Allah Ya kiyaye abinda ka biyo bayan yajin aikin kungiyar Malaman Jami`o`i (ASUU)

A yau an shiga watanni biyu da fara yajin aikin da `yan kungiyar Malaman Jami`o`i ta kasa wato ASUU suka fara ranar 1 ga watan Yulin da ya gabata a dukkan jami`o`in kasar nan. Makasudin yajin aikin a wannan karon, shi ne kungiyar ta ASUU, na neman gwamnatin tarayya da ta aiwatar da wata yarjejeniyar […]

Allah Ya kiyaye abinda ka biyo bayan yajin aikin kungiyar Malaman Jami`o`i (ASUU)
Allah Ya kiyaye abinda ka biyo bayan yajin aikin kungiyar Malaman Jami`o`i (ASUU)

A yau an shiga watanni biyu da fara yajin aikin da `yan kungiyar Malaman Jami`o`i ta kasa wato ASUU suka fara ranar 1 ga watan Yulin da ya gabata a dukkan jami`o`in kasar nan. Makasudin yajin aikin a wannan karon, shi ne kungiyar ta ASUU, na neman gwamnatin tarayya da ta aiwatar da wata yarjejeniyar da suka sa hannu da ita a shekarar 2009, bayan wani yajin aiki da `yan kungiyar suka yi a lokacin.
Wasu daga cikin bukatun da waccan jarjejeniya ta kunsa, akwai batun a shekarar 2012, gwamnatin taryya za ta bayar da tsabar kudi har Naira biliyan 100, ga jami`o`in don su bunkasa ayyukan koyo da koyarwa, wadanda suka hada da gine-ginen dakunan kwanan dalibai da wuraren daukar darussa da makamantansu. Kuma tsakanin shekarun 2013 zuwa 2015, gwamnatin tarayyar za ta sake bayar da tsabar kudi Naira biliyan 400 ga jami`o`in don ci gaba da samar da irin wadancan bukatu da na ambata tun farko. Wani batu kuma da yarjeniyar ta kunsa shi ne biyan tsabar kudi Naira biliyan 87, na alawus-alawus ga Malaman da sauran Ma`aikatan jami`o`in ne (a zaman biyan bashin na baya).
Bayan fara wannan yajin aiki ne gwamnatin tarayya ta shiga tattaunawa da `yan kungiyar ta ASUU a karkashin jagorancin shugaban kungiyar na kasa, Dokta Nasiru Isah Fagge,ya yin daga bangaren gwmnatin tarayya na karkashin jagorancin Sakataren gwamnatin tarayya Sanata Pius Ayim Pius da Ministar Ilmi Farfesa Rukayyatu Rufa`i
 Bayan zaman da aka yi tsakanin bangarorin biyu, da kuma irin rokon da wasu masu  fada a ji a kasar nan suka yi, kamar  Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammadu Sa`ad Abubakar da Iyayen yara da daliban kansu, ga gwamnatin tarayya da kungiyar ta ASUU, na su yi wa Allah su gaggauta kawo karshen wannan yajin aiki, gwamnatin taryya ta canja taku a cikin wancan tsarin tattaunawa, inda ta nada Gwamnan Jihar Binuwai, Dokta Gabriel Suswan a zaman shugaban Kwamitin tattaunawa. Fara tattaunawa da kwamitin ne ya haifar da gwamnatin tarayya ta yi tayin bayar da Naira biliyan 130, ga Malaman jami`o`in.
  Kamar yadda gwamnatin tarayyar ta kasafta wadannan kudi, za a yi amfani da Naira biliyan 100, don samar da dakunan kwanan dalibai da na daukar darussa da sauran gine-gine a jami`o`in, ya yin da Naira biliyan 30, za su  kasance wani bangare na biyan alawus-alawus daga cikin Naira biliyan 87, da Malamai da sauran ma`aikatan jami`o`in suke bi.
Bayar da wannan tayin, ya sanya shugabannin na ASUU suka harzuka, suka kuma kira wani taron manema labarai a ranar Alhamis din makon jiya a Legas, inda shugaban kungiyar Dokta Nasiru Isah Fagge ya ce daga yanzu ba sauran tattaunawa tsakaninsu da gwamnatin tarayyar, bare har a yi batun su koma bakin aiki akan wancan tayi. A fadarsa muddin ba gwamnati tace ta amince da waccan yarjejeniya da suka sanya hannu a shekarar 2009, ba, sannan ta bayyana irin matakan da zata bi wajen tabbatar da aiwatar da ita sau da kafa, to, kuwa batun a ci gaba da tattaunawa tsakanin juna a manta da ita.
 Dokta Fagge, ya zargi Hukumar kula da Jami`o`i ta kasa wato NUC da cewa gwamnati na neman yin amfani da ita wajen karkatar da kudaden da suka kamata a inganta fannin ilmi wajen bayar da kwangilolin da ke cike da sama da fadi, alhali bayar da ayyukan kwangila ba sa cikin ayyukan da aka kafata dominsu. Ya yi nuni da cewa, bisa ga lissafin da suka yi idan har an gina dakin kwanan dalibai mai gadaje 560 a kowace jami`a akan tsabar kudi N1.2 biliyan, a gwari-gwari kowane wurin gado daya a kowane daki zai tashi akan Naira 2.143miliyan ya yin da daki daya zai kasance akan Naira 6.571miliyan.
 Kome ke gaskiya ko rshin gaskiyar wancan zargi na sama da fadin kwangilar da za a bayar don gine-gine a jami`o`in kasar nan wannan ba shine abinda ya fi damun Iyayen yara da dalibai ba da ma dukkan wanda harkar ci gaban ilmin kasar nan ta damesa ba. Babban abinda ya fi damun iyayen yara da dalibai bai wuce irin yadda a kullum harkokin ilmin kasar nan tun daga tushe suke ta tabarbarewa ba. Ilmin Firamare zuwa ilmin Sakandare da na manyan makarantu irin na jami`o`i, na fama da matsaloli, kama daga rashin kayayyakin ayyukan koyo da koyarwa rashin kwararru da wadatattun Malamai, sai kuma yanzu yajin aiki da shi kadai ne yaren da Mahukuntan kasar nan suke ji wajen saurare da biyawa ma`aikata bukatunsu yake ta kara kassara fannin ilmin.
Masana fannin ilmi da kididdigar abin da kaje ya zo akansa sun tabbatar da cewa kasar nan ita ce kan gaba a duniya akan yajin aikin Malaman manyan makarantu, (haka ma a sauran yajin ma`aikata), yajin aikin da yake kasancewa a kullum Malaman manyan makarantun kan gwama shi da nasu bukatun kodai na neman karin albashi ko alawus-alawus, sabanin yadda `yan kasa suke tunanin ya kamata na Malaman  su rika raba bukatunsu dana makarantunsu. Labarin haka yake akan irin yadda yajin aikin ke dakushe kammala karatun daliban, ta yadda dalibai kan shafe shekaru biyar zuwa shida a karatun da ya kamata su yi a cikin shekaru hudu, haka labarin yake ga wadanda karatunsu ya kan kai shekaru biiyar ko shida.
Daga yadda ake ciki a wannan yajin aiki da yardar Allah kome daren dadewa za a daidaita, amma sai an yi sa`ar gaske daidaitawar za ta amfani talakan kasar nan, don kuwa gwamnati na ta kokawa akan abubuwa sun yi mata yawa, wasu kuma `yan Boko suna ta bayar da shawarar cewa lallai gwamanti ta bar jami`o`in kasar nan su samawa kansu mafita, ma`ana su kara kudaden karatu, karin da ba sai an fada ba zai iya kara sa mutane musamman Hausa/Fulani su ci gaba da bijirewa tura `ya`yansu neman ilmin zamani, ilmin da yanzu ta bayyana gwamnatinjihar Barno ta sha alwashin bayar da wasu `yan kudade ga dukkan mahajfin day a bari aka sa dansa ko `yarsa makarantar Boko. Don haka gibin dake tsakaninmu da abokan zamanmu zai ci gaba da fadada, wanda dama ya lafiyar giwa bare ta yi hauka.