Allah Ya jikan Mahmoon Baba-Ahmed 1944 zuwa 2018

Inna lillahi wa inna ilaihi raji`un. Allah Ya yi gaskiya da Ya ce daga gare Shi muke kuma gare Shi za mu koma. Da kimanin karfe 11 da wani abu na dare a ranar Alhamis din makon jiya (8-2-2018), Allah Ya karbi ran daya daga cikin malamaina da na koyi aikin jarida a aikace a […]

Allah Ya jikan Mahmoon Baba-Ahmed 1944 zuwa 2018

Inna lillahi wa inna ilaihi raji`un. Allah Ya yi gaskiya da Ya ce daga gare Shi muke kuma gare Shi za mu koma. Da kimanin karfe 11 da wani abu na dare a ranar Alhamis din makon jiya (8-2-2018), Allah Ya karbi ran daya daga cikin malamaina da na koyi aikin jarida a aikace a wajensu, kuma abokin gwagwarmaya a fagen na jarida a wannan zamani, wato Malam Mahmoon Baba-Ahmed  a Kaduna bayan ya sha fama da jinyar ajali a tsaitsaye, yana da shekara 74, a duniya. Allah Ya rahamshe shi da rahamarSa.

A 1983, na fara haduwa da marigayi Mahmoon a Maiduguri babban birnin tsohuwar Jihar Barno a zamanin suna hade da Jihar Yobe, ni kuwa ina wakilin jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo da take karkashin Kamfanin buga jaridun New Nigerian. A wancan lokaci an yi wa Mahmoon canjin wajen aiki ne a zamansa na wakilin Rediyon Tarayya na Kaduna daga Kano zuwa Maiduguri, bayan rasuwar Malam Umaru Yahaya a wani mummunan hadarin mota a wajen garin Ngamdu. 

Na tabbatar da cewa a wancan lokaci da aka tura Mahmoon zuwa Maiduguri don ya canji marigayi Umaru Yahaya sai da aka yi  kyakykyawan nazari a kan wa zai iya hawa kujerar marigayin ya zauna daidai, kasancewar a lokacin Jihar Borno tana fama da rigingimun siyasa a tsakanin Gwamnan Jihar Alhaji Muhammadu Goni na Jam’iyyar GNPP, ta marigayi Alhaji Waziri Ibrahim da shi kansa Waziri Ibrahim din da kuma Gwamna Goni a gefe daya da Jam’iyyar NPN. 

Kamar dai yadda ake fama da rigingimu a Kano a lokacin tsakanin Gwamna Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi da Shugaban jam’iyyarsu ta PRP na kasa, marigayi Malam Aminu Kano, rigingimun da a lokacin suka yi sanadiyyar tsaga Jam’iyyar PRP zuwa bangarori biyu wato bangaren TAbO a karkashin jagorancin Malam Aminu Kano da  bangaren SANTSI. Rigingimun na Barno ma haka suka yi kamari, har ta kai ga Gwamnatin Tarayya ta Jam’iyyar NPN ta Shugaban kasa Alhaji Shehu Shagari ta bayar da umarnin a fitar da Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dokokin Jihar Barno Alhaji Abdurrahman Darma daga kasar nan bisa ga zargin cewa dan kasar Chadi ne, wanda daga bisani wata kotun Jihar Barno ta yanke hukuncin cewa Shugaban Masu Rinjaye dan Najeriya ne kuma dan asalin Jihar Barno. 

A takaice mai karatu abin da nake son kawo maka a wannan makala bai wuce yadda na san marigayi Mahmoon ba a zamansa na gwarzo kuma hazikin dan jarida, wanda ya rayu a kan gwagwarmayar yako wa duk wani mai rauni hakkinsa, kamar yadda ma’aikacin jarida na hakika ya kamata ya rika zama kowane lokaci cikin gudanar da ayyukansa.

Aikin farko na aikin dauko rahoto na rigingimu da na fara yi a tsakiyar ana rigima shi ne wanda na yi da Mahmoon a farkon  1983, lokacin da Majalisar Dokokin Jihar Barno bisa ga umarnin Gwamna Goni ta nemi tsige Mai Bade Alhaji Saleh Sulaiman, duk da Kotun daukaka kara ta tabbatar da halaccin zaben da masu zaben Sarkin Bade suka yi masa a wancan lokacin, amma tunda Gwamna Goni ba ya son sa bisa ga zargin shi Mai Bade dan NPN ne, don haka ya kafa kahon zuka a kan lallai sai ya cire shi. A wancan zama da Majalisar Dokokin ta yi wadansu mutanen gari sun kai farmaki a majalisar, inda suka tada zaman majalisar, ta yadda wadansu ’yan majalisar suka sha da kyar, wadansu ma aka jikkata su. Ana cikin  waccan hatsaniya marigayi Mahmoon ya ja ni muka kutsa kai cikin majalisa yana dauke da na’urar daukar magana da niyyar ya samu hayaniyar da ake yi a cikin majalisar don kafa wa masu saurare hujjar duk wasu bayanai da labarin zai kunsa. Allah Ya sa ni a karan-kaina ba zan iya shiga wancan rigima ba, balle in ce ma zan dauko labari, a wajen marigayi Mahmoon na fara ganin haka.

Kadan ke nan daga abin da na koya na aikin jarida a aikace a wajen marigayi Mahmoon Baba-Ahmed da zan iya kawo wa mai karatu saboda karancin fili. Amma Allah Ya sani tun kafin mu hadu da Mahmoon har ma ta kai mun yi aiki tare yake cikin wadanda irin yadda suke kawo rahotanninsu cikin ba shayin komai suke burge ni matuka. Alal misali yadda ya rika ba da rahotannin rikicin Malam Buba Marwa Maitatsine da ya nemi ya ta da Kano a 1980, da kuma irin yadda ya rika kawo rahotannin rikicin siyasar SANTSI da TAbO a Jamhuriyya ta Biyu duk a zamansa na wakilin Rediyon Tarayya na Kaduna. 

Marigayi Mahmoon yana daga cikin zakakuran wakilan gidan Rediyon Tarayya na Kaduna tare da marigayi Umaru Yahaya da marigayi Yelwa Gabi da marigayi Ma’azu Umaru da makamantansu da masu sauraren rediyo na kasar nan da ita kanta tashar gidan Rediyon Tarayya ta Kaduna da mu ma’aikatan jarida za a dade ba mu manta da su ba. Saboda irin gagarumar sadaukarwar da suka bayar wajen yin aikin jarida ba tare da shayi, ko kwadayin wani abin duniya ba, illa dai aikin kawai suka sa gaba domin ci gaban al’umma. A lokacin da muke tare da Mahmoon, ya taba gaya min cewa shi bai ki ba ko da Jamhuriyyar Nijar gidan Rediyon Tarayya na Kaduna zai tura shi a shirye yake ya je don dauko labarai.

A watan Oktoban 1983 da Gwamna Sabo Bakin Zuwo na Jihar Kano ya ci zabe a inuwar Jam’iyyar PRP, ya nada Mahmoon a matsayin Janar Manajan Gidan Rediyon Kano, a zaman da ya yi na shekarar daya da wata daya, marigayi Mahmoon, ya fara amfani da jami’an wasta labarai na kananan hukumomin jihar su rika aiko wa tashar labarai da rahotannin abubuwan da suke wakana a kananan hukumominsu, shirin da kullum kara bunkasa yake, baya ga sauran sauye-sauyen da ya kawo. Haka labarin irin wannan kokarin kawo ci gaba ya kasance a gidan Rediyon Jihar Kaduna, inda nan ma ya rike mukamin Manajan Darakta na wani dan lokaci.

Idan ka kalli tsawon kusan shekara 50 da marigayi Mahmoon ya yi na baya-bayan nan har zuwa lokacin da Allah Ya karbi ransa ba ya da wani abu a gabansa da ya wuce maganar aikin jarida, kasancewar bayan ya yi ritaya ya kafa jaridar Hausa mai suna SAWABA.

Ko da ya daina buga jaridar ya ci gaba da rubuce-rubuce na fadakarwa da ilimantarwa da nishadantarwa a kan harkokin siyasa da na tattalin arzikin kasa da na zamantakewar al’umma a cikin wasu jaridun kasar nan kamar wannan jarida ta AMINIYA, inda yake da shafi mai taken: MATASHIYA. Marigayi Mahmoon ya rasu yana da shekara 74 a duniya ya bar matar aure 1 da ’ya’ya 8 da jikoki 6. Ina rokon Allah (SWT) Ya gafarta wa Mahmoon kura-kuransa Ya yaye masa duhu da azabar kabari, Ya duba bayansa, Ya ba iyalansa da ’yan uwa da aminai da abokai da ma sauran jama’ar da suka amfana da gudunmawarsa hakurin wannan babban rashi. Amin summa amin. Mu kuma Ya kyautata tamu zuwan.