Allah Ya jikan Tijjani Ado Ahmed 1979 zuwa 2017
Innah Lillahi Wa Innah Ilaihi Raji`un. A yau cikin ikon Allah zan cika wa mai karatu alkawarin da na yi ta dauka akan zan kawo ta’aziyyar abokin aiki Tijjani Ado Ahmed, wanda Allah Ya yi wa rasuwa a ranar Asabar 30-09-2017, a wani asibiti da ke kasar Amurka, kasar da ya sauka a ranar 23-09-2017, […]
Innah Lillahi Wa Innah Ilaihi Raji`un. A yau cikin ikon Allah zan cika wa mai karatu alkawarin da na yi ta dauka akan zan kawo ta’aziyyar abokin aiki Tijjani Ado Ahmed, wanda Allah Ya yi wa rasuwa a ranar Asabar 30-09-2017, a wani asibiti da ke kasar Amurka, kasar da ya sauka a ranar 23-09-2017, don wata ziyarar aiki ta makonni biyu, bisa ga amsa gayyatar kasar Amurka da ta yi wa wasu ‘yan jarida 20. Tijjani Ado Ahmed dai ya kasance wakilin gidan Rediyon nan mai zaman kansa na Freedom da ke Kano a cikin wancan ayari, kasancewar shi ke gabatarwa ofishin jakadancin kasar Amurka a nan , wani shiri cikin harshen Turanci mai suna “Gaisuwa daga kasar Amurka.”
Da ma babban dalilin da ya sa ban gabatar da wannan makala ba tun farko, bai wuce ba a yi masa sutura ba, sai a ranar Talatar nan da ta gabata bayan isowar gawarsa daga kasar Amurka, Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi II, ya jagoranci daruruwan al’ummar Musulmi wajen yi masa sallah, sannan kuma wasu daruruwan suka yi masa rakiya zuwa makabartar dan Dolo da ke Goron dutse cikin birnin Kano inda aka binneshi.
Rahotanni sun tabbatar da cewa ba wata doguwar jinya Tijjani ya yi ba kafin rasuwarsa, don kuwa an ce sun sauka ke nan daga wani jirgi da ya kaisu Atalanta, a cikin ziyarar aikin da suka kai, sai Tijjani ya yi kuka da kansa na ciwo, inda ba da wata-wata ba aka garzaya da shi asibiti, amma an ce kafin ma a binciki me ya same shi, Allah Ya karbi ransa. Amma a can baya Salisu Baffayo, abokin aikinsa a gidan Rediyo Freedom, wanda kuma suka hau jirgi daya don zuwa aikin hajjin bana tare, wanda kuma suka kasance tare duk tsawon kwanaki 29 da Tijjanin, ba dare ba rana, kasancewar dakinsu daya. A zaman Makkah ne Salisu ya ce Tijjanin ya yi fama da mura, wanda bayan auna shi a asibiti aka fada masa jininsa ya hau, har ma mai yin awon ya ce da Tijjani dama kana da hawan jini? Inda Tijjani ya ce ba shi da hawan jini kuma bai taba yi ba. Don haka likitan bai ba Tijjani maganin hawan jini ba, mai yi wuwa sannin aikin ibadar yana dauke da yanayin canjin jiki iri-iri.
Dama kafin Tijjani ya tafi aikin Hajji yana da ziyarar aiki da zai kai kasar Amurka, wanda hakan ta sanya ya dawo da wuri tun ma lokacin dawowarsa ba ta yi ba. Dawowarsa ke da wuya, sai Tijjani ya yi wo mini waya yana sanar da ni cewa zai dawo bakin aiki mu cigaba da yin shirin “Barka da Hantsi” a ranakun Litinin da Talata da Laraba wato 18, da 19, da 20, ga watan Satumbar da ya gabata ta yadda zai yi amfani da ranakun Alhamis da Juma’a, wato 21, da 22, don zuwa Abuja, inda za su tashi zuwa kasar Amurka, har yana cewa da ni ai shi bai sani ba idan ma’aikaci ya tafi aikin Hajji, ashe a cikin hutunsa ne, don haka ya dawo bakin aiki da niyyar idan Allah Ya dawo da shi daga kasar Amurka sai ya dauki sauran hutunsa yadda zai huta sosai da sosai. Allahu Akbar, ashe-ashe, a can Allah zai karbi ran Tijjani, Allah Ya gafarta masa.
A duk tsawon aikin kwanaki uku da muka yi da Tijjani, daga lokaci zuwa lokaci a cikin shiri da bayan mun kammala, ya kan dunkula hannunsa yana dukan kirjinsa a gefen hagu daga sama, yana cewa da ni wurin ke mai ciwo da zafi, ni kuwa na kan ce da shi to ka je asibiti mana.
A wannan hali, muka yi ban kwana da Tijjani, bayan isar su kasar Amurka, Tijjani ya yiwo mani sakon waya, inda ya ke cewa da ni Muna nan Amurka komai yana tafiya daidai. Na mayar masa da amsar fatan alheri da addu’ar Allah Ya dawo da su lafiya. Sai bayan rasuwarsa ne, wadanda suke Fesibuk da Watsaf da shi suke nuna mini irin hotunan da ya rinka dauka tun akan hanya da isarsu Amurka yana turo musu, daga ciki har da inda suke tare da Babban limamin masallacin juma’a na Birnin Washinton. Allahu Akbar, Allah Ya jikan Tijjani.
Kafin in shiga tarihin gajeruwar rayuwa, kuma mai cike da albarkan ta Tijjani, ya kamata in sanar da mai karatu cewa a cikin watan Nuwambar 2011, muka fara shirin “Barka da Hantsi” da marigayi Tijjani, shirin da na fara gabatar da shi da taimakawar Ahmed Rufa’i Bello a ranar Litinin 24 ga watan Oktoban 2011, amma kasancewar a lokacin Ahmed Rufa’i yana dalibta a Jami’ar Bayero, hakan ta sa Hukumar gidan Rediyon ta canja shi da Tijjani har zuwa rasuwarsa. A taikaice dai shekaru 6 da shirin ya cika a ranar Talatan nan da ta gabata, da Tijjani muka yi su. Daga baya an kawo mini mataimaka irinsu Abubakar Muhammad Janar da yanzu ya ke mataimaki na musamman ga Gwamnan Kano a ofishin Kwamishinan kananan Hukumomi da Salisu Baffayo da kuma a baya-bayannan Abdulkarim Muhammad Abdulkarim.
A tsawon wannan zaman aiki da muka yi da marigayi Tijjani na fahimci cewa duk da yake matashi ne dan shekaru 38, amma haziki ne mai kaifin hankali da natsuwa da girmama na gaba cikin ladabi da biyayya da kokarin neman abin kansa da zumunci da kuma uwa uba amana, kusan a kan komai na rayuwar yau da kullum. Ko kusa ba so nike in ce ba ma samun sabani a kan aiki ba, amma dai yana daga cikin matasan wannan zamanin da za su ce da babba ka yi hakuri a duk lokacin da wani sabani ya gitta.
Tijjani ya samu yin karatun zamani har ya kai ga yin digirin farko a fannin jarida, sannan kuma ya kara da wasu manyan digiri na biyu a fannoni daban-daban. Ya yi aikin koyarwa a makarantar gwaji ta Usman bn Affan da ke Kano, ya fara aiki da gidan Radiyo Freedom a ranar 1-04-2008. Ya kuma taba zama Sakatare Janar na kungiyar Samar wa matasa sana’o’i ta Jihar Kano, wanda daga bisani ya zama shugabanta, sannan kuma sh ine shugaban ci gaban matasan unguwar Chiranci ta kewayen birinin Kano. Tijjani ya rasu ya bar mahaifiyarsa Hajiya Rakiya da ‘ya‘yansa maza biyu wato Ado Tijjani Ado da ake ma lakabi da Sultan dan shekara goma da kaninsa Muhammad dan shekaru biyar.
Kafin in yi ta’aziyya ga mahaifiyar Tijjani da sauran ‘yan uwansa, irinsu Hajiya Binta Mansur, da Hajiya Maryam Mansur da yaya Mahamoud Ado Ahmed da Ummi Ado Ahmed da Salamatu Sa’idu da Fatima Ado Ahmed da Mohammad Ado Ahmed da Abdulkadir Ado Ahmed da Muftahu Ado Ahmed da Kamalu Ado Ahmed, ya kamata in fara da dubun dubatar masoyanmu maza da mata, manya da kanana musamman ma’abotan sauraren shirin “Barka da Hantsi” na kusa da na nesa bisa ga irin yadda suka rinka nuna alhininsu da addu’o’in neman gafara ga Tijjani, da irin yadda jama’a suka karrama shi wajen halartar jana’izarsa. Irin wannan karamci, mu da muke raye Ya kara karfafa mana gwiwa akan mu kara rike aikinmu cikin kamanta gaskiya da rikon amana da addu’ar mu ma Allah Ya girmama mutuwarmu. Shi kuma Tijjani Allah Ya gafarta masa Ya ba mu hakurin jure rashinsa ameen summa ameen.