda da aka dawo wannan mulkin na dimokuradiyya da irin banbancin gwamnatocin da aka samu, da rana daya ba wata gwamnatin jihar Kano da taba canja shi akan wancan mukami. Kai karewa ma da karau, bayan ganin irin yadda mallakin Gidauniyar jihar Kano, ya zama mallakin jihohin Kano da Jigawa, ya sanya a shekarar 1998, Malam Magaji ya shugabanci kafa Inuwar Jama`ar Kano, Inuwar da aka tara makudan kudade, aka kuma danka shugabancin Kwamitin Amintattun mutanenta a hannunsa Malam Magaji, Inuwar da bayan duk shekara take gabatar da cikakkrn rahotonta da ya hada matsayin kudadenta da irin gudummuwar da ta bayar musamman akan fannin ilmin zamani da na islamiyya (musamman bayar da tallafin kayayyakin koya da koyarwa da horar da Malamai), har Allah Ya karbi ransa shi ne shugaban KwamitinAmintattunta.
 Abinka da mai neman labarai, ko don irin wannan ranar, wata rana na taba tambayar wani babban mutum na Kano akan me ya sa Mahukuntan Kano suke wa Malam Magaji irin wannan amincewa a koda yaushe, alhali ina ganin akwai wasu irinsa da nake ganin za su iya? Abinda ya fito bakin wancan babban mutum shine ai ba shi da kwadayi kuma yana da amana da jajircewa wjen kamanta gaskiya da adalci a dukkan abinda ya sa gaba. Fadin haka ke da wuya sai na tuna tun lokacin da na san shi sama da shekaru 30, sannan kuma na ba kaina amsa akan lalle kam haka Malam Magaji yake. Mai neman kara sanin wake Malam Magaji danbatta sai ya yi kakarin samun littafin tarinin rayuwarsa da ya rubuta da hannunsa mai suna “Cike da kaddara.’
Allah Ya jikan Dattijo dan kishin kasa sauran `yan mazan jiya,wadanda kullum ake ta rasa irinsu kuma ake rasa masu maye gurabensu Ya ba iyalinsa da `yanuwa da daukacin mutanen Jihar Kano da na kasa baki daya hakurin jure rashinsa. Amin summa amin.