Allah Ya sa wannan ne sanadin gyara a aikin Hajjin kasar nan
Alhamdulillah! Allah cikin ikonSa da kudirarSa ranar Lahadin da ta gabata ce aka fara jigilar Maniyan kasar nan na bana zuwa kasar Saudiyya, da za su yi aikin Hajjin bana, aikin da ya ke daya daga cikin shika-shikan Musulunci biyar da suka wajaba a kan dukkan Musulmi baligi kuma mai hankali. A bana a Kaduna […]
Alhamdulillah! Allah cikin ikonSa da kudirarSa ranar Lahadin da ta gabata ce aka fara jigilar Maniyan kasar nan na bana zuwa kasar Saudiyya, da za su yi aikin Hajjin bana, aikin da ya ke daya daga cikin shika-shikan Musulunci biyar da suka wajaba a kan dukkan Musulmi baligi kuma mai hankali. A bana a Kaduna aka yi bikin al`ada da aka saba yi duk shekara a farkon fara jigilar. Bikin da Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa`ad Abubakar na III, yana cewa shi ne na farko irin sa da aka taba yi a Kadunan. Kimanin maniyata dubu 76 za su sauke farali a bana, yayin da dubu 66 za su je ne ta hannun Hukumomin jin dadin Alhazai na jihohi da babban birnin tarayya Abuja, yayin da dubu 10 za su je aikin ta jirgin yawo. Ana sa ran kammala jigilar maniyan jihohin kafin nan da ranar 17-09-15, yayin da ake sa ran jirgin farko na maniyatan zai fara dawowa kasar nan a ranar 27-09-15, in Allah Ya kaimu.
A yayin bikin, shugabanni kama daga kan shugaban kasa da ya samu wakilcin gwamnan jihar ta Kaduna kuma mai masaukin baki, Malam Nasiru El-Rufa`i, zuwa mai alfarma Sarkin Musulmi da Maimartaba Sarkin Gwandu, Alhaji Muhammadu Iliyasu Bashir da Maimartaba Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi na II, kuma shugaban kwamitin mutane biyar da gwamnatin tarayya ta kafa a zaman kwamitin sa kai na Sarakuna da malaman addinin Musulunci da za su yi rakiya, kuma su duba yadda aikin Hajjin na bana zai gudana, da Maimartaba Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris da Mai martaba Sarkin Birnin Gwari, kuma Amirul Hajj na Jihar Kaduna Alhaji Jibril mai gwari da sauran malaman addinin Islama duk kira suka yi ga maniyatan na bana da lallai su sa ni cewa babban guzurinsu a aikin Hajjin, shi ne, tsoron Allah, sannan kuma su kula da dokokin kasar Saudiyya, ta yadda za su tsare mutuncinsu da na kasar nan a idanun duniya, sannan kuma su guji jidali da badala da husuma a yayin aikin ibadar, muddin suna son aikinsu ya zama karbabbe. Dadin dadawa suka shawarce su da su dukufa cikin yi wa kasar nan da shugabanninta addu`o`in da za su kara kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali da karuwar arzikin kasar nan da mutanenta.
Aikin Hajjin na bana shi ne na farko irinsa a tarihin kasar nan da gwamnatin tarayya ta fito karara ta bada shelar cewa a banan, ba za ta tura Ayarin gwamnatin ba, bare kuma na Amirul Hajj, Amirul Hajj din da aka mayar da shi na din-din-din akan jagorancin mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa`ad Abubakar na III, a `yan shekarun baya-bayan nan, (koda yake mai alfarma Sarkin Musulmi ya kan nada wasu Sarakuna a madadinsa). Kakakin shugaban kasa Muhammadu Buhari akan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu, shi ya bada shelar haka a madadin Shugaba Buhari, inda ya kara da cewa, amma gwamnatin za ta kara mayar da hankali wajen kara ingancin harkokin hulda da kasar ta Saudiyya a yayin aikin da na kiwon lafiya da kuma jin dadin Mahajjatan.
Malam Garba Shehu ya fadi cewa ko kusa wannan sabon tsari ba ya da aniyar kuntata wa wani ko wasu, illa dai saboda irin halin da kasar nan take ciki na ganin tana ririta dan dari da kwabon da take da shi, bisa ga halin da kasar nan take ciki na rashin kudi. Ya fadi cewa ta wannan hanya gwamnatin tarayya za ta samu adana Dalar Amurka miliyan daya $1miliyan (kwatankwacin N196miliya), da wasu kuma N30miliyan da ake hidimomin cikin gida akan ayarin. Koda a lokacin bikin fara tashin maniyatan, a cikin sakon shugaban kasa ya sake jaddada cewa gwamnati tarayya ba za ta dauki nauyin kowane irin ayari, inda ya kara da cewa harta wancan Kwamitin sa kan da Mai martaba Sarkin Kano zai jagoranta, Hukumar kula da aikin Hajj ta kasa, wato NAHCOM, ita za ta dauki dawainiyarsa, daga irin kudin da ta kan caji maniyata a zaman dawainiyar da ta ke musu a cikin aikin ibadar. Tabbas wasu `yan kasa za su ji wannan labari bambarakwai, musamman Sarakuna da Malamai da na kusa da su, da suka mayar da cin gajiyar shiga ayarin Amirul Hajj ko shugaban ayarin gwamnatin tarayya, tamfar gado, don kuwa kamar yadda na fadi tun farko, wannan shi ne karon farko da gwamnatin tarayya ta ke tarbar aradu da ka ta ce ta hana, duk kuwa da kiraye-kirayen da aka sha yi a baya akan lallai a rage koma a hana gaba daya. Babban abin da zai saukaka hayaniyar kace-nace akan batun bai wuce cewa shugaban kasa Buhari Musulmi ne, kuma kowa ya ji irin mawuyacin halin da kasar nan ta ke ciki na irin barnar da gwamnatocin da suka gabata suka yi wa tattalin arzikin kasar nan, al`amarin da ya kai ga biyan albashi ya gagari ita kanta gwamnatin tarayya da wasu gwamnatocin jihohi sama da 20. Na san yadda ya soke ayarin rakiyar maniyatan kasar nan haka zai soke na sauran abokan zama masu zuwa ziyara wuraren ibadarsu.
Tunda Shugaba Buhari ya yi wannan hobbasa, yanzu kuma ya kamata gwamnatin tarayyar ta mayar da hankali wajen gyara irin barnar kudin da ake tafkawa a gwamnatocin jihohi da Majalisun kananan Hukumomi da sunan tallafa wa maniyata cikin aikin ibadar, alhali duk abin da ake ma maniyacin kasar nan tun daga nan gida, har zuwa kasa mai tsarki daga cikin kudin da ya biya ake masa. Kamar yadda yanzu ta bayyana akan umurnin da Shugaba Buhari ya ba Hukumar kula da aikin Hajji ta kasa da ta kula da wancan Kwamitin sa kai na Maimartaba Sarkin Kano daga irin kudin da take cajar maniyatan bisa ga dawainiyar da ta ke masu. Idan har Hukumar kula da aikin Hajjin ta kasa, tana samun wasu kudi daga maniyaci akan ta yi masa dawainiya, to, ina ga Hukumomin jihohi da suke cikakkiyar dawainiya da maniyatan.
Lokaci ya yi da za a fara yi wa maniyatan kasar nan bayani dalla-dalla akan kudin da suke biya, ta yadda zai iya bambanta aya da tsakuwa, amma yanzu rufa-rufa ake yi masa, ana cewa an taimake shi, alhali ba haka ba ne. Bayan haka ta samu, kuma sai a dauki tsauraran matakai, wajen ganin an rage ko an kawo karshen cuwa-cuwar da ake yi wajen rabon kujerun zuwa aikin, duk da yake an san cewa kujeru dubu 76 da ake ware wa kasar nan sun yi matukar yin kadan, amma ai abin takaicin dillancin kujerun ake yi, ba wai kai su ake ga maniyata mabukata ba. Allah Ya bada ikon kowa ya ba da gudummuwarsa da za a gyara wannan muhimmin aikin ibadar Musulmi da ya ke wajibi akan mai lafiya da ikon guzuri, kamar yadda kasar Indonisiya da sauran kasashen Musulmi suka kawo tsafta a aikin baki daya.