Allah Ya sa bana ta fi bara a fannin tsaro da karuwar arziki
Allah cikin ikonSa yau har an samu kwana 18, a wannan shekarar Miladiya ta 2019. Kasancewar Nasara ya ci mu da yaki, duk kda cewar ya ce ya ba mu ’yanci a zaman kasa, amma dai ya tafi ya bar mu dabaibaye da matsalolin komai za mu yi a rayuwarmu da tafiyar da kusan dukan […]
Allah cikin ikonSa yau har an samu kwana 18, a wannan shekarar Miladiya ta 2019. Kasancewar Nasara ya ci mu da yaki, duk kda cewar ya ce ya ba mu ’yanci a zaman kasa, amma dai ya tafi ya bar mu dabaibaye da matsalolin komai za mu yi a rayuwarmu da tafiyar da kusan dukan harkokin kasashenmu da lissafin shekararsa muke aiki. Abin sai addu’a, sai kuma mahukunta san yi damarar gyarawa. Alal misali Jihar Kano ce jiha ta farko a kasar nan a zamanin gwamnatin Malam Ibrahim Shekarau ta fara bullo da amfani da kwanakin wata na shekarar Hijira a cikin gudanar da ayyukan gwamnati. Hijirar da a kanta aka samar da lissafin kidayar shekarar Musulunci.
Ba niyyar makalar ta yau ba ce ta yi tsokaci a kan shekarar Hijirar da a yau muke 11 ga watan Jimada Ula 1440, Bayan Hijjira, illa dai tsokaci na yi a kan yadda muke yin watsi da amfani da shekarar Musuluncin cikin tafiyar da harkokinmu na yau da kullum, ga shi kuma kundin tsarin mulkin kasar nan na 1999, da akai wa kwaskwarima ko kusa bai hana mu ba. Allah Ya ba mu ikon waiwayowa a kan yin amfani da lissafin shekarar Hijira cikin dukan harkokinmu da na kasa baki daya. Niyyar makalar ta yau bai wuce kamar yadda aka saba duk shekara a yi waiwaye adon tafiya a kan wasu daga cikin abubuwan da kasar nan ta ratso a shekarar da gabata ba, wato 2018, kuma a yi hasashen wadanda aka fuskanta a wannan shekara ta 2019, kamar na matakan tsaro da siyasa da tattalin arziki da zamantakewa da sauransu, musamman da bana ce shekarar babban zaben kasar nan da a yau ya rage kwanaki 28, cikin yardar Allah.
Alhamdulillah, sheakarar 2018 ko kusa ba ka ce tafi ta 2017, zaman lafiya ko samun bunkasar tattalin arziki ba, saboda irin abubuwan da suka faru a cikinta na rashin tsaro da rigingimun siyasa da matsalolin tattalin arziki, kai har ma da na zamantakewarmu. Ko shakka babu samuwar hakan, ba ta rasa nasaba da kasancewar shekarar 2018, din ita ce shekarar kakan zaben bana ba. Dama a bisa ga al’ada a kasashe irin namu da na sauran duniya, duk lokacin da aka shiga jajibirin shekarar zabe, za ka tarar ana samun rikice-rikice da hayaniya da hauma-hauma iri-iri da kara kawo tashe-tashen hankula da kashe-kashe, musamman a kasashe irin na nahiyarmu ta Afirka. Ba don komai ba hakan ke kara ta’azzara, sai don irin yadda ’yan siyasa kan mayar da neman mulki tamkar wani abu na a mutu ko a yi rai.
Kamar yadda na fara ambatawa a sama, cewa bara, shekarar jajibirin zabubbukan bana ce, don haka tun a cikin watan Oktoban barar da jam’iyyun siyasa suka gudanar da tarurrukan fitar da gwanayen da za su tsaya musu zabubbukan, aka fara rigingimu da fadace-fadace da kashe-kashe kamar yadda ya faru a Jihar Zamfara inda aka kashe mutum bakwai a rigimar cikin-gida na Jam’iyyar APC, mai mulkin jihar. Haka aka ke ci gaba da irin wadannan rigingimu da fadace-fadace da kashe-kashe a jihohi irin su Kwara da Kano, a cikin hananiyar gangamin neman kuri’a da ake kai yanzu, baya ga hayaniya da kalaman batunci da na tunzura jama’a da ake ta samu suna fitowa daga bakunan wadansu ’yan takara ko magoya bayansu. Duk dai da sunan ’yancin yin gangamin zabe da doka ta ba da dama. Babbar fata duk wani mai kishi da zaman lafiyar kasar nan a yanzu bai wuce Allah Ya ba ’yan kasa ikon zaben shugabanni nagari tun daga sama har kasa da kuma ganin an yi su cikin kwanciyar hankali da lumana.
Idan ka yi ta batun matakan tsaro in na rikicin ’yan kungiyar Boko Haram da ake fama ta shi tun a shekarar 2009, musamman yanzu a jihohin Barno da Yobe, ka iya cewa alhamdullahi askarawan kasar nan sun nuna kwazo a cikin shekarar 2018, sai dai wani abin rashin jin dadi shi ne a karshe-karshen shekarar ta 2018 da ’yan kwanakin cikin sabuwar shekarar nan, ’yan Boko Haram din sun tashi haikan suna kai hare-haren kwanton bauna da yakin sunkuru a kan sansanonin askarawan, da yunkurin sake kwace wasu garuruwan da askarawan suka kwato Ko a makon jiya sai da sojoji suka yi jana’izar jami’ansu 14, a Kaduna da ’yan kungiyar ta Boko Haram suka kashe a wani harin kwanton bauna da suka kai musu a hanyar Damaturu zuwa Maiduguri. Su ma sojojin a zaman nuna bacin ransu sun yi dirar mikiya a ofishoshin buga jaridun Daily Trust da Aminiya da ke Maiduguri da Legas da Abuja har suka kame wadansu editocin jaridar biyu kan zargin wai jaridar tana buga labarai masu tunzura al’umma kan hare-haren ’yan Boko Haram a Jihar Borno da kuma sanya sojojin a cikin hadari.
Wani dan bayani ke nan a kan rikicin kungiyar Boko Haram a shiyyar Arewa maso Gabas.
A kan batun annobar sace-sacen shanu, ka iya cewa hakan ta lafa matuka, amma batun garkuwa da mutane don neman kudaden fansa gaskiyar magana sabon salo ya dauka a cikin shekarar ta 2018 da farkon wannan shekara. Na girgiza da a watan Disamban bara lokacin da jami’an tsaro suka nuna masu garkuwa da mutane a kan hanyar Enugu zuwa Fatakwal da daya daga cikinsu yake ikirari da bakinsa cewa sun yi niyyar samun Naira miliyan 500, a matsayin kudaden fansa ta hanyar yin garkuwa da mutane a cikin watan Disamba. Abin da ya girgiza ni bai wuce, dukan wadanda aka nuna Fulani ne daga Jihar Zamfara ba, kuma a yankin Kurmi na Kudu maso Yamma da ta Kudu maso Kudu, suke yin haka ba wai a nan Arewa ba, can suke gudanar da miyagun ayyukan nasu, kuma ba tare da wadansu ’yan can shiyyoyin ba da a da su muke zargi da kwarewa a kan wadannan miyagun ayyuka. Allah Ya kiyaye!
Garkuwa da mutane don neman kudin fansa ta fantsama a jihohin da a da suke jin waiwai dinta irin Jihata ta Katsina, jihar da a yanzu zai yi wuya a samu kwana uku a jere ba ka ji rahotannin yin garkuwa da mutane don neman kudin fansa ko dai a kan hanya ko a kutsa kai har cikin gida a dauke wanda ko wadanda tsautsayi ya rutsa da su. Ko a mako biyu da suka gabata wadansu masu garkuwa da mutane a tsakanin Malumfashi zuwa Katsina sun yi yunkurin sace Galadiman Katsina Mai shari’a Mamman Nasir tsohon Shugaban Kotun Daukaka Kara ta Kasa, amma ganin ba ya iya tafiya da kafa kamar yadda suke bukata suka rabu da shi, amma an ce sun tafi da na tare da shi.
Mai karatu zan tsaya a nan, saboda karancin fili ba zan iya tabo batun tattalin arzikin kasa da sauran batutuwan da suka wakana a bara ba. Fata dai Allah Ya sa shekarar 2019, ta fi ta 2018, a fannin zaman lafiya kwanciyar hankali da karuwar arziki a kasar nan da duniya baki daya, amin summa amin.